< Zaccharias Propheta 1 >

1 in mense octavo in anno secundo Darii factum est verbum Domini ad Zacchariam filium Barachiae filium Addo prophetam dicens
A wata na bakwai na shekara ta biyu ta mulkin Dariyus, maganar Ubangiji ta zo wa annabi Zakariya ɗan Berekiya ɗan Iddo.
2 iratus est Dominus super patres vestros iracundia
“Ubangiji ya yi fushi sosai da kakanninku.
3 et dices ad eos haec dicit Dominus exercituum convertimini ad me ait Dominus exercituum et convertar ad vos dicit Dominus exercituum
Saboda haka ka gaya wa mutanen, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ku komo gare ni,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki, ‘ni kuma zan komo gare ku,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki.
4 ne sitis sicut patres vestri ad quos clamabant prophetae priores dicentes haec dicit Dominus exercituum convertimini de viis vestris malis et cogitationibus vestris pessimis et non audierunt neque adtenderunt ad me dicit Dominus
Kada ku zama kamar kakanninku, waɗanda annabawa na dā suka ce musu, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ku juya daga mugayen hanyoyinku da mugayen abubuwan da kuke yi.’ Amma ba su saurara ba, ko ma su kula da ni, in ji Ubangiji.
5 patres vestri ubi sunt et prophetae numquid in sempiternum vivent
Yanzu ina kakanninku suke? Annabawan kuma fa, sun rayu har abada ne?
6 verumtamen verba mea et legitima mea quae mandavi servis meis prophetis numquid non conprehenderunt patres vestros et conversi sunt et dixerunt sicut cogitavit Dominus exercituum facere nobis secundum vias nostras et secundum adinventiones nostras fecit nobis
Amma maganata da dokokina da na umarta ta wurin bayina annabawa fa, ashe, ba su tabbata ba a kan kakanninku? “Sa’an nan suka tuba suka ce, ‘Ubangiji Maɗaukaki ya yi mana daidai abin da hanyoyinmu suka cancanci mu samu, kamar dai yadda ya yi niyya yi.’”
7 in die vicesima et quarta undecimo mense sabath in anno secundo Darii factum est verbum Domini ad Zacchariam filium Barachiae filium Addo prophetam dicens
A rana ta ashirin da huɗu ga watan goma sha ɗaya, wato, watan Shebat, a shekara ta biyu ta Dariyus, maganar Ubangiji ta zo wa annabi Zakariya ɗan Berekiya ɗan Iddo.
8 vidi per noctem et ecce vir ascendens super equum rufum et ipse stabat inter myrteta quae erant in profundo et post eum equi rufi varii et albi
Da dare, na ga wahayi, a gabana kuwa ga mutum a kan jan doki! Yana tsaye a cikin itatuwa masu furanni, a bayansa a cikin itatuwan ci-zaƙi, a bayansa kuwa akwai dawakai masu ruwan ja, ruwan ƙasa-ƙasa da kuma ruwan fari.
9 et dixi quid sunt isti domine mi et dixit ad me angelus qui loquebatur in me ego ostendam tibi quid sint haec
Sai na yi tambaya na ce, “Mene ne waɗannan ranka yă daɗe?” Mala’ikan da yake magana da ni ya amsa ya ce, “Zan nuna maka mene ne su.”
10 et respondit vir qui stabat inter myrteta et dixit isti sunt quos misit Dominus ut perambularent terram
Sai mutumin da yake tsaye cikin itatuwan ci-zaƙin ya yi bayani cewa, “Su ne waɗanda Ubangiji ya aika ko’ina a duniya.”
11 et responderunt angelo Domini qui stabat inter myrteta et dixerunt perambulavimus terram et ecce omnis terra habitatur et quiescit
Sai suka ce wa mala’ikan da yake tsaye cikin itatuwan ci-zaƙin, “Mun ratsa ko’ina a duniya, sai muka ga duniya duka tana zaman lafiya.”
12 et respondit angelus Domini et dixit Domine exercituum usquequo tu non misereberis Hierusalem et urbium Iuda quibus iratus es iste septuagesimus annus est
Sa’an nan mala’ikan Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji Maɗaukaki, har yaushe za ka ci gaba da ƙi nuna wa Urushalima da kuma garuruwan Yahuda jinƙai, waɗanda kake fushi da su shekarun nan saba’in?”
13 et respondit Dominus angelo qui loquebatur in me verba bona verba consolatoria
Sai Ubangiji ya yi wa mala’ikan da ya yi magana da ni magana da kalmomi masu daɗi da kuma masu ta’azantarwa.
14 et dixit ad me angelus qui loquebatur in me clama dicens haec dicit Dominus exercituum zelatus sum Hierusalem et Sion zelo magno
Sai mala’ikan da yake magana da ni ya ce, “Ka yi shelar maganan nan, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ina kishi domin Urushalima da Sihiyona,
15 et ira magna ego irascor super gentes opulentas quia ego iratus sum parum ipsi vero adiuverunt in malum
amma ina fushi da ƙasashen da suke ji suna zaman lafiya, na ɗan yi fushina kawai, amma sai suka ƙara musu masifar.’
16 propterea haec dicit Dominus revertar ad Hierusalem in misericordiis domus mea aedificabitur in ea ait Dominus exercituum et perpendiculum extendetur super Hierusalem
“Saboda haka, ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Zan komo Urushalima da jinƙai, a can ne za a sāke gina gidana. Za a kuma miƙe ma’auni a bisa Urushalima,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki.
17 adhuc clama dicens haec dicit Dominus exercituum adhuc affluent civitates meae bonis et consolabitur Dominus adhuc Sion et eliget adhuc Hierusalem
“Ci gaba da yin shela, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Garuruwana za su sāke kwarara da wadata, Ubangiji kuma zai sāke yi wa Sihiyona ta’aziyya, yă kuma zaɓi Urushalima.’”
18 et levavi oculos meos et vidi et ecce quattuor cornua
Sa’an nan na dubi sama a gabana kuwa sai ga ƙahoni huɗu!
19 et dixi ad angelum qui loquebatur in me quid sunt haec et dixit ad me haec sunt cornua quae ventilaverunt Iudam et Israhel et Hierusalem
Na tambayi mala’ikan da yake mini magana, na ce, “Mene ne waɗannan?” Ya amsa mini ya ce, “Waɗannan su ne ƙahonin da suka watsar da Yahuda, Isra’ila da kuma Urushalima.”
20 et ostendit mihi Dominus quattuor fabros
Sa’an nan Ubangiji ya nuna mini maƙera guda huɗu.
21 et dixi quid isti veniunt facere qui ait dicens haec sunt cornua quae ventilaverunt Iudam per singulos viros et nemo eorum levavit caput suum et venerunt isti deterrere ea ut deiciant cornua gentium quae levaverunt cornu super terram Iuda ut dispergerent eam
Na yi tambaya na ce, “Mene ne waɗannan suke zuwa yi?” Ya amsa ya ce, “Waɗannan ne ƙahonin da suka watsar da Yahuda har ba wanda yake iya ɗaga kansa, amma maƙeran sun zo don su tsorata su su kuma saukar da ƙahonin ƙasashen nan waɗanda suka ɗaga ƙahoninsu gāba da ƙasar Yahuda don su warwatsa ta.”

< Zaccharias Propheta 1 >