< 1 Jaona 2 >

1 Ry keleiakoo, isokirako o raha zao tsy handilara’ areo. Aa naho eo ty mandilatse, le manam-pañalañalañe aman-dRae tika, Iesoà Norizañey, i Vantañey.
’Ya’yana ƙaunatattu, ina rubuta muku wannan ne don kada ku yi zunubi. Amma in wani ya yi zunubi, muna da wani wanda yake magana da Uba don taimakonmu, wato, Yesu Kiristi, Mai Adalci.
2 Ie ty fañeferañe o hakeon-tikañeo, tsy ty antikañ’ avao fa a ty voatse toy iaby.
Shi ne hadayar kafara saboda zunubanmu, kuma ba don namu kaɗai ba amma har ma da zunuban duniya duka.
3 Zao ty aharendrehañe t’ie mahafohiñe aze, le t’ie mañambeñe o lili’eo.
Ta haka za mu tabbata cewa mun san shi in muna yin biyayya da umarnansa.
4 Ie manao ty hoe: Fantako re, fe tsy mañambeñe o lili’eo ro remborake, vaho tsy ama’e ty hatò.
Mutumin da ya ce, “Na san shi,” amma ba ya yin abin da ya umarta, maƙaryaci ne, gaskiya kuwa ba ta cikinsa.
5 Aa ndra ia ia mañambeñe o tsara’eo, le fonitse ama’e ao ty fikokoañe an’ Andrianañahare. Zao ty ahafohinañe t’ie ama’e:
Amma in wani ya yi biyayya da maganarsa, ƙaunar Allah ta zama cikakkiya ke nan a cikinsa. Ta haka muka san cewa muna cikinsa.
6 ze manao te mimoneñe ama’e ao, tsy mahay tsy mañavelo amy fañaveloa’ey.
Duk wanda ya ce yana rayuwa a cikinsa dole yă yi tafiya kamar yadda Yesu ya yi.
7 O ry rañetseo, tsy isokirako lily vao, fa i lily haehae tama’ areo am-pifo­to­rañ’ añey. I lily taoloy i tsara jinanji’ areoy.
Abokaina ƙaunatattu, ba sabon umarni nake rubuta muku ba, a’a, daɗaɗɗen umarnin nan ne, wanda kuke da shi tun farko. Wannan tsohon umarni shi ne saƙon da kuka riga kuka ji.
8 Tovo’e, isokirako lily vao, ze tò ama’e naho ama’ areo, amy te mihelañ’ añe i ieñey vaho mireandreañe i toe hazàvañey.
Duk da haka ina rubuta muku sabon umarni; ana ganin gaskiyar umarnin a cikinsa da kuma cikinku, gama duhu yana shuɗewa, haske na gaskiya kuwa yana haskakawa.
9 Ze manao te an-kazavañe f’ie malain-dongo le mbe añ’ieñe ao.
Duk wanda ya ce yana cikin haske yana kuma ƙin ɗan’uwansa, ashe a duhu yake har yanzu.
10 Mimoneñe an-kazavañe ao ty mikoko rahalahy, le tsy ama’e ty hahatsikapy aze.
Duk wanda yake ƙaunar ɗan’uwansa, a cikin hasken yake rayuwa ke nan, kuma babu wani abin da yake cikinsa da zai sa yă yi tuntuɓe.
11 Fe añ’ ieñe ao ty malain-dongo le an-ka­moro­moroñañe ao ty andenà’e, vaho alik’ ama’e ty hombà’e fa nigoà’ i ieñey o maso’eo.
Amma duk wanda yake ƙin ɗan’uwansa, cikin duhu yake, yana kuma tafiya cikin duhu ke nan; bai ma san inda za shi ba, domin duhun ya makanta shi.
12 Manokitse ama’ areo iraho ry keleiako, fa votso-kakeo añamy tahina’ey.
Ina rubuta muku,’ya’yana ƙaunatattu, domin an gafarta muku zunubanku saboda sunansa.
13 Manokitse ama’ areo iraho ry aba, amy te fohi’ areo i boak’am-baloha’ey. Manokitse ama’ areo iraho ry ajalahio, fa nahagioke i ratiy. Nanokitse ama’ areo iraho ry kabìy, amy te mahafohiñe an-dRae.
Ina rubuta muku, ubanni, domin kun san shi wanda yake tun farko. Ina rubuta muku, samari, domin kun ci nasara a kan mugun nan.
14 Nanokitse ama’ areo iraho, ry aba, amy te fohi’ areo i boak’am-baloha’ey. Nanokitse ama’ areo iraho ry ajalahy, amy te maozatse, naho mimoneñe ama’ areo ao o tsaran’ Añahareo, vaho fa nahareketse i ratiy.
Ina rubuta muku,’ya’yana ƙaunatattu, domin kun san Uba. Ina rubuta muku, ubanni, domin kun san shi wanda yake tun farko. Ina rubuta muku, samari, domin kuna da ƙarfi, maganar Allah kuwa tana zaune a cikinku, kun kuma ci nasara a kan mugun nan.
15 Ko mikoko ty voatse toy, ndra o raha ami’ty voatse toio. Naho eo ty mikoko ty voatse toy, tsy ama’e ty fikokoan-dRae.
Kada ku ƙaunaci duniya, ko wani abin da yake cikinta. In wani yana ƙaunar duniya, ƙaunar Uba ba ta cikinsa.
