< اول تواریخ 6 >
پسران لاوی اینها بودند: جرشون، قهات و مراری. | 1 |
’Ya’yan Lawi maza su ne, Gershon, Kohat da Merari.
پسران قهات اینها بودند: عمرام، یصهار، حبرون و عزیئیل. | 2 |
’Ya’yan Kohat maza su ne, Amram, Izhar, Hebron da Uzziyel.
هارون، موسی و مریم فرزندان عمرام بودند. هارون چهار پسر داشت به نامهای: ناداب، ابیهو، العازار و ایتامار. | 3 |
Yaran Amram su ne, Haruna, Musa da Miriyam.’Ya’yan Haruna maza su ne, Nadab, Abihu, Eleyazar da Itamar.
نسل العازار به ترتیب اینها بودند: فینحاس، ابیشوع، | 4 |
Eleyazar shi ne mahaifin Finehas, Finehas mahaifin Abishuwa,
Abishuwa mahaifin Bukki, Bukki mahaifin Uzzi,
Uzzi mahaifin Zerahiya, Zerahiya mahaifin Merahiyot,
Merahiyot mahaifin Amariya, Amariya mahaifin Ahitub,
Ahitub mahaifin Zadok, Zadok mahaifin Ahimawaz,
Ahimawaz mahaifin Azariya, Azariya mahaifin Yohanan,
عزریا. عزریا کاهن خانهٔ خدا بود خانهای که به دست سلیمان در اورشلیم بنا شد. | 10 |
Yohanan mahaifin Azariya (shi ne ya yi hidima a matsayin firist a haikalin da Solomon ya gina a Urushalima),
Azariya mahaifin Amariya, Amariya mahaifin Ahitub,
Ahitub mahaifin Zadok, Zadok mahaifin Shallum,
Shallum mahaifin Hilkiya, Hilkiya mahaifin Azariya,
یهوصادق. وقتی خداوند مردم یهودا و اورشلیم را به دست نِبوکَدنِصَّر اسیر کرد، یهوصادق هم جزو اسرا بود. | 14 |
Azariya mahaifin Serahiya, Serahiya kuwa mahaifin Yehozadak.
Yehozadak ne aka ɗauka sa’ad da Ubangiji ya tura Yahuda da Urushalima zuwa zaman bauta ta hannun Nebukadnezzar.
چنانکه قبلاً گفته شد، جرشون، قهات و مراری پسران لاوی بودند. | 16 |
’Ya’yan Lawi maza su ne, Gershom, Kohat da Merari.
لبنی و شمعی پسران جرشون بودند. | 17 |
Waɗannan su ne sunayen’ya’yan Gershom. Libni da Shimeyi.
پسران قهات، عمرام، یصهار، حبرون، عزیئیل بودند. | 18 |
’Ya’yan Kohat maza su ne, Amram, Izhar, Hebron da Uzziyel.
محلی و موشی پسران مراری بودند. | 19 |
’Ya’yan Merari maza su ne, Mali da Mushi. Waɗannan suke gidajen Lawiyawan da aka jera bisa ga kakanninsu.
نسل جرشون به ترتیب اینها بودند: لبنی، یحت، زمه، | 20 |
Na Gershom su ne, Libni, Yahat, Zimma,
یوآخ، عدو، زارح و یاترای. | 21 |
Yowa, Iddo, Zera da Yeyaterai.
نسل قهات به ترتیب اینها بودند: عمیناداب، قورح، اسیر، | 22 |
Zuriyar Kohat su ne, Amminadab, Kora, Assir,
القانه، ابیآساف، اسیر، | 23 |
Elkana, Ebiyasaf, Assir,
تحت، اوریئیل، عزیا و شائول. | 24 |
Tahat, Uriyel, Uzziya da Shawulu.
