< Canticum Canticorum 6 >

1 quo abiit dilectus tuus o pulcherrima mulierum quo declinavit dilectus tuus et quaeremus eum tecum
Ina ƙaunataccenki ya tafi, yake mafiya kyau cikin mata? Wace hanya ce ƙaunataccenki ya bi, don mu taimake ki nemansa.
2 dilectus meus descendit in hortum suum ad areolam aromatis ut pascatur in hortis et lilia colligat
Ƙaunataccena ya gangara zuwa lambunsa, zuwa inda fangulan kayan yaji suke, don yă yi kiwo a cikin lambun don kuma yă tattara furen bi-rana.
3 ego dilecto meo et dilectus meus mihi qui pascitur inter lilia
Ni na ƙaunataccena ce, ƙaunataccena kuma nawa ne; yana kiwo a cikin furen bi-rana.
4 pulchra es amica mea suavis et decora sicut Hierusalem terribilis ut castrorum acies ordinata
Ke kyakkyawa ce, ƙaunatacciyata, kamar Tirza, kyakkyawa kuma kamar Urushalima, mai daraja kamar mayaƙa da tutoti.
5 averte oculos tuos a me quia ipsi me avolare fecerunt capilli tui sicut grex caprarum quae apparuerunt de Galaad
Ki kau da idanu daga gare ni; gama suna rinjayata. Gashinki yana kama da garken awakin da suke gangarawa daga Gileyad.
6 dentes tui sicut grex ovium quae ascenderunt de lavacro omnes gemellis fetibus et sterilis non est in eis
Haƙoranki suna kama da garken tumakin da suke haurawa daga inda aka yi musu wanka. Kowanne yana tare da ɗan’uwansa; babu waninsu da yake shi kaɗai.
7 sicut cortex mali punici genae tuae absque occultis tuis
Kumatunki sun yi kamar rumman da aka tsaga biyu a cikin lulluɓinki.
8 sexaginta sunt reginae et octoginta concubinae et adulescentularum non est numerus
Sarauniyoyi sittin za su iya kasance a can, da ƙwarƙwarai tamanin da kuma budurwai da suka wuce ƙirge;
9 una est columba mea perfecta mea una est matris suae electa genetrici suae viderunt illam filiae et beatissimam praedicaverunt reginae et concubinae et laudaverunt eam
amma kurciyata, cikakkiyata, dabam take, tilo kuwa ga mahaifiyarta,’yar lele ga wadda ta haife ta.’Yan mata sun gan ta suka ce da ita mai albarka; sarauniyoyi da ƙwarƙwarai sun yabe ta.
10 quae est ista quae progreditur quasi aurora consurgens pulchra ut luna electa ut sol terribilis ut acies ordinata
Wace ce wannan da ta bayyana sai ka ce ketowar alfijir? Kyakkyawa kamar wata, mai haske kamar rana, mai daraja kamar taurari a jere?
11 descendi ad hortum nucum ut viderem poma convallis ut inspicerem si floruisset vinea et germinassent mala punica
Na gangara zuwa cikin itatuwan almon don in ga ƙananan itatuwan da suke girma a kwari, don in ga ko inabi sun yi’ya’ya ko rumman suna fid da furanni.
12 nescivi anima mea conturbavit me propter quadrigas Aminadab
Kafin in san wani abu, sha’awarta ta sa ni a cikin keken yaƙin sarkin mutanena.
13 revertere revertere Sulamitis revertere revertere ut intueamur te quid videbis in Sulamiten nisi choros castrorum
Ki dawo, ki dawo, ya Bashulammiya; ki dawo, ki dawo, don mu dube ki! Ƙaunatacce Don me kuke duban Bashulammiya sai ka ce rawar Mahanayim?

< Canticum Canticorum 6 >