16 Toe tsy boak’ aman-dRae fa hirik’ ami’ty voatse toy ze an-tane atoy iaby—ty hadrao’ o nofotseo, ty fihañam-pihaino naho ty fisengean-kaveloñe.—
Gama duk abin da yake na duniya, kamar sha’awace-sha’awacen mutuntaka, sha’awar idanunsa, da kuma taƙama da abin da yake da shi, yake kuma yi, ba daga wurin Uba suke fitowa ba sai dai daga duniya.
17 Fa mihelañe añe ty voatse toy naho o ìna rati’eo, fe ho veloñe nainai’e ty manao o satrin’ Añahareo. (aiōn g165)
Duniya da sha’awace-sha’awacenta suna shuɗewa, amma mutumin da yake aikata nufin Allah, zai rayu har abada. (aiōn g165)
18 Ry keleiako, fa sa sahengaha’e toy; ie nahajanjiñe te ho avy i norizam-bìlañey, toe maro ty norizam-bìlañe pok’eo henaneo. Izay ty aharendrehañe t’ie fa sa honka’e.
’Ya’yana ƙaunatattu, waɗannan su ne kwanakin ƙarshe; kuma kamar yadda kuka ji cewa magabcin Kiristi yana zuwa, ko yanzu ma abokan gāban Kiristi da yawa sun zo. Ta haka muka san cewa kwanakin ƙarshe sun iso.
19 Nienga an-tika iereo, fa toe tsy nimpiaman-tika. Naho toe ni-mpitraok’ aman-tika le mbe ho ni-mpiaman-tikañ’ avao; fa izay ty mampidodea te tsy ni-mpiaman-tika.
Waɗannan masu gāba da Kiristi suna cikinmu a dā, amma sun bar mu, don tun dā ma su ba namu ba ne. Ai, da su namu ne, da har yanzu suna tare da mu. Amma sun bar mu, wannan ya nuna a fili cewa su ba namu ba ne.
20 Fa nanàvoñe anahareo i Masiñey, vaho hene fohi’areo.
Amma ku kam, kuna da shafewa daga wurin Mai Tsarkin nan, kuma dukanku kun san gaskiya.
21 Tsy t’ie tsy mahafohiñe ty hatò ty nisokirako fa t’ie mahafohiñe, vaho tsy amam-bande ty hatò.
Ina rubuta muku ba domin ba ku san gaskiya ba ne, a’a, sai dai domin kun santa, kun kuma san cewa babu yadda ƙarya za tă fito daga gaskiya.
22 Ia ty remborake naho tsy ty mandietse te Iesoà i Norizañey. Norizam-bìlan-dre, mpitety an-dRae naho i Anakey.
Wane ne maƙaryaci? Ai, shi ne mutumin da yake mūsun cewa Yesu shi ne Kiristi. Irin wannan mutum shi ne magabcin Kiristi, ya yi mūsun Uban da kuma Ɗan.
23 Tsy aman-dRae ze mitety i Anakey; aman-dRae ka ze miantoke i Anakey.
Ba wanda yake mūsun Ɗan, sa’an nan yă ce yana da Uban; duk wanda ya yarda da Ɗan, yana da Uban a cikinsa ke nan.
24 Aa le ampi­moneño ama’ areo ao i jinanji’ areo tam-baloha’ey. Ie imoneña’ i jinanjiñe am-baloha’ey, le himoneñe amy Anakey naho aman-dRae ao nahareo.
Ku lura fa cewa abin da kuka ji daga farko, bari yă ci gaba da kasance a cikinku. In kuwa ya ci gaba da zama a cikinku, za ku kasance a cikin Ɗan, da kuma a cikin Uban.
25 Zao i nampitamae’e antikañey, le i haveloñe nainai’e tsy modoy. (aiōnios g166)
Wannan shi ne abin da ya yi mana alkawari, wato, rai madawwami. (aiōnios g166)
26 Nisokireko ama’ areo irezao ty amo mipay hamañahio.
Ina rubuta muku waɗannan abubuwa ne game da waɗanda suke ƙoƙari su sa ku kauce.
27 F’ie, toe imo­neña’ i Fanavonañe niazo’ areo ama’ey, le tsy ipaiañe ka te hatoro ondaty, fa hitoroa’ i Fanavona’ey ze he’e, ie ro to, fa tsy vande—aa ty amy nañòha’e anahareoy, le imoneño.
Game da ku kuwa, shafan nan da kuka karɓa daga gare shi tana nan a cikinku, ba kwa kuma bukata wani yă koyar da ku. Amma kamar yadda shafan nan tasa tana koya muku kome, ita kuwa gaskiya ce ba ƙarya ba, yadda dai ta koya muku, to, sai ku zauna a cikinsa.
28 Ie amy zao ry keleiako, imo­neño, hahatokisan-tika amy fiboaha’ey, tsy hitsolofìñe an-kasalarañe te totsake.
Yanzu fa, ya ku’ya’yana ƙaunatattu, sai ku ci gaba a cikinsa, domin sa’ad da ya bayyana, mu iya tsaya gabagadi babu kunya a dawowarsa.
29 Kanao rendre’ areo t’ie vantañe, le fohi’ areo te hene mitoloñe ami’ty fahiti’e ze anake nampia­reñe’e.
In kun san cewa shi mai adalci ne, to, kun dai san cewa duk mai aikata abin da yake daidai haifaffensa ne.

< 1 Jaona 2 >