< مرقس 15 >
بامدادان، بیدرنگ روسای کهنه بامشایخ و کاتبان و تمام اهل شورامشورت نمودند و عیسی را بند نهاده، بردند و به پیلاطس تسلیم کردند. | ۱ 1 |
Da sassafe, sai manyan firistoci suka hadu da dattawa da manyan malamai, da majalisa suka daure Yesu, suka sa shi gaba suka mika shi ga Bilatus.
پیلاطس از او پرسید: «آیا تو پادشاه یهودهستی؟» او در جواب وی گفت: «تو میگویی.» | ۲ 2 |
Bilatus ya tambaye shi, kaine sarkin Yahudawa? ya amsa ya ce “haka ka ce”
و چون روسای کهنه ادعای بسیار بر او می نمودند، | ۳ 3 |
Sai manyan firistochi suka kawo zargi iri iri a kan Yesu.
پیلاطس باز از او سوال کرده، گفت: «هیچ جواب نمی دهی؟ ببین که چقدر بر توشهادت میدهند!» | ۴ 4 |
Bilatus ya sake tambayarsa, ba ka da abin cewa? ka lura da yawan zargi da ake yi maka.
اما عیسی باز هیچ جواب نداد، چنانکه پیلاطس متعجب شد. | ۵ 5 |
Amma Yesu baya sake yi masa magana ba. wannan ya ba shi mamaki.
و در هر عید یک زندانی، هرکه رامی خواستند، بجهت ایشان آزاد میکرد. | ۶ 6 |
A lokacin idi, Bilatus ya kan sakar masu da dan bursuna wanda jama'a suka bukaci a saka,
و برابانامی با شرکای فتنه او که در فتنه خونریزی کرده بودند، در حبس بود. | ۷ 7 |
A cikin gidan yari, in da aka tsare wadansu yan tawaye, da masu kisan kai, akwai wani mai kisan kai, ana ce da shi Barrabbas.
آنگاه مردم صدازده، شروع کردند بهخواستن که برحسب عادت با ایشان عمل نماید. | ۸ 8 |
Sai Jama'a suka zo wurin Bilatus ya yi masu kamar yadda ya saba yi.
پیلاطس درجواب ایشان گفت: «آیا میخواهید پادشاه یهود را برای شما آزاد کنم؟» | ۹ 9 |
Bilatus ya amsa masu ya ce, kuna so in sakar maku sarkin Yahudawa?
زیرا یافته بودکه روسای کهنه او را از راه حسد تسلیم کرده بودند. | ۱۰ 10 |
Yayi wannan domin ya sani cewa Firistoci sun bada shi ne domin suna kishin sa,
اما روسای کهنه مردم را تحریض کرده بودند که بلکه برابا را برای ایشان رهاکند. | ۱۱ 11 |
Sai Firistochi suka zuga jama'a, sai suka yi kuwwa suna cewa, a sakar masu Barrabbas amaimakon Yesu.
پیلاطس باز ایشان را در جواب گفت: «پس چه میخواهید بکنم با آن کس که پادشاه یهودش میگویید؟» | ۱۲ 12 |
Bilatus ya sake yi masu tambaya “Yaya zan yi da Sarkin Yahudawa?”
ایشان بار دیگر فریادکردند که «او را مصلوب کن!» | ۱۳ 13 |
sai suka amsa da kuwwa” a “giciye shi!”
پیلاطس بدیشان گفت: «چرا؟ چه بدی کرده است؟» ایشان بیشتر فریاد برآوردند که «او را مصلوب کن.» | ۱۴ 14 |
Bilatus ya ce masu menene laifinsa sai suka kara ihu, “a giciye shi.”
پس پیلاطس چون خواست که مردم راخشنود گرداند، برابا را برای ایشان آزاد کرد وعیسی را تازیانه زده، تسلیم نمود تا مصلوب شود. | ۱۵ 15 |
Bilatus don yana son ya farantawa jama'a zuciya sai ya sakar masu da Barrabbas sai ya yi wa Yesu bulala, sannan ya mika shi a giciye shi.
آنگاه سپاهیان او را بهسرایی که دارالولایه است برده، تمام فوج را فراهم آوردند | ۱۶ 16 |
Sojoji suka kai shi cikin kagara, suka tara rundunan soja,
وجامهای قرمز بر او پوشانیدند و تاجی از خاربافته، بر سرش گذاردند | ۱۷ 17 |
Suka sa masa tufafin shulaiya suka nada masa rawanin kaya,
و او را سلام کردن گرفتند که «سلامای پادشاه یهود!» | ۱۸ 18 |
Suna masa kirari na ba'a suna cewa, “A gaida sarkin Yahudawa!”