القانه دو پسر داشت: عماسای و اخیموت. | 25 |
Zuriyar Elkana su ne, Amasai, Ahimot,
نسل اخیموت به ترتیب اینها بودند: القانه، صوفای، نحت، | 26 |
Elkana, Zofai, Nahat,
الیآب، یروحام، القانه و سموئیل. | 27 |
Eliyab Yeroham, Elkana da Sama’ila.
یوئیل پسر ارشد سموئیل و ابیا پسر دوم او بود. | 28 |
’Ya’yan Sama’ila maza su ne, Yowel ɗan fari da Abiya ɗa na biyu.
نسل مراری به ترتیب اینها بودند: محلی، لبنی، شمعی، عزه، شمعی، هجیا و عسایا. | 29 |
Zuriyar Merari su ne, Mali, Libni, Shimeyi, Uzza,
Shimeya, Haggiya da Asahiya.
داوود پادشاه پس از آنکه صندوق عهد را در عبادتگاه قرار داد، افرادی را انتخاب کرد تا مسئول موسیقی عبادتگاه باشند. | 31 |
Waɗannan su ne mutanen da Dawuda ya sa su lura da waƙa a cikin gidan Ubangiji bayan da aka kawo akwatin alkawari yă huta a can.
پیش از آنکه سلیمان خانهٔ خداوند را در شهر اورشلیم بنا کند، این افراد به ترتیب در خیمهٔ ملاقات این خدمت را انجام میدادند. | 32 |
Suka yi hidima da waƙa a gaban tabanakul, Tentin Sujada, sai da Solomon ya gina haikalin Ubangiji a Urushalima. Suka yi ayyukansu bisa ga ƙa’idodin da aka shimfiɗa musu.
اینها بودند مردمانی که همراه پسرانشان خدمت میکردند: هیمان رهبر گروه از طایفهٔ قهات بود. نسب نامهٔ او که از پدرش یوئیل به جدش یعقوب میرسید عبارت بود از: هیمان، یوئیل، سموئیل، | 33 |
Ga mutanen da suka yi hidimar, tare da’ya’yansu maza. Daga mutanen Kohat akwai, Heman, mawaƙi ɗan Yowel, ɗan Sama’ila,
القانه، یروحام، الیئیل، توح، | 34 |
ɗan Elkana, ɗan Yeroham, ɗan Eliyel, ɗan Towa,
صوف، القانه، مهت، عماسای، | 35 |
ɗan Zuf, ɗan Elkana, ɗan Mahat, ɗan Amasai,
القانه، یوئیل، عزریا، صفنیا، | 36 |
ɗan Elkana, ɗan Yowel, ɗan Azariya, ɗan Zefaniya
تحت، اسیر، ابیآساف، قورح، | 37 |
ɗan Tahat, ɗan Assir, ɗan Ebiyasaf, ɗan Kora,
یصهار، قهات، لاوی و یعقوب. | 38 |
ɗan Izhar, ɗan Kohat, ɗan Lawi, ɗan Isra’ila;
آساف خویشاوند هیمان، دستیار او بود و در طرف راست او میایستاد. نسب نامهٔ آساف که از پدرش برکیا به جدش لاوی میرسید عبارت بود از: آساف، برکیا، شمعی، | 39 |
da kuma Asaf’yan’uwan Heman, waɗanda suka yi hidima a hannun damansa. Asaf ɗan Berekiya, ɗan Shimeya,
میکائیل، بعسیا، ملکیا، | 40 |
ɗan Mika’ilu, ɗan Ba’asehiya, ɗan Malkiya,
ɗan Etni, ɗan Zera, ɗan Adahiya
ɗan Etan, ɗan Zimma, ɗan Shimeyi,
ɗan Yahat, ɗan Gershom, ɗan Lawi;
ایتان دستیار دیگر هیمان از طایفهٔ مراری بود و در طرف چپ او میایستاد. نسب نامهٔ او که از قیشی به جدش لاوی میرسید عبارت بود از: ایتان، قیشی، عبدی، ملوک، | 44 |
da kuma daga’yan’uwansu, mutanen Merari, a hannun hagunsa. Etan ɗan Kishi, ɗan Abdi, ɗan Malluk,
حشبیا، اَمَصیا، حلقیا، | 45 |
ɗan Hashabiya, ɗan Amaziya, ɗan Hilkiya,
ɗan Amzi, ɗan Bani, ɗan Shemer,
محلی، موشی، مراری و لاوی. | 47 |
ɗan Mali, ɗan Mushi, ɗan Merari, ɗan Lawi.
