< Canticum Canticorum 7 >

1 quam pulchri sunt gressus tui in calciamentis filia principis iunctura feminum tuorum sicut monilia quae fabricata sunt manu artificis
Ƙafafunki a cikin takalma kyakkyawa ne, Ya diyar sarki! Tsarin ƙafafunki sun yi kamar kayan ado masu daraja, aikin hannun gwanin sassaƙa.
2 umbilicus tuus crater tornatilis numquam indigens poculis venter tuus sicut acervus tritici vallatus liliis
Cibinki kamar kwaf ne da bai taɓa rasa gaurayayyen ruwan inabi ba. Kwankwasonki ya yi kamar damin alkama wanda furen bi-rana ya kewaye.
3 duo ubera tua sicut duo hinuli gemelli capreae
Nonanki sun yi kamar bareyi biyu, tagwayen barewa.
4 collum tuum sicut turris eburnea oculi tui sicut piscinae in Esebon quae sunt in porta filiae multitudinis nasus tuus sicut turris Libani quae respicit contra Damascum
Wuyanki ya yi kamar hasumiyar hauren giwa. Idanunki sun yi kamar tafkin Heshbon kusa da ƙofar Bat Rabbim. Hancinki ya yi kamar hasumiyar Lebanon wadda take duban Damaskus.
5 caput tuum ut Carmelus et comae capitis tui sicut purpura regis vincta canalibus
Kanki ya yi miki rawani kamar Dutsen Karmel. Gashinki ya yi kamar shunayya; yakan ɗauke hankalin sarki.
6 quam pulchra es et quam decora carissima in deliciis
Kai! Ke kyakkyawa ce kuma kina sa ni jin daɗi, Ya ƙaunatacciya, da farin cikin da kike kawo!
7 statura tua adsimilata est palmae et ubera tua botris
Tsayinki ya yi kamar itacen dabino, kuma nonanki sun yi kamar’ya’yan itace.
8 dixi ascendam in palmam adprehendam fructus eius et erunt ubera tua sicut botri vineae et odor oris tui sicut malorum
Na ce, “Zan hau itacen dabino; zan kama’ya’yansa.” Bari nonanki su zama kamar nonna kuringa, ƙanshin numfashinki ya yi kamar gawasa,
9 guttur tuum sicut vinum optimum dignum dilecto meo ad potandum labiisque et dentibus illius ruminandum
kuma bakinki ya yi kamar ruwan inabi mafi kyau. Ƙaunatacciya Bari ruwan inabi yă wuce kai tsaye zuwa ga ƙaunataccena, yana gudu a hankali a leɓuna da kuma haƙora.
10 ego dilecto meo et ad me conversio eius
Ni ta ƙaunataccena ce, kuma sha’awarsa domina ne.
11 veni dilecte mi egrediamur in agrum commoremur in villis
Ka zo, ƙaunataccena, bari mu je bayan gari, bari mu kwana a ƙauye.
12 mane surgamus ad vineas videamus si floruit vinea si flores fructus parturiunt si floruerunt mala punica ibi dabo tibi ubera mea
Bari mu tafi gonar inabi da sassafe don mu ga ko kuringar ta yi’ya’ya, ko furanninsu sun buɗe, ko rumman sun yi fure, a can zan nuna maka ƙaunata.
13 mandragorae dederunt odorem in portis nostris omnia poma nova et vetera dilecte mi servavi tibi
Manta-uwa sun ba da ƙanshinsu, a bakin ƙofa kuwa akwai kowane abinci mai daɗi, sabo da tsoho, da na ajiye dominka, ƙaunataccena.

< Canticum Canticorum 7 >