و نی بر سراو زدند و آب دهان بر وی انداخته و زانو زده، بدو تعظیم مینمودند. | ۱۹ 19 |
Sai suka buge shi a kai da kulki suka kuma tofa masa yau a fuska, suka kuma durkusa suna yi masa sujadar ba'a.
و چون او را استهزاکرده بودند، لباس قرمز را از وی کنده جامه خودش را پوشانیدند و او را بیرون بردند تامصلوبش سازند. | ۲۰ 20 |
Bayan sun gama yi masa ba'a sai suka cire masa tufafin shunnaiya, sai suka maida masa tasa tufafinsa, sai suka fitar dashi don su giciye shi.
و راهگذری را شمعون نام، از اهل قیروان که از بلوکات میآمد، و پدر اسکندر و رفس بود، مجبور ساختند که صلیب او را بردارد. | ۲۱ 21 |
Suna cikin tafiya sai suka hadu da wani, mai suna Saminu Bakairawani (wato uban Alizanda da Rufus); suka tillasta shi ya dauki gijiyen Yesu.
پس اورا به موضعی که جلجتا نام داشت یعنی محل کاسه سر بردند | ۲۲ 22 |
Sojojin suka kawo Yesu wurin da ake kira Golgota (wato kokon kai)
و شراب مخلوط به مر به وی دادند تا بنوشد لیکن قبول نکرد. | ۲۳ 23 |
Suka bashi ruwan inabi hade da mur, amma ya ki ya sha.
و چون او رامصلوب کردند، لباس او را تقسیم نموده، قرعه برآن افکندند تا هر کس چه برد. | ۲۴ 24 |
Sai suka giciye shi, suka kuma raba tufafinsa suka kuma jefa kuri'a domin kowanne soja ya sami rabonsa.
و ساعت سوم بود که اورا مصلوب کردند. | ۲۵ 25 |
A sa'a ta uku aka giciye shi.
و تقصیر نامه وی این نوشته شد: «پادشاه یهود.» | ۲۶ 26 |
Sai aka rubuta alamar zargi da take cewa “Ga Sarkin Yahudawa”
و با وی دو دزد را یکی از دست راست و دیگری از دست چپ مصلوب کردند. | ۲۷ 27 |
Suka kuma giciye shi tare da wadansu yan fashi guda biyu.
پس تمام گشت آن نوشتهای که میگوید: «ازخطاکاران محسوب گشت.» | ۲۸ 28 |
Daya a hannun damansa daya a hannun hagunsa. Domin a cika abinda nassi ya fada.
و راهگذاران او رادشنام داده و سر خود را جنبانیده، میگفتند: «هانای کسیکه هیکل را خراب میکنی و در سه روز آن را بنا میکنی، | ۲۹ 29 |
suke wucewa suna zaginsa suna kada kai suna cewa, “Aha! kai da zaka rushe haikali ka kuma gina shi cikin kwana uku,
از صلیب به زیرآمده، خود را برهان!» | ۳۰ 30 |
ka ceci kanka mana, ka sauka daga giciye!”
و همچنین روسای کهنه و کاتبان استهزاکنان با یکدیگر میگفتند؛ «دیگران را نجات داد و نمی تواند خود را نجات دهد. | ۳۱ 31 |
Haka ma manyan firistoci da malamai, suka yi masa ba'a suna cewa “Ya ceci wadansu amma bai iya ceci kansa ba”
مسیح، پادشاه اسرائیل، الان از صلیب نزول کند تا ببینیم و ایمان آوریم.» و آنانی که با وی مصلوب شدند او را دشنام میدادند. | ۳۲ 32 |
Bari Almasihu Sarkin Yahudawa ya sauka daga giciye. Domin mu gaskata shi, sai wadanda aka giciye shi tare dasu, suma suka yi masa ba'a.
و چون ساعت ششم رسید تا ساعت نهم تاریکی تمام زمین را فرو گرفت. | ۳۳ 33 |
sa'a ta shida zuwa sa'a ta tara, duhu ya rufe ko'ina,
و در ساعت نهم، عیسی به آواز بلند ندا کرده، گفت: «ایلوئی ایلوئی، لما سبقتنی؟» یعنی «الهی الهی چرا مراواگذاردی؟» | ۳۴ 34 |
A sa'a ta tara, Yesu ya tada murya da karfi ya ce Eloi, Eloi lamathsabathani?” Ma'ana Ya Allahna Ya Allahna, me ya sa ka yashe ni?”
