< Romerne 16 >
1 Jeg anbefaler eder Føbe, vår søster, som er menighets-tjenerinne i Kenkreæ,
Ina gabatar muku da’yar’uwarmu Fibi, baranyar ikkilisiya a Kenkireya.
2 at I tar imot henne i Herren, som det sømmer sig for de hellige, og går henne til hånde i alt som hun måtte trenge eders hjelp i; for hun har også gått mange til hånde, ja mig selv.
Ina roƙonku ku karɓe ta a cikin Ubangiji yadda ya dace a karɓi tsarkaka a kuma ba ta kowane irin taimakon da take bukata daga wurinku, gama ta zama mai taimako ƙwarai ga mutane masu yawa, haɗe da ni ma.
3 Hils Priska og Akvilas, mine medarbeidere i Kristus Jesus,
Ku gai da Firiskila da Akwila, abokan aikina cikin Kiristi Yesu.
4 de som har våget sitt eget liv for mitt, og som ikke alene jeg takker, men også alle menigheter av hedningene,
Sun yi kasai da ransu saboda ni. Ba ni kaɗai nake musu godiya ba amma har ma da dukan ikkilisiyoyin Al’ummai.
5 og hils menigheten i deres hus. Hils Epenetus, min elskede, som er Asias førstegrøde for Kristus.
Ku kuma gai da ikkilisiyar da take haɗuwa a gidansu. Ku gai da ƙaunataccen abokina Efenetus, wanda ya zama na farko a karɓar Kiristi a lardin Asiya.
6 Hils Maria, som har arbeidet meget for eder.
Ku gai da Maryamu wadda ta yi muku aiki tuƙuru.
7 Hils Andronikus og Junias, mine frender og mine medfanger, de som har et godt navn blandt apostlene, de som også før mig er kommet til Kristus.
Ku gai da Anduronikus da Yuniyas, dangina waɗanda aka daure a kurkuku tare da ni. Su fitattu ne sosai a cikin manzanni, sun riga ni zama masu bin Kiristi.
8 Hils Amplias, min elskede i Herren.
Ku gai da Amfiliyatus, ƙaunataccena a cikin Ubangiji.
9 Hils Urbanus, vår medarbeider i Kristus, og Stakys, min elskede.
Ku gai da Urbanus, abokin aikinmu cikin Kiristi, da kuma ƙaunataccen abokina Sitakis.
10 Hils Apelles, den prøvede i Kristus. Hils dem av Aristobulus' hus.
Ku gai da Afelles wanda amincinsa cikin Kiristi tabbatacce ne. Ku gai da iyalin gidan Aristobulus.
11 Hils Herodion, min frende. Hils dem av Narkissus' hus som er i Herren.
Ku gai da ɗan’uwana, Hirodiyon. Ku gai da iyalin gidan Narkissus da suke cikin Ubangiji.
12 Hils Tryfena og Tryfosa, som har arbeidet i Herren. Hils Persis, den elskede, som har arbeidet meget i Herren.
Ku gai da Tiryifena da Tiryifosa, matan nan da suke aiki tuƙuru cikin Ubangiji. Ku gai da ƙaunatacciyata Fersis, wata matan da ta yi aiki tuƙuru cikin Ubangiji.
13 Hils Rufus, den utvalgte i Herren, og hans og min mor.
Ku gai da Rufus zaɓaɓɓe cikin Ubangiji, da kuma mahaifiyarsa, wadda ta zama kamar mahaifiya a gare ni.
14 Hils Asynkritus, Flegon, Hermes, Patrobas, Hermas, og brødrene hos dem.
Ku gai da Asinkiritus, Filegon, Hermes, Faturobas, Hermas da kuma’yan’uwan da suke tare da su.
15 Hils Filologus og Julia, Nereus og hans søster og Olympas, og alle de hellige hos dem.
Ku gai da Filologus, Yuliya, Nereyus da’yar’uwarsa, da kuma Olimfas da dukan tsarkakan da suke tare da su.
16 Hils hverandre med et hellig kyss! Alle Kristi menigheter hilser eder.
Ku gaggai da juna da sumba mai tsarki. Dukan ikkilisiyoyin Kiristi suna gaishe ku.
17 Men jeg formaner eder, brødre, til å holde øie med dem som volder tvedrakten og anstøtene imot den lære som I har lært, og gå av veien for dem;
Ina roƙonku,’yan’uwa, ku yi hankali fa da masu raba tsakani, saɓanin koyarwar da kuka koya, suna sa tuntuɓe. Ku yi nesa da su.
18 for disse tjener ikke vår Herre Jesus Kristus, men sin egen buk, og ved sin søte tale og sine fagre ord dårer de de enfoldiges hjerter.
Gama irin waɗannan mutane ba sa bautar Ubangijinmu Kiristi, sai dai cikinsu. Ta wurin yaudara da kuma daɗin baki, suna ruɗin marasa wayo.
19 For ordet om eders lydighet er kommet ut til alle; derfor gleder jeg mig over eder, men jeg ønsker at I skal være vise til det gode og rene for det onde.
Kowa ya riga ya ji game da biyayyarku, don haka ina cike da farin ciki game da ku; amma ina so ku zama masu hikima game da abin da yake nagari, ku kuma zama marasa laifi ga abin da yake mugu.
20 Men fredens Gud skal i hast knuse Satan under eders føtter. Vår Herre Jesu Kristi nåde være med eder!
Allah na salama zai tattake Shaiɗan ba da daɗewa ba yă kuma sa shi a ƙarƙashin sawunku. Alherin Ubangijinmu Yesu kuma yă kasance tare da ku.
21 Timoteus, min medarbeider, og Lukius og Jason og Sosipater, mine frender, hilser eder.
Timoti, abokin aikina, yana gai da ku, haka ma Lusiyus, Yason, da Sosifater, dangina.
22 Jeg Tertius, som nedskriver brevet, hilser eder i Herren.
Ni, Tertiyus, wanda ya rubuta wannan wasiƙa, ina gai da ku cikin Ubangiji.
23 Gajus, min og hele menighetens vert, hilser eder. Erastus, byens regnskapsfører, og broderen Kvartus hilser eder.
Gayus, mai masauƙina, mai kuma saukar da dukan’yan Ikkilisiya, yana gaishe ku. Erastus, mai bi da ayyukan jama’ar gari, da kuma ɗan’uwanmu Kwartus, suna gaishe ku.
24 Vår Herre Jesu Kristi nåde være med eder alle! Amen.
25 Men ham som er mektig til å styrke eder efter mitt evangelium og Jesu Kristi forkynnelse, efter åpenbaringen av den hemmelighet som har vært fortidd i evige tider, (aiōnios )
Ɗaukaka ta tabbata ga mai ikon ƙarfafa ku bisa ga bisharata, bisa ga wa’azin Yesu Kiristi, wadda ta gare ta ne aka bayyana asirin nan da yake ɓoye tun fil azal, (aiōnios )
26 men nu er kommet for lyset og ved profetiske skrifter efter den evige Guds befaling kunngjort for alle folk for å virke troens lydighet, (aiōnios )
amma yanzu kuwa aka bayyana, aka kuma sanar ta wurin rubuce-rubucen annabawa bisa ga umarnin Allah madawwami, domin dukan al’ummai su gaskata su kuma yi masa biyayya (aiōnios )
27 ham, den ene vise Gud ved Jesus Kristus, være æren i all evighet! Amen. (aiōn )
ɗaukaka ta tabbata har abada ga Allah, wanda shi ne kaɗai mai hikima ta wurin Yesu Kiristi! Amin. (aiōn )