< Vēstule Ebrējiem 9 >
1 Tad nu gan arī tai pirmai derībai bija Dieva kalpošanas likumi un laicīgs svētums.
To ko da alkawarin farko ma ya na da wurin sujada da kuma ka'idojin sujada a nan duniya.
2 Jo Dieva telts bija uzcelta: tai priekšējā bija tas lukturis un tas galds un tās Dieva priekšā noliktas maizes; tā top saukta tā svētā vieta.
Domin a cikin alfarwar akwai daki da aka shirya, daki na waje wanda ake kira wuri mai tsarki. A wannan wuri akwai kebabbun fitilu, akwai teburi da kuma gurasa.
3 Bet aiz tā otra priekškaramā auta tas dzīvoklis, kas top saukts tā vissvētākā vieta;
Kuma bayan labule na biyun akwai wani daki, wanda ake kira wuri mafi tsarki.
4 Tam bija tas kvēpināmais zelta altāris un tas derības šķirsts, vispāri pārvilkts ar zeltu, kurā tas zelta trauciņš ar to debess maizi un Ārona zizlis, kas bija zaļojis, un tie derības galdiņi.
Yana da bagadin zinariya domin turare. Yana kuma da akwatin alkawarin, wanda aka lailaye shi gaba daya da zinariya. A cikinsa a kwai kaskon zinariya dake dauke da manna, da sandar Haruna wadda tayi toho, da kuma allunan duwatsu na alkawarin.
5 Un virsū pār to tie godības ķerubi, kas to derības šķirsta vāku apēnoja: par to tagad nav jārunā īpaši.
A sama da akwatin alkawarin akwai siffofin kerubobi masu daukaka da suke wa marfin jinkai inuwa, wadanda yanzu ba zamu iya yin bayani akansu ba daki daki.
6 Kad nu šās lietas tā sataisītas, tad tie priesteri gan allažiņ ieiet tai dzīvokļa priekšējā daļā, Dieva kalpošanas darbus darīdami,
Bayan an shirya wadannan abubuwa, firistocin alfarwar sukan shiga daki na wajen alfarwar akai akai suna aikin hidimominsu.
7 Bet tai otrā tas augstais priesteris vien vienreiz par gadu, ne bez asinīm, ko viņš upurē par sava paša un to ļaužu noziegumiem;
Amma babban firist din ne kadai yake shiga daki na biyun, sau daya tak a shekara, kuma tilas sai tare da jinin hadaya domin kansa, da kuma domin laifuffukan mutane da a kayi ba dagangan ba.
8 Caur to Svētais Gars rāda, ka ceļš uz to svēto vietu vēl nav parādīts, kamēr tā dzīvokļa priekšēja daļa pastāv;
Ruhu Mai Tsarki yana nuna cewar ba'a riga an bayyana hanyar zuwa wuri mafi Tsarki ba muddin alfarwar nan ta farko na a tsaye.
9 Tā ir to tagadēju laiku līdzība, pēc kuras upurē dāvanas un upurus, kas to, kas kalpo, nevar pilnīgu darīt pēc zināmas sirds,
Wannan ya zama bayani ne game da lokacin yanzu. Da kyaututtuka da hadayu dukka da ake mikawa basu iya sun kammala lamirin mai yin sujadar ba.
10 Bet tie tikai līdz ar ēdieniem un dzērieniem un daudzkārtīgām mazgāšanām kā ārīgi miesas likumi uzlikti līdz tam laikam, kad viss labāki tiks pārtaisīts.
Abinci ne da abin sha kawai wadanda aka hada da bukukuwan wanke wanke dabam dabam. Wadannan duka tsare tsare ne da aka shirya a dinga yi a zahiri har sai an shirya sabuwar ka'ida.
11 Bet Kristus, to nākamo labumu augstais priesteris, ir nācis un caur jo lielu un jo pilnīgu dzīvokli, ne rokām taisītu - tas ir, ne no šīs radības, -
Almasihu yazo a matsayin babban firist na abubuwa masu kyau da suka zo, ta wurin alfarwa babba, kammalalla kuma mafi tsarki wadda ba hannuwan mutane suka gina ba, wadda ba ta wannan duniyar aka halicce ta ba. Amma almasihu ya zo a matsayin babban firist na abubuwa masu kyau da ke zuwa.
12 Nedz ar āžu un teļu asinīm, bet ar Savām paša asinīm Viņš vienreiz ir iegājis tai svētā vietā un sagādājis mūžīgu pestīšanu. (aiōnios )
Ba ta jinin awaki da 'yan, maruka bane, amma Almasihu da jininsa ya shiga wuri mafi tsarki sau daya tak domin kowa dukka ya karbo mana fansa ta har abada. (aiōnios )
13 Jo ja vēršu un āžu asinis un pelni no jaunas govs nešķīstos apslacinājot šķīsta uz miesas šķīstību;
To idan jinin awaki da na bajimai da yayyafa tokar karsana bisa wadanda suka bata tsarkinsu yana tsarkake su ya wanke jikkunansu.