و بعضی از حاضرین چون شنیدند گفتند: «الیاس را میخواند.» | ۳۵ 35 |
Wasu daga cikin na tsaye, da suka ji shi, sai suka ce, “Duba, yana kiran Iliya.”
پس شخصی دویده، اسفنجی را از سرکه پر کرد و برسر نی نهاده، بدو نوشانید و گفت: «بگذارید ببینیم مگر الیاس بیاید تا او را پایین آورد.» | ۳۶ 36 |
Sai wani ya hanzarta, ya dauki soso ya tsoma a ruwan inabi mai tsami, ya soka agora ya mika masa don yasha. Mutumin yace bari mu gani ko Iliya zai zo ya saukar da shi.
پس عیسی آوازی بلند برآورده، جان بداد. | ۳۷ 37 |
Sai Yesu yayi kuka da babban murya da karfi sannan ya rasu.
آنگاه پرده هیکل از سر تا پا دوپاره شد. | ۳۸ 38 |
Sai labulen haikalin ya rabu kashi biyu daga sama har kasa.
و چون یوزباشی که مقابل وی ایستاده بود، دید که بدینطور صدا زده، روح را سپرد، گفت؛ «فی الواقع این مرد، پسر خدا بود.» | ۳۹ 39 |
Sa'adda da jarumin sojan da ke tsaye yana fuskantar Yesu ya ga yadda ya mutum, Sai ya ce “hakika, wannan mutum Dan Allah ne.”
و زنی چند از دور نظر میکردند که ازآنجمله مریم مجدلیه بود و مریم مادر یعقوب کوچک و مادر یوشا و سالومه، | ۴۰ 40 |
Akwai kuma mata wadanda ke dubawa daga nesa. Daga cikinsu akwai Maryamu Magadala, da Maryamu( Uwar Yakubu da Yusufu) da Salome.
که هنگام بودن او در جلیل پیروی و خدمت او میکردند. و دیگرزنان بسیاری که به اورشلیم آمده بودند. | ۴۱ 41 |
Wadannan matan sune suka bishi sa'adda da yake Galilee suna yi masa hidima. Da wadansu mata da yawa suka zo Urushalima tare da shi.
و چون شام شد، از آن جهت روز تهیه یعنی روز قبل از سبت بود، | ۴۲ 42 |
Da maraice an shiga shirye shirye domin kashe gari asabbaci ce.
یوسف نامی ازاهل رامه که مرد شریف از اعضای شورا و نیزمنتظر ملکوت خدا بود آمد و جرات کرده نزدپیلاطس رفت و جسد عیسی را طلب نمود. | ۴۳ 43 |
Sai Yusufu daga garin Arimatiya ya zo, mutumin kirki, mai girma kuma dan majalisar dattawa, mai sauraron mulkin Allah, da gaba gadi ya tafi wurin Bilatus ya bukaci a bashi jikin Yesu.
پیلاطس تعجب کرد که بدین زودی فوت شده باشد، پس یوزباشی را طلبیده، از او پرسید که «آیاچندی گذشته وفات نموده است؟» | ۴۴ 44 |
Bilatus ya yi mamakin mutuwar Yesu cikin lokaci kadan, sai ya kira jarumin ya tabbattar koYesu ya mutu.
چون ازیوزباشی دریافت کرد، بدن را به یوسف ارزانی داشت. | ۴۵ 45 |
Bayan ya tabbattar daga wurin jarumin soja cewa Yesu ya mutu, sai ya bada jikin ga Yusufu.
پس کتانی خریده، آن را از صلیب به زیر آورد و به آن کتان کفن کرده، در قبری که ازسنگ تراشیده بود نهاد و سنگی بر سر قبرغلطانید. | ۴۶ 46 |
Yusufu ya sayo likafani. ya saukar da shi daga giciye, ya kawo likafanin nan ya lulube jikin Yesu dashi. Ya kai shi kabarin da aka sassaka da dutse, wadda ya shirya shi domin kansa. Ya kawo dutse ya rufe bakin kabarin da shi.
و مریم مجدلیه و مریم مادر یوشادیدند که کجا گذاشته شد. | ۴۷ 47 |
Maryamu Magadaliya da Maryamu Uwar Yusufu sun ga wurin da aka yi jana'izar Yesu.