< مکاشفهٔ یوحنا 9 >
و چون فرشته پنجم نواخت، ستارهای رادیدم که بر زمین افتاده بود و کلید چاه هاویه بدو داده شد. (Abyssos ) | ۱ 1 |
Sa'annan mala'ika na biyar ya busa kahonsa. Na ga tauraro daga sama da ya fado zuwa duniya. An ba tauraron nan mabudin hanyar rami marar iyaka. (Abyssos )
و چاه هاویه را گشاد ودودی چون دود تنوری عظیم از چاه بالا آمد وآفتاب و هوا از دود چاه تاریک گشت. (Abyssos ) | ۲ 2 |
Ya bude hanyar rami marar iyaka, sai hayaki ya fito daga kofar kamar hayaki daga babban ramin wuta. Rana da iska suka juya duhu, sabili da hayakin da ke fitowa daga kofar ramin. (Abyssos )
و از میان دود، ملخها به زمین برآمدند و به آنها قوتی چون قوت عقربهای زمین داده شد | ۳ 3 |
Daga cikin hayakin kuwa sai ga fari sun fito zuwa duniya, aka ba su iko kamar na kunamai cikin duniya.
و بدیشان گفته شدکه ضرر نرسانند نه به گیاه زمین و نه به هیچ سبزی و نه به درختی بلکه به آن مردمانی که مهر خدا رابر پیشانی خود ندارند. | ۴ 4 |
Aka gaya masu kada su yi wa ciyayi da kowanne koren ganye ko itace illa, sai dai mutanen da basu da hatimin Allah a goshinsu.
و به آنها داده شد که ایشان را نکشند بلکه تا مدت پنج ماه معذب بدارند و اذیت آنها مثل اذیت عقرب بود، وقتی که کسی را نیش زند. | ۵ 5 |
Ba a basu izini su kashe wadannan mutane ba, sai dai su azabtar da su na watani biyar. Zafinsu kuwa zai zama kamar na cizon kunama idan ta harbi mutum.
و در آن ایام، مردم طلب موت خواهند کرد و آن را نخواهند یافت و تمنای موت خواهند داشت، اما موت از ایشان خواهدگریخت. | ۶ 6 |
A kwanakin nan mutane za su nemi mutuwa, amma ba za su same ta ba. Za su yi marmarin mutuwa, amma mutuwa za ta guje su.
و صورت ملخها چون اسبهای آراسته شده برای جنگ بود و بر سر ایشان مثل تاجهای شبیه طلا، و چهره های ایشان شبیه صورت انسان بود. | ۷ 7 |
Farin kuwa suna kama da dawakai da aka shirya domin yaki. A bisa kansu akwai wani abu kamar rawanan zinariya, fuskokinsu kuma kamar na 'yan adam.
و مویی داشتند چون موی زنان، و دندانهایشان مانند دندانهای شیران بود. | ۸ 8 |
Gashinsu kuma kamar na mata yake, hakoransu kamar hakoran zaki.
و جوشنها داشتند، چون جوشنهای آهنین و صدای بالهای ایشان، مثل صدای ارابه های اسبهای بسیار که به جنگ همی تازند. | ۹ 9 |
Sulkunansu kuma kamar na karfe, karar fikafikansu kuma kamar karar kekunan dawakin yaki masu yawa da dawakai da aka shirya domin zuwa yaki.
و دمها چون عقربها با نیشهاداشتند؛ و در دم آنها قدرت بود که تا مدت پنج ماه مردم را اذیت نمایند. | ۱۰ 10 |
Suna da wutsiya da kari kamar kunamai; A wutsiyar su kuma suna da ikon da zai azabtar da mutane na tsawon wata biyar.
و بر خود، پادشاهی داشتند که ملک الهاویه است که در عبرانی به ابدون مسمی است و در یونانی او را اپلیون خوانند. (Abyssos ) | ۱۱ 11 |
Suna da wani kamar sarki a kansu, mala'ikan rami marar iyaka. Sunansa da Ibraniyanci Abadon, da Helenanci kuma Afoliyon. (Abyssos )
یک وای گذشته است. اینک دو وای دیگر بعد از این میآید. | ۱۲ 12 |
Bala'i na fari ya wuce. Duba! Bayan wannan akwai masifu guda biyu masu zuwa.
و فرشته ششم بنواخت که ناگاه آوازی از میان چهار شاخ مذبح طلایی که در حضور خداست شنیدم | ۱۳ 13 |
Mala'ika na shida ya busa kahonsa, sai na ji murya daga kahonin bagadin zinariya da ke gaban Allah.
که به آن فرشته ششم که صاحب کرنابود میگوید: «آن چهار فرشته را که بر نهر عظیم فرات بستهاند، خلاص کن.» | ۱۴ 14 |
Muryar ta ce wa mala'ika na shida da ke rike da kahon, “Kwance mala'ikun nan hudu da ke daure a babban kogin Yufiretis,''
پس آن چهارفرشته که برای ساعت و روز و ماه و سال معین مهیا شدهاند تا اینکه ثلث مردم را بکشند، خلاصی یافتند. | ۱۵ 15 |
Mala'iku hudun da aka shirya domin wannan sa'a, da wannan rana, da wannan wata, da kuma wannan shekara, aka sake su su kashe daya bisa uku na 'yan adam.
و عدد جنود سواران، دویست هزار هزار بود که عدد ایشان را شنیدم. | ۱۶ 16 |
Yawan sojoji da ke kan dawakai shine 200, 000, 000. Na ji adadin su.
و به اینطور اسبان و سواران ایشان را دررویا دیدم که جوشنهای آتشین و آسمانجونی وکبریتی دارند و سرهای اسبان چون سر شیران است و از دهانشان آتش و دود و کبریت بیرون میآید. | ۱۷ 17 |
Haka na ga dawakan a cikin wahayina da mahayansu: Sulkunansu jawur kamar wuta, bakin shudi, da kuma ruwan doruwa. Kawunan dawakan suna kama da na zakuna, daga bakunansu kuma wuta, da hayaki da farar wuta suka fito.
از این سه بلا یعنی آتش و دود وکبریت که از دهانشان برمی آید، ثلث مردم هلاک شدند. | ۱۸ 18 |
Aka kashe daya bisa uku na mutane ta annoban nan uku: wuta, hayaki da farar wuta da suka fito daka bakunansu.
زیرا که قدرت اسبان در دهان و دم ایشان است، زیرا که دمهای آنها چون مارهاست که سرها دارد و به آنها اذیت میکنند. | ۱۹ 19 |
Domin iko na dawakan na bakunansu da wutsiyoyinsu - domin wutsiyoyinsu suna kama da macizai, kuma suna da kawuna wadanda dasu suke ji wa mutane rauni.
و سایرمردم که به این بلایا کشته نگشتند، از اعمال دستهای خود توبه نکردند تا آنکه عبادت دیوها وبتهای طلا و نقره و برنج و سنگ و چوب را که طاقت دیدن و شنیدن و خرامیدن ندارند، ترک کنند؛ | ۲۰ 20 |
Sauran 'yan adam, da ba a kashe su ta wannan annoba ba, basu tuba daga ayyukan da suka yi ba. Basu kuma daina bautar aljanu da gumakan zinariya, da azurfa, da tagulla, da dutse, da itace ba - abubuwan da ba su gani, ji, ko tafiya.
و از قتلها و جادوگریها و زنا و دزدیهای خود توبه نکردند. | ۲۱ 21 |
Basu kuma tuba ba daga kisan kai, sihiri, fasikanci, ko kuma ayyukansu na sata ba.