14 Cik vairāk Kristus asinis, kas caur to mūžīgo Garu Sevi pašu bezvainīgu Dievam ir upurējis, šķīstīs jūsu zināmu sirdi no nedzīviem darbiem, kalpot Tam dzīvam Dievam? (aiōnios )
To balle kuma jinin Almasihu, wanda ta wurin Ruhu madawwami ya mika kansa hadaya marar aibi ga Allah, wanda yake wanke lamirinmu daga matattun ayyuka domin muyi bautar Allah mai rai? (aiōnios )
15 Un tādēļ Viņš ir tās jaunās derības (testamenta) vidutājs, lai, kad nāve bija notikusi par atpestīšanu no tām pārkāpšanām, kas bija apakš tās pirmās derības, tie, kas ir aicināti, dabū to apsolīto mūžīgo mantību. (aiōnios )
Domin wannan dalili, Almasihu shine magamin sabon alkawari. Wannan kuwa ya kasance ne domin anyi mutuwar da ta 'yantar da wadanda ke karkashin tsohon alkawari daga sakamakon zunubansu, saboda wadanda Allah ya kira su karbi alkawarin gadonsu madawwami. (aiōnios )
16 Jo kur ir iestādījums(testaments), tur tam iestādītajam vajag būt mirušam.
Gama duk inda wani ya rubuta wasiyya ya bari, dole ne a tabbatar da mutuwar wanda yayi wasiyyar nan.
17 Jo iestādījums (testaments) ir stiprs, kad tas iestādītājs miris; jo tas nekad nav spēkā, kamēr viņš vēl dzīvs, kas to cēlis.
Gama sai inda akayi mutuwa ake amfani da wasiyya, amma ba ta da amfani idan wanda ya rubuta ta yana nan da rai.
18 Tāpēc arī tā pirmā derība nav iecelta bez asinīm.
Ko alkawari na farko bai tabbata ba sai tare da jini.
19 Jo kad Mozus visus likumus pēc bauslības bija runājis uz visiem ļaudīm, tad tas ņēma teļu un āžu asinis ar ūdeni un purpura vilnu un īzapu un apslacināja pašu to grāmatu kā arī visus ļaudis,
Gama bayan Musa ya bada dukkan dokoki da ke cikin shari'ar ga dukkan mutanen, sai ya dauki jinin 'yan marukan da awakin, tare da ruwa, da jan yadi, da reshen itacen doddoya mai soso, ya yayyafa bisa mutanen da kuma littafin dokokin.
20 Sacīdams: šīs ir tās derības asinis, ko Dievs jums ir pavēlējis.
Daga nan yace, “Wannan ne jinin alkawarin da Allah ya bayar da dokoki gareku.”
21 Tā līdzīgi viņš arī Dieva telti un visus Dieva kalpošanas rīkus apslacināja ar asinīm.
Ta haka kuma, ya yayyafa jinin bisa alfarwar da dukkan kayayyakin da ke cikinta wanda ake hidimar firistanci da su.
22 Un gandrīz viss ar asinīm top šķīstīts pēc bauslības, un bez asins izliešanas nenotiek piedošana.
Kuma bisa ga shari'a, kusan komai da jini ake tsarkake shi. Idan babu zubar da jini to babu gafarar zunubi.
23 Tad nu tām debes' lietu līdzībām tā vajag tapt šķīstītām, bet tām debes' lietām pašām caur labākiem upuriem, nekā šie ir.
Saboda haka ya zama tilas wadannan kayayyaki na kwaikwayon abubuwan dake cikin sama a tsarkake su da hadayar dabbobi. Duk da haka abubuwa na sama dole a tsarkake su da hadaya mafi kyau.
24 Jo Kristus nav iegājis tai rokām taisītā svētā vietā, caur ko tā patiesā top zīmēta, bet pašās debesīs, ka tas tagad parādītos priekš Dieva vaiga par mums;
Domin Almasihu bai shiga cikin wuri mafi tsarki da aka yi da hannuwa ba, wanda kwaikwayo ne kawai na abin da ke na gaske. Maimakon hakan, ya shiga cikin samaniya da kanta, sa'an nan yaje gaban Allah domin mu.
25 Nedz ka Viņš Sevi pašu daudzreiz upurētu, tā kā tas augstais priesteris ik gadus svētā vietā ieiet ar svešām asinīm.
Bai je wurin don ya mika kansa sau da yawa, kamar yadda firist din alfarwa yake yi ba, wanda yake shiga wuri mafi tsarki kowacce shekara da jinin wata dabba.
26 Citādi Viņam būtu pienācies daudzreiz ciest no pasaules iesākuma; bet tagad Viņš vienreiz laiku galā ir parādījies, grēku iznīcināt caur Savu paša upuri. (aiōn )
Idan haka ne, to dole ke nan ya sha wahala akai akai tun farkon duniya. Amma yanzu sau daya ne tak aka bayyana shi a karshen zamanai domin ya kauda zunubi ta wurin mika hadayar kansa. (aiōn )
27 Un tā, kā cilvēkiem ir nolikts vienreiz mirt un pēc tam tā tiesa:
Kamar yadda aka kaddara wa kowa ya mutu sau daya tak, kuma bayan haka sai shari'a.
28 Tāpat arī Kristus, vienreiz upurēts, daudz ļaužu grēkus atņemt, taps redzēts otru reizi bez grēka no tiem, kas Viņu gaida, uz mūžīgu dzīvošanu.
Haka kuma Almasihu, wanda aka mika shi sau daya tak domin ya dauke zunuban mutane da yawa, zai kuma bayyana karo na biyu, ba domin yin aikin kawar da zunubi ba, amma domin ceton wadanda suke jiran zuwansa da hakuri.