سایر خدمات خیمهٔ عبادت به عهدهٔ لاویان دیگر بود. | 48 |
Aka ba’yan’uwansu Lawiyawa dukan sauran ayyukan tabanakul, gidan Allah.
ولی خدمات زیر به عهدهٔ هارون و نسل او بود: تقدیم هدایای سوختنی، سوزاندن بخور، تمام وظایف مربوط به قدسالاقداس و تقدیم قربانیها برای کفارهٔ گناهان بنیاسرائیل. آنها تمام این خدمات را طبق دستورهای موسی خدمتگزار خدا انجام میدادند. | 49 |
Amma Haruna da zuriyarsa su ne waɗanda suke miƙa hadayu a kan bagaden hadaya ta ƙonawa da kuma a kan bagaden turare haɗe da dukan abin da ake yi a Wuri Mafi Tsarki, suna yin kafara domin Isra’ila, bisa ga dukan abin da Musa bawan Allah ya umarta.
نسل هارون اینها بودند: العازار، فینحاس، ابیشوع، | 50 |
Waɗannan su ne zuriyar Haruna, Eleyazar, Finehas, Abishuwa,
مرایوت، امریا، اخیطوب، | 52 |
Merahiyot, Amariya, Ahitub,
طایفهٔ قهات که از نسل هارون بودند، نخستین گروهی بودند که قرعه به نامشان درآمد و شهر حبرون در سرزمین یهودا با چراگاههای اطرافش به ایشان داده شد. | 54 |
Waɗannan su ne wuraren zamansu da aka ba su rabo su zama yankunansu (aka ba wa zuriyar Haruna waɗanda suke daga gidan Kohat, domin rabo na fari nasu ne):
Aka ba su Hebron a Yahuda tare da wuraren kiwon da suke kewayenta.
(مزارع و روستاهای اطراف آن قبلاً به کالیب پسر یفنه به ملکیت داده شده بود.) | 56 |
Amma filaye da ƙauyukan da suke kewayen birnin aka ba wa Kaleb ɗan Yefunne.
علاوه بر شهر حبرون که از شهرهای پناهگاه بود، این شهرها نیز با چراگاههای اطرافش به نسل هارون داده شد: لبنه، یتیر، اشتموع، حیلین، دبیر، عاشان و بیتشمس. | 57 |
Saboda haka aka ba wa zuriyar Haruna Hebron (birnin mafaka), da Libna, Yattir Eshtemowa,
Ashan, Yutta da Bet-Shemesh, tare da wuraren kiwonsu.
از طرف قبیلهٔ بنیامین نیز شهرهای جبع، علمت و عناتوت با چراگاههای اطرافشان به ایشان داده شد. | 60 |
Daga kabilar Benyamin kuma aka ba su Gibeyon, Geba, Alemet da Anatot, tare da wuraren kiwonsu. Waɗannan garuruwa waɗanda aka raba a tsakanin mutanen gidan Kohat, goma sha uku ne duka.
همچنین برای بقیهٔ طایفهٔ قهات ده شهر در سرزمین غربی قبیلهٔ منسی به قید قرعه تعیین شد. | 61 |
Aka ba sauran zuriyar Kohat rabon garuruwa goma daga gidajen rabin kabilar Manasse.
خاندانهای طایفهٔ جرشون سیزده شهر به قید قرعه از قبیلههای یساکار، اشیر، نفتالی و نصف قبیله منسی در باشان دریافت نمودند. | 62 |
Aka ba zuriyar Gershom, gida-gida, rabon garuruwa goma sha uku daga kabilan Issakar, Asher da Naftali, da kuma daga sashen rabi kabilar Manasse da yake a Bashan.
