< مکاشفهٔ یوحنا 8 >
و چون مهر هفتم را گشود، خاموشی قریب به نیم ساعت در آسمان واقع شد. | ۱ 1 |
Lokacin da Dan Ragon nan ya bude hatimi na bakwai, sai aka yi shiru a sama na kimanin rabin sa'a.
و دیدم هفت فرشته را که در حضور خد ایستادهاند که به ایشان هفت کرنا داده شد. | ۲ 2 |
Sa'anan na ga mala'iku bakwai wadanda ke tsaye a gaban Allah, aka kuma basu kahonni bakwai
و فرشتهای دیگرآمده، نزد مذبح بایستاد با مجمری طلا و بخوربسیار بدو داده شد تا آن را به دعاهای جمیع مقدسین، بر مذبح طلا که پیش تخت است بدهد، | ۳ 3 |
Wani mala'ika ya zo, rike da tasar turaren konawa na zinariya, a tsaye gaban bagadi. Turaren konawa mai yawa aka bashi saboda ya mika su tare da adu'o'in dukan masu bada gaskiya akan bagadin kona turare na zinariya a gaban kursiyin.
و دود بخور، از دست فرشته با دعاهای مقدسین در حضور خدا بالا رفت. | ۴ 4 |
Hayakin turaren konawa, da adu'o'in masu bada gaskiya, suka tashi sama a gaban Allah daga hanun mala'ikar.
پس آن فرشته مجمررا گرفته، از آتش مذبح آن را پر کرد و به سوی زمین انداخت و صداها و رعدها و برقها و زلزله حادث گردید. | ۵ 5 |
Mala'ikan ya dauki tasar turaren konawa ya cika ta da wuta daga bagadin. Sa'annan ya wurgo ta kasa zuwa duniya, sai ga tsawar aradu, da cida, da walkiya mai haske, da kuma girgizar kasa.
و هفت فرشتهای که هفت کرنا را داشتندخود را مستعد نواختن نمودند | ۶ 6 |
Mala'ikun nan bakwai wadanda suke da kahonni bakwai suka yi shirin busa su.
و چون اولی بنواخت تگرگ و آتش با خون آمیخته شده، واقع گردید و به سوی زمین ریخته شد و ثلث درختان سوخته و هر گیاه سبز سوخته شد. | ۷ 7 |
Mala'ika na fari ya hura kahonsa, sai ga kankara da wuta a garwaye da jini. Aka jeho shi kasa zuwa duniya sai kashi daya cikin uku na duniya ya kone, daya cikin uku na itatuwa suka kone, da duk danyar ciyawa suka kone kaf.
و فرشته دوم بنواخت که ناگاه مثال کوهی بزرگ، به آتش افروخته شده، به دریا افکنده شد و ثلث دریا خون گردید، | ۸ 8 |
Mala'ika na biyu ya busa kahonsa, sai wani abu mai kama da babban dutse mai cin wuta aka jefo shi cikin teku. Kashi daya cikin uku na tekun ya zama jini,
و ثلث مخلوقات دریایی که جان داشتند، بمردند و ثلث کشتیها تباه گردید. | ۹ 9 |
daya cikin uku na rayayyun halittu da ke cikin ruwa suka mutu, sai daya bisa uku na jiragen ruwa aka hallaka.
و چون فرشته سوم نواخت، ناگاه ستارهای عظیم، چون چراغی افروخته شده از آسمان فرود آمد و بر ثلث نهرها و چشمه های آب افتاد. | ۱۰ 10 |
Mala'ika na uku ya busa kahonsa, sai gagarumin tauraro ya fado daga sama, yana ci kamar cocila, bisa kashi daya cikin uku na koguna da mabulbulan ruwa.
و اسم آن ستاره را افسنتین میخوانند؛ و ثلث آبها به افسنتین مبدل گشت و مردمان بسیار ازآبهایی که تلخ شده بود مردند. | ۱۱ 11 |
Sunan tauraron Daci. Kashi daya cikin uku na ruwaye suka yi daci, sai jama'a da yawa suka mutu domin ruwayen sun yi daci.
و فرشته چهارم بنواخت و به ثلث آفتاب وثلث ماه و ثلث ستارگان صدمه رسید تا ثلث آنهاتاریک گردید و ثلث روز و ثلث شب همچنین بینور شد. | ۱۲ 12 |
Mala'ika na hudu ya busa kahonsa, sai daya cikin kashi uku na rana ya harbu, da daya cikin kashi uku na wata da kuma daya cikin kashi uku na taurari. Sai daya cikin kashi uku nasu duka suka duhunce; daya cikin kashi uku na yini da daya cikin uku na dare suka rasa hasken su.
و عقابی را دیدم و شنیدم که دروسط آسمان میپرد و به آواز بلند میگوید: «وای وای وای بر ساکنان زمین، بسبب صداهای دیگرکرنای آن سه فرشتهای که میباید بنوازند.» | ۱۳ 13 |
Da na duba sai na ji gaggafa da take shawagi a tsakiyar sararin sama tana kira da babban murya, “Kaito, kaito, kaito, ga mazaunan duniya sabili da sauran karar kahonni na mala'ikun nan uku da za su busa.”