< 2 Korintierne 4 >

1 Derfor, da vi har denne tjeneste, eftersom vi har fått miskunn, så taper vi ikke motet;
Saboda haka, da yake ta wurin jinƙan Allah ne muke da wannan hidima, ba za mu fid da zuciya ba.
2 men vi har sagt oss løs fra alle skammelige snikveier og farer ikke frem med list, heller ikke forfalsker vi Guds ord, men ved å kunngjøre sannheten anbefaler vi oss til alle menneskers samvittighet for Guds åsyn.
Ba ruwanmu da ɓoye-ɓoye na munafuncin da suke abubuwan kunya. Ba ruwanmu da ruɗu, ko yin ƙarya da kalmar Allah. Sai dai muna faɗin gaskiya a fili. Ta haka ne kowa zai yi shaidar gaskiyarmu a gaban Allah cikin zuciyarsa.
3 Er da enn vårt evangelium skjult, så er det skjult blandt dem som går fortapt,
Ko da bishararmu a rufe take, tana a rufe ne ga waɗanda suke hallaka.
4 i hvem denne verdens gud har forblindet de vantros sinn, forat lyset fra evangeliet om Kristi herlighet, han som er Guds billede, ikke skal skinne for dem. (aiōn g165)
Allahn zamanin nan ya makanta hankulan marasa ba da gaskiya, yadda har ba za su iya ganin hasken bishara ta ɗaukakar Kiristi ba, wanda yake kamannin Allah. (aiōn g165)
5 For vi forkynner ikke oss selv, vi forkynner Kristus Jesus som Herre, oss derimot som eders tjenere for Jesu skyld.
Gama ba wa’azin kanmu muke yi ba, sai dai na Yesu Kiristi, a kan shi ne Ubangiji, mu kuma bayinku saboda Yesu.
6 For Gud, som bød at lys skulde skinne frem av mørke, han er den som også har latt det skinne i våre hjerter, forat kunnskapen om Guds herlighet i Jesu Kristi åsyn skulde stråle frem fra oss.
Domin shi Allah wanda ya ce, “Bari haske yă haskaka daga duhu,” ya sa haskensa ya haskaka a cikin zukatanmu, don yă ba mu hasken sanin ɗaukakar Allah a fuskar Kiristi.
7 Men vi har denne skatt i lerkar, forat den rike kraft skal være av Gud og ikke av oss,
Amma muna da wannan dukiya a cikin tulunan yumɓu, don a nuna wannan mafificin ikon nan daga Allah ne, ba daga gare mu ba.
8 idet vi alltid er i trengsel, men ikke kuet, tvilende, men ikke mistvilende,
A matse muke a kowane gefe, sai dai ba a gurgunta mu ba. An rikitar da mu, amma ba mu fid da zuciya ba.
9 forfulgt, men ikke opgitt, nedslått, men ikke tilintetgjort -
An tsananta mana, amma ba a yashe mu ba, an fyaɗe mu da ƙasa, amma ba a hallaka mu ba.
10 alltid bærende Jesu død med oss i legemet, forat også Jesu liv skal åpenbares i vårt legeme.
Kullum muna ɗauke da mutuwar Yesu a jikinmu, domin ran Yesu yă bayyana a jikinmu.
11 For ennu mens vi lever, overgis vi stadig til døden for Jesu skyld, forat også Jesu liv skal åpenbares i vårt dødelige kjød.
Muddin muna a raye, kullum zaman mutuwa muke yi saboda Yesu, don a bayyana ran Yesu ta wurin jikin nan namu mai mutuwa.
12 Således er da døden virksom i oss, men livet i eder.
Ta haka, mutuwa tana aiki a cikinmu, ku kuwa rai a cikinku.
13 Men eftersom vi har den samme troens Ånd - efter det som er skrevet: Jeg trodde, derfor talte jeg - så tror vi og, derfor taler vi og,
A rubuce yake cewa, “Na gaskata; saboda haka na yi magana.” Da wannan ruhun bangaskiya ne mu ma muka gaskata, saboda haka muke magana.
14 for vi vet at han som opvakte den Herre Jesus, skal også opvekke oss med Jesus og stille oss frem sammen med eder.
Domin mun san cewa shi da ya tā da Ubangiji Yesu daga matattu, zai tashe mu mu ma tare da Kiristi, yă kuma miƙa mu a gabansa tare da ku.
15 For det skjer alt sammen for eders skyld, forat nåden kan utbrede sig til dess flere og virke rikelig takksigelse til Guds ære.
Duk wannan fa don amfaninku ne, domin alherin nan da yake bazuwa zuwa ga mutane masu yawa, yă zama dalilin godiya mai yawa ga ɗaukakar Allah.
16 Derfor taper vi ikke motet, men om og vårt utvortes menneske går til grunne, så fornyes dog det innvortes dag for dag.
Saboda haka, ba mu fid da zuciya ba. Ko da yake a waje, jikinmu mai mutuwa yana lalacewa, amma can ciki, ana sabunta mu kowace rana.
17 For vår trengsel, som er kortvarig og lett, virker for oss en evig fylde av herlighet i overmål på overmål, (aiōnios g166)
Don wannan’yar wahalar tamu mai saurin wucewa, ita take tanadar mana madawwamiyar ɗaukaka mai yawa, fiye da kwatanci. (aiōnios g166)
18 såsom vi ikke har det synlige for øie, men det usynlige; for det synlige er timelig, men det usynlige evig (aiōnios g166)
Domin ba abubuwan da ido yake gani ne muke dubawa ba, sai dai marasa ganuwa. Gama abubuwan da ake gani masu saurin wucewa ne, marasa ganuwa kuwa, madawwama ne. (aiōnios g166)

< 2 Korintierne 4 >