< دوم قرنتیان 5 >
زیرا میدانیم که هرگاه این خانه زمینی خیمه ما ریخته شود، عمارتی از خداداریم، خانهای ناساخته شده بهدستها و جاودانی در آسمانها. (aiōnios ) | ۱ 1 |
Mun san cewa idan wannan gidan da muke zaune a ciki ya rushe, muna da wani ginin daga wurin Allah. Gida ne wanda ba hannuwan mutane suka gina ba, amma madawwamin gida ne a cikin sama. (aiōnios )
زیرا که در این هم آه میکشیم، چونکه مشتاق هستیم که خانه خود را که ازآسمان است بپوشیم، | ۲ 2 |
Domin a cikin wannan jiki muna gurnani, muna jira a suturta mu da wurin zaman mu na samaniya.
اگر فی الواقع پوشیده و نه عریان یافت شویم. | ۳ 3 |
Muna jiran wannan ne domin ta wurin suturtar da mu ba za a same mu tsirara ba.
از آنرو که ما نیز که در این خیمه هستیم، گرانبار شده، آه میکشیم، از آن جهت که نمی خواهیم این را بیرون کنیم، بلکه آن را بپوشیم تا فانی در حیات غرق شود. | ۴ 4 |
Gama babu shakka yayinda muke cikin wannan alfarwa, muna gurnani, muna nawaita. Ba mu so muyi zaman hutanci. Maimakon haka, muna so a suturtar da mu, domin rai ya hadiye abu mai mutuwa.
اما او که ما را برای این درست ساخت خدا است که بیعانه روح را به ما میدهد. | ۵ 5 |
Wanda kuwa yake shirya mu domin ainihin wannan abu Allah ne, wanda ya ba mu Ruhu a matsayin alkawarin abinda ke zuwa.
پس دائم خاطرجمع هستیم و میدانیم که مادامی که در بدن متوطنیم، از خداوند غریب میباشیم. | ۶ 6 |
Domin wannan mu zama da gabagadi koyaushe. Mu lura da cewa yayinda muka shagala cikin jiki, muna nesa da Ubangiji.
(زیرا که به ایمان رفتار میکنیم نه به دیدار) | ۷ 7 |
Gama bisa ga bangaskiya muke tafiya, ba bisa ga ganin ido ba.
پس خاطرجمع هستیم و این را بیشترمی پسندیم که از بدن غربت کنیم و به نزد خداوندمتوطن شویم. | ۸ 8 |
Don haka muna da gabagadi. Mun gwammace mu rabu da jiki domin mu zauna tare da Ubangiji.
لهذا حریص هستیم بر اینکه خواه متوطن و خواه غریب، پسندیده او باشیم. | ۹ 9 |
Sai muka maishe shi burinmu, ko muna cikin jiki ko nesa, mu gamshe shi.
زیرا لازم است که همه ما پیش مسند مسیح حاضر شویم تا هرکس اعمال بدنی خود را بیابد، بحسب آنچه کرده باشد، چه نیک چه بد. | ۱۰ 10 |
Domin tilas dukanmu mu hallara a gaban kursiyin shari'a na Almasihu, saboda kowa ya karbi sakamakon abubuwan da yayi cikin jiki, ko masu kyau ne ko marasa kyau.
پس چون ترس خدا را دانستهایم، مردم رادعوت میکنیم. اما به خدا ظاهر شدهایم و امیدوارم به ضمایر شما هم ظاهر خواهیم شد. | ۱۱ 11 |
Don haka, domin mun san tsoron Ubangiji, muna rinjayar mutane. Allah na ganin yadda muke a fili. Ina fatan hakan a fili take ga lamirinku.
زیرا بار دیگر برای خود به شما سفارش نمی کنیم، بلکه سبب افتخار درباره خود به شمامی دهیم تا شما را جوابی باشد برای آنانی که درظاهر نه در دل فخر میکنند. | ۱۲ 12 |
Ba muna kokarin mu rinjaye ku domin ku kalle mu a matsayin amintattun mutane ba. Maimakon haka, muna ba ku dalilin yin takama da mu, domin ku sami amsar da za ku bada ga wadanda ke fahariya da kasancewarsu amma ba game da abinda ke zuciya ba.
زیرا اگر بیخودهستیم برای خداست و اگر هشیاریم برای شمااست. | ۱۳ 13 |
Gama idan mun fita daga hankulanmu, saboda Allah ne. Kuma idan muna cikin hankalinmu, domin ku ne.
زیرا محبت مسیح ما را فرو گرفته است، چونکه این را دریافتیم که یک نفر برای همه مردپس همه مردند. | ۱۴ 14 |
Domin kaunar Almasihu ta tilas ta mu, domin mun tabbatar da wannan: cewa mutum daya ya mutu domin kowa, kuma domin wannan duka sun mutu.
و برای همه مرد تا آنانی که زندهاند، از این به بعد برای خویشتن زیست نکنندبلکه برای او که برای ایشان مرد و برخاست. | ۱۵ 15 |
Kuma Almasihu ya mutu domin kowa, domin wadanda ke raye kada su sake rayuwa domin kansu. A maimakon haka, su yi rayuwa domin shi wanda ya mutu kuma aka tashe shi.
بنابراین، ما بعد از این هیچکس را بحسب جسم نمی شناسیم، بلکه هرگاه مسیح را هم بحسب جسم شناخته بودیم، الان دیگر او رانمی شناسیم. | ۱۶ 16 |
Domin wannan dalili, daga yanzu ba za mu kara shar'anta kowa bisa ga ma'aunin 'yan'adam ba, ko da yake a baya mun taba duban Almasihu a haka. Amma yanzu mun daina shar'anta kowa ta haka.
پس اگر کسی در مسیح باشد، خلقت تازهای است؛ چیزهای کهنه درگذشت، اینک همهچیز تازه شده است. | ۱۷ 17 |
Saboda haka, duk wanda ke cikin Almasihu, sabon halitta ne. Tsofaffin al'amura sun shude. Duba, sun zama sababbi.
و همهچیز ازخدا که ما را بواسطه عیسی مسیح با خود مصالحه داده و خدمت مصالحه را به ما سپرده است. | ۱۸ 18 |
Dukan wadannan abubuwa daga Allah ne. Ya sulhunta mu da kansa ta wurin Almasihu, ya kuma ba mu hidimar sulhu.
یعنیاینکه خدا در مسیح بود و جهان را باخود مصالحه میداد و خطایای ایشان را بدیشان محسوب نداشت و کلام مصالحه را به ما سپرد. | ۱۹ 19 |
Wato, cikin Almasihu, Allah na sulhunta duniya zuwa gare shi, ba tare da lissafin zunubansu a kansu ba. Yana damka mana sakon sulhu.
پس برای مسیح ایلچی هستیم که گویا خدا به زبان ما وعظ میکند. پس بخاطر مسیح استدعامی کنیم که با خدا مصالحه کنید. | ۲۰ 20 |
Don haka an zabe mu a matsayin wakilan Almasihu, kamar dai Allah na kira ga mutane ta wurin mu. Muna rokon ku, saboda Almasihu: ''ku sulhuntu ga Allah!''
زیرا او را که گناه نشناخت در راه ما گناه ساخت تا ما در وی عدالت خدا شویم. | ۲۱ 21 |
Shi ya maida Almasihu ya zama hadaya domin zunubinmu. Shine wanda bai taba zunubi ba. Ya yi haka ne don mu zama adalchin Allah a cikin sa.