< Canticum Canticorum 1 >

1
Waƙar Waƙoƙin Solomon.
2 osculetur me osculo oris sui quia meliora sunt ubera tua vino
Bari yă sumbace ni da sumbar bakinsa, gama ƙaunarka ta fi ruwan inabi zaƙi.
3 fraglantia unguentis optimis oleum effusum nomen tuum ideo adulescentulae dilexerunt te
Ƙanshin turarenka mai daɗi ne; sunanka kuwa kamar turaren da aka tsiyaye ne. Shi ya sa mata suke ƙaunarka!
4 trahe me post te curremus introduxit me rex in cellaria sua exultabimus et laetabimur in te memores uberum tuorum super vinum recti diligunt te
Ka ɗauke ni mu gudu, mu yi sauri! Bari sarki yă kai ni gidansa. Ƙawaye Muna farin ciki muna kuma murna tare da kai, za mu yabi ƙaunarka fiye da ruwan inabi. Ƙaunatacciya Daidai ne su girmama ka!
5 nigra sum sed formonsa filiae Hierusalem sicut tabernacula Cedar sicut pelles Salomonis
Ni baƙa ce, duk da haka kyakkyawa. Ya ku’yan matan Urushalima, ni baƙa ce kamar tentunan Kedar, kamar labulen tentin Solomon.
6 nolite me considerare quod fusca sim quia decoloravit me sol filii matris meae pugnaverunt contra me posuerunt me custodem in vineis vineam meam non custodivi
Kada ku harare ni domin ni baƙa ce, gama rana ta dafa ni na yi baƙa.’Ya’yan mahaifiyata maza sun yi fushi da ni suka sa ni aiki a gonakin inabi; na ƙyale gonar inabi na kaina.
7 indica mihi quem diligit anima mea ubi pascas ubi cubes in meridie ne vagari incipiam per greges sodalium tuorum
Faɗa mini, kai da nake ƙauna, ina kake kiwon garkenka kuma ina kake kai tumakinka su huta da tsakar rana. Me ya sa zan kasance kamar macen da aka lulluɓe kusa da garkunan abokanka?
8 si ignoras te o pulchra inter mulieres egredere et abi post vestigia gregum et pasce hedos tuos iuxta tabernacula pastorum
Ke mafiya kyau a cikin mata, in ba ki sani ba, to, ki dai bi labin da tumaki suke bi ki yi kiwon’yan awakinki kusa da tentunan makiyaya.
9 equitatui meo in curribus Pharaonis adsimilavi te amica mea
Ina kwatanta ke ƙaunatacciyata, da goɗiya mai jan keken yaƙin kayan Fir’auna.
10 pulchrae sunt genae tuae sicut turturis collum tuum sicut monilia
’Yan kunne sun ƙara wa kumatunki kyau, wuyanki yana da jerin kayan wuya masu daraja.
11 murenulas aureas faciemus tibi vermiculatas argento
Za mu yi’yan kunnenki na zinariya, da adon azurfa.
12 dum esset rex in accubitu suo nardus mea dedit odorem suum
Yayinda sarki yake a teburinsa, turarena ya bazu da ƙanshi.
13 fasciculus murrae dilectus meus mihi inter ubera mea commorabitur
Ƙaunataccena yana kamar ƙanshin mur a gare ni, kwance a tsakanin ƙirjina.
14 botrus cypri dilectus meus mihi in vineis Engaddi
Ƙaunataccena kamar tarin furanni jeji ne gare ni daga gonakin inabin En Gedi.
15 ecce tu pulchra es amica mea ecce tu pulchra oculi tui columbarum
Ke kyakkyawa ce, ƙaunatacciyata! Kai, ke kyakkyawa ce! Idanunki kamar na kurciya ne.
16 ecce tu pulcher es dilecte mi et decorus lectulus noster floridus
Kai kyakkyawa ne, ƙaunataccena! Kai, kana ɗaukan hankali! Gadonmu koriyar ciyawa ce.
17 tigna domorum nostrarum cedrina laquearia nostra cypressina
Al’ul su ne ginshiƙan gidanmu; fir su ne katakan rufin gidanmu.

< Canticum Canticorum 1 >