از طرف قبایل رئوبین، جاد و زبولون دوازده شهر به قید قرعه به خاندانهای مراری داده شد. | 63 |
Aka ba zuriyar Merari, gida-gida, rabon garuruwa goma sha biyu daga kabilan Ruben, Gad da Zebulun.
به این ترتیب بنیاسرائیل این شهرها را با چراگاههای اطرافشان به لاویان دادند. | 64 |
Saboda haka Isra’ilawa suka ba Lawiyawa waɗannan garuruwa da wuraren kiwonsu.
شهرهای اهدایی قبیلهٔ یهودا، شمعون و بنیامین نیز به قید قرعه به ایشان داده شد. | 65 |
Daga kabilan Yahuda, Simeyon da Benyamin suka ba su rabon sunayen garuruwan da aka ambata.
قبیلهٔ افرایم این شهرها و چراگاههای اطراف آنها را به خاندانهای طایفهٔ قهات داد: شکیم (یکی از شهرهای پناهگاه که در کوهستان افرایم واقع بود)، جازر، یقمعام، بیتحورون، ایلون و جترمون. | 66 |
Aka ba wa waɗansu na mutanen gidan Kohat yankin garuruwansu daga kabilar Efraim.
A ƙasar tudun Efraim aka ba su Shekem (birnin mafaka), da Gezer,
Aiyalon da Gat-Rimmon, tare da wuraren kiwonsu.
از سرزمین غربی قبیلهٔ منسی، دو شهر عانیر و بلعام با چراگاههای اطراف آنها به خاندانهای دیگر قهات داده شد. | 70 |
Daga rabin kabilar Manasse kuwa, Isra’ilawa suka ba da Aner da Bileyam, tare da wuraren kiwonsu, ga sauran gidajen mutanen Kohat.
شهرهای زیر با چراگاههای اطرافشان به خاندانهای طایفهٔ جرشون داده شد: از طرف سرزمین شرقی قبیلهٔ منسی: شهرهای جولان در زمین باشان و عشتاروت؛ | 71 |
Mutanen Gershom suka sami waɗannan. Daga gidan rabin kabilar Manasse, sun sami Golan a Bashan da kuma Ashtarot, tare da wuraren kiwonsu;
از قبیلهٔ یساکار: قادش، دابره، | 72 |
daga kabilar Issakar suka sami Kedesh, Daberat,
Ramot da Anem, tare da wuraren kiwonsu;
از قبیلهٔ اشیر: مشآل، عبدون، | 74 |
daga kabilar Asher suka sami Mashal, Abdon,
Hukok da Rehob, tare da wuraren kiwonsu;
از قبیلهٔ نفتالی: قادش در جلیل، حمون و قریتایم. | 76 |
daga kabilar Naftali kuwa suka sami Kedesh a Galili, Hammon da Kiriyatayim, tare da wuraren kiwonsu.
شهرهای زیر با چراگاههای اطرافشان به خاندانهای طایفهٔ مراری داده شد: از قبیلهٔ زبولون: رمونو و تابور؛ از قبیلهٔ رئوبین در شرق رود اردن مقابل شهر اریحا: باصر در بیابان، یهصه، قدیموت و میفعت؛ از قبیلهٔ جاد: راموت در ناحیهٔ جلعاد، محنایم، حشبون و یعزیر. | 77 |
Mutanen Merari (sauran Lawiyawan) suka sami waɗannan. Daga kabilar Zebulun suka sami Yokneyam, Karta, Rimmon da Tabor, tare da wuraren kiwonsu;
daga kabilar Ruben a hayin Urdun a gabashi Yeriko suka sami Bezer a hamada, Yahza,
Kedemot da Mefa’at, tare da wuraren kiwonsu;
daga kabilar Gad kuwa suka sami Ramot a Gileyad, Mahanayim,
Heshbon da Yazer, tare da wuraren kiwonsu.