< Hebreerne 5 >
1 For hver yppersteprest tas iblandt mennesker og innsettes for mennesker til tjeneste for Gud, for å frembære både gaver og slaktoffer for synder,
Kowanne babban firist, da yake an zabe shi ne daga cikin mutane, a kansa shi ya wakilci mutane ga al'amarin Allah, don ya mika sadakoki da kuma hadayu domin kawar da zunubai.
2 som en som kan bære over med de vankundige og villfarende, fordi han også selv er skrøpelighet underlagt,
Yana kuma iya tafiyar da jahilai da sangartattu a cikin salihanci, tun da shi ke rarrauna ne shi ta ko'ina.
3 og for dens skyld må frembære syndoffer, som for folket, så og for sig selv.
Saboda haka, wajibi ne ya mika hadayu, ba saboda kawar da zunuban jama'a kadai ba, har ma da na kansa.
4 Og ingen tiltar sig selv den ære, men den som kalles av Gud, likesom Aron.
Ba wanda zai kai kansa wannan matsayi mai girma, sai dai Allah ya yi kiransa ga haka, kamar yadda aka kirayi Haruna.
5 Således tilla da heller ikke Kristus sig den ære å bli yppersteprest, men han som sa til ham: Du er min Sønn, jeg har født dig idag;
Haka kuma, Almasihu, ba shi ya daukaka kansa ya zama Babban firist ba, sai dai wannan ne ya sa shi, wanda ya ce da shi, “Kai Dana ne; Yau na zama Uba a gare ka.''
6 likesom han og på et annet sted sier: Du er prest til evig tid efter Melkisedeks vis. (aiōn )
Kamar dai yadda a wani wuri kuma ya ce, “Kai firist ne na har abada, bisa ga kwatancin Malkisadak.” (aiōn )
7 Og han har i sitt kjøds dager med sterkt skrik og tårer frembåret bønner og nødrop til ham som kunde frelse ham fra døden, og han blev bønnhørt for sin gudsfrykt,
Almasihu, a lokacin zamansa a duniya, ya yi addu'o'i da roke-roke, tare da kuka mai tsanani, har da hawaye, ga wannan da yake da ikon cetonsa daga mutuwa, aka kuwa saurare shi saboda tsannin mika kansa.
8 og således lærte han, skjønt han var Sønn, lydighet av det han led,
Ko da yake shi Da ne, ya koyi biyayya ta wurin wuyar da ya sha.
9 og da han var fullendt, blev han ophav til evig frelse for alle dem som lyder ham, (aiōnios )
Har ya kai ga kammala, sai ya zama tushe madawwami, ceto ga dukkan wadanda suke masa biyayya. (aiōnios )
10 og blev av Gud kalt yppersteprest efter Melkisedeks vis.
Gama Allah yana kiransa Babban firist, bisa ga kwatancin Malkisadak.
11 Om dette har vi meget å si, som også er vanskelig å utlegge, eftersom I er blitt trege til å høre.
Muna da abu da yawa da za mu fada a game da Yesu, amma zai yi wuyar bayani, da yake basirarku ta dushe.
12 For skjønt I efter tiden burde være lærere, trenger I atter til at en lærer eder hvad som er de første grunner i Guds ord, og I er blitt sådanne som trenger til melk, ikke fast føde.
Ko da yake yanzu kam, ya kamata ku zama masu koyarwa, duk da haka, ashe, ba ku wuce wani ya sake koya muku jigajigan farko na Maganar Allah ba? har ya zamana sai an ba ku madara ba abinci mai tauri ba?
13 For hver den som får melk, er ukyndig i rettferds ord, for han er jo et barn;
To, duk wanda yake madara ce abincinsa, bai kware da maganar adalci ba, kamar jariri yake.
14 men fast føde er for voksne, for dem som ved bruken har sine sanser opøvd til å skille mellem godt og ondt.
Amma abinci mai tauri, ai, na manya ne, wato wadanda hankalinsu ya horu yau da kullum, don su rarrabe nagarta da mugunta.