< Hebreerne 2 >
1 Derfor må vi så meget mere gi akt på det vi har hørt, forat vi ikke skal drive bort derfra.
Dole mu ƙara mai da hankali sosai ga abubuwan da muka ji, don kada mu kauce.
2 For dersom det ord som var talt ved engler, stod fast, og hver overtredelse og ulydighet fikk sin fortjente lønn,
Gama in saƙon da aka faɗi ta bakin mala’iku ya zama tabbatacce, kuma kowane ƙeta umarni da rashin biyayya suka karɓi sakamakonsu da ya dace,
3 hvorledes skal da vi undfly om vi ikke akter så stor en frelse? - den som først blev forkynt ved Herren og derefter stadfestet for oss av dem som hadde hørt ham,
yaya za mu tsira in muka ƙyale irin wannan babban ceto? Wannan ceto, wanda Ubangiji ne ya fara sanar, aka kuma tabbatar mana ta bakin waɗanda suka ji shi.
4 idet Gud vidnet med, både ved tegn og under og mangehånde kraftige gjerninger og utdeling av den Hellige Ånd efter sin vilje.
Allah shi ma ya shaida ta wurin alamu, abubuwan banmamaki da mu’ujizai iri-iri, da kuma baye-bayen Ruhu Mai Tsarki da aka rarraba bisa ga nufinsa.
5 For det var ikke under engler han la den kommende verden, som vi taler om.
Ba ga mala’iku ba ne ya sa su yi mulkin duniya mai zuwa, wanda muke magana a kai ba.
6 Men en har på et sted vidnet så: Hvad er et menneske, at du kommer ham i hu, eller et menneskes sønn, at du akter på ham?
Amma akwai wani wurin da wani ya shaida cewa, “Mene ne mutum, da kake tuna da shi, ɗan mutum da kake kula da shi?
7 Du gjorde ham lite ringere enn englene; med herlighet og ære kronte du ham, og satte ham over dine henders gjerninger;
Ka sa shi ƙasa kaɗan da darajar mala’iku; ka naɗa shi da ɗaukaka da girma,
8 alle ting la du under hans føtter. For idet han underla ham alle ting, undtok han intet som ikke er ham underlagt; men nu ser vi ennu ikke at alle ting er ham underlagt;
ka kuma sa kome a ƙarƙashin ƙafafunsa.” Ta wurin sa kome a ƙarƙashinsa, Allah bai bar wani abu da bai sa a ƙarƙashinsa ba. Duk da haka a yanzu ba mu ga kowane abu a ƙarƙashinsa ba.
9 men den som var gjort lite ringere enn englene, Jesus, ham ser vi, fordi han led døden, kronet med herlighet og ære, forat han ved Guds nåde skulde smake døden for alle.
Sai dai muna ganin Yesu, wanda aka mai da shi ƙasa kaɗan da darajar mala’iku, yanzu kuwa an naɗa shi da ɗaukaka da girma domin yă sha wahalar mutuwa, domin ta wurin alherin Allah yă ɗanɗana mutuwa saboda kowa.
10 For det sømmet sig for ham for hvis skyld alle ting er til, og ved hvem alle ting er til, da han førte mange barn til herlighet, gjennem lidelser å fullende deres frelses høvding.
Ta wurin kawo’ya’ya masu yawa zuwa ga ɗaukaka, ya dace cewa Allah, wanda dominsa da kuma ta wurinsa ne kome yake kasancewa, ya sa tushen cetonsu yă zama cikakke ta wurin shan wahala.
11 For både den som helliggjør, og de som helliggjøres, er alle av en; derfor skammer han sig ikke ved å kalle dem brødre,
Da shi wanda yake tsarkake mutane da kuma su waɗanda ake tsarkakewa duk’yan iyali ɗaya ne. Saboda haka Yesu ba ya kunyan kiransu’yan’uwansa.
12 når han sier: Jeg vil kunngjøre ditt navn for mine brødre, midt i menigheten vil jeg lovsynge dig.
Ya ce, “Zan sanar da sunanka ga’yan’uwana; a gaban jama’a zan rera yabonka.”
13 Og atter: Jeg vil sette min lit til ham. Og atter: Se, her er jeg og de barn som Gud har gitt mig.
Har wa yau ya ce, “Zan dogara gare shi.” Ya kuma ce, “Ga ni, da’ya’yan da Allah ya ba ni.”
14 Eftersom da barnene har del i blod og kjød, fikk også han i like måte del deri, forat han ved døden kunde gjøre til intet den som hadde dødens velde, det er djevelen,
Da yake’ya’yan suna da nama da jini, shi ma sai ya ɗauki kamanninsu na mutum domin ta wurin mutuwarsa yă hallaka wanda yake riƙe da ikon mutuwa, wato, Iblis
15 og utfri alle dem som av frykt for døden var i trældom all sin livstid.
ya kuma’yantar da waɗanda dukan rayuwarsu tsoron mutuwa ya riƙe su cikin bauta.
16 For engler tar han sig jo ikke av, men Abrahams ætt tar han sig av;
Gama tabbatacce ba mala’iku ne ya taimaka ba, sai dai zuriyar Ibrahim.
17 derfor måtte han i alle ting bli sine brødre lik, forat han kunde bli en miskunnelig og trofast yppersteprest for Gud til å gjøre soning for folkets synder.
Saboda wannan dole a mai da shi kamar’yan’uwansa ta kowace hanya, domin yă zama babban firist mai aminci da mai jinƙai cikin hidima ga Allah, yă kuma miƙa hadayar sulhu saboda zunuban mutane.
18 For derved at han selv har lidt og har vært fristet, kan han komme dem til hjelp som blir fristet.
Domin shi kansa ya sha wahala sa’ad da aka gwada shi, yana iya taimakon waɗanda ake yi wa gwaji.