< Romanos 8 >

1 nihil ergo nunc damnationis est his qui sunt in Christo Iesu qui non secundum carnem ambulant
Saboda haka babu kayarwa yanzu ga wadanda ke cikin Almasihu Yesu.
2 lex enim Spiritus vitae in Christo Iesu liberavit me a lege peccati et mortis
Domin ka'idar ruhun rai a cikin Almasihu Yesu ta maishe mu 'yanttatu daga ka'idar zunubi da mutuwa.
3 nam quod inpossibile erat legis in quo infirmabatur per carnem Deus Filium suum mittens in similitudinem carnis peccati et de peccato damnavit peccatum in carne
Saboda abin da shari'a bata iya aikatawa ba domin kasawa ta wurin jiki, Allah ya yi. Ya aiko da dansa a kamanin jiki mai zunubi domin ya zama hadaya domin zunubi, sai ya yi Allah wadai da zunubi a cikin jiki.
4 ut iustificatio legis impleretur in nobis qui non secundum carnem ambulamus sed secundum Spiritum
Ya yi haka domin bukatar shari'a ta sami cika a cikinmu, mu da muke tafe ba ta gwargwadon jiki ba, amma ta gwargwadon ruhaniya.
5 qui enim secundum carnem sunt quae carnis sunt sapiunt qui vero secundum Spiritum quae sunt Spiritus sentiunt
Wadanda ke rayuwa gwargwadon jiki sukan lura da al'amuran jiki, amma su da ke rayuwa a gwargwadon Ruhu sukan mai da hankali ga al'amuran Ruhu.
6 nam prudentia carnis mors prudentia autem Spiritus vita et pax
To kwallafa rai ga jiki mutuwa ce, amma kwallafa rai ga Ruhu rai ne da salama.
7 quoniam sapientia carnis inimicitia est in Deum legi enim Dei non subicitur nec enim potest
Haka yake domin kwallafa rai ga jiki gaba yake da Allah, gama baya biyyaya ga shari'ar Allah, balle ma ya iya.
8 qui autem in carne sunt Deo placere non possunt
Wadanda ke a jiki ba su iya faranta wa Allah zuciya.
9 vos autem in carne non estis sed in Spiritu si tamen Spiritus Dei habitat in vobis si quis autem Spiritum Christi non habet hic non est eius
Duk da haka, ba ku cikin jiki amma a cikin Ruhu, idan gaskiya ne, Ruhun Allah na rayuwa cikinku. Amma idan wani ba shi da Ruhun Almasihu, shi ba na sa bane.
10 si autem Christus in vobis est corpus quidem mortuum est propter peccatum spiritus vero vita propter iustificationem
In Almasihu na cikinka, jikin ka fa matacce ne ga zunubi, amma ruhu na rayuwa bisa ga adalci.
11 quod si Spiritus eius qui suscitavit Iesum a mortuis habitat in vobis qui suscitavit Iesum Christum a mortuis vivificabit et mortalia corpora vestra propter inhabitantem Spiritum eius in vobis
Idan Ruhun wanda ya tada Yesu daga matattu na raye a cikinku, to shi wanda ya tada Almasihu da ga matattu za ya bada rai ga jikinku masu matuwa ta wurin Ruhunsa, da ke rayuwa a cikin ku.
12 ergo fratres debitores sumus non carni ut secundum carnem vivamus
To, 'yan' uwa, muna da hakki amma ba bisa jiki ba, da za mu yi rayuwa bisa ga dabi'ar jiki.
13 si enim secundum carnem vixeritis moriemini si autem Spiritu facta carnis mortificatis vivetis
Gama idan kun yi rayuwa gwargwadon jiki, za ku mutu kenan, amma idan ta wurin Ruhu ku ka kashe ayyukan jiki, za ku rayu.
14 quicumque enim Spiritu Dei aguntur hii filii sunt Dei
Gama duk wadanda Ruhun Allah ke bishe su, su 'ya 'yan Allah ne.
15 non enim accepistis spiritum servitutis iterum in timore sed accepistis Spiritum adoptionis filiorum in quo clamamus Abba Pater
Gama ba ku karbi ruhun bauta da ke sa tsoro ba. Maimakon haka, kun karbi ruhun diyanci, ta wurinsa muke tadda murya muna kira, “Abba, Uba!”
16 ipse Spiritus testimonium reddit spiritui nostro quod sumus filii Dei
kansa na bada shaida tare da namu ruhun cewa mu 'ya'yan Allah ne.
17 si autem filii et heredes heredes quidem Dei coheredes autem Christi si tamen conpatimur ut et conglorificemur
Idan mu 'ya'ya ne, ai mu magada ne kenan, magadan Allah. Kuma mu magada ne tare da Almasihu, hakika idan mun sha wahala tare da shi za a kuma daukaka mu tare da shi.
18 existimo enim quod non sunt condignae passiones huius temporis ad futuram gloriam quae revelabitur in nobis
Gama na yi la'akari cewa wahalonin zamanin nan ba su isa a kwatanta su da daukakar da za'a bayyana mana ba.
19 nam expectatio creaturae revelationem filiorum Dei expectat
Saboda yadda halitta ke marmarin bayyanuwar 'ya'yan Allah.
20 vanitati enim creatura subiecta est non volens sed propter eum qui subiecit in spem
Gama an kaskantar da halitta ga banza, ba da nufin ta ba, amma na shi wanda ya kaskantar da ita. Ta na cikin tabbacin alkawarin.
21 quia et ipsa creatura liberabitur a servitute corruptionis in libertatem gloriae filiorum Dei
Cewa halitta kanta za ta kubuta daga bautar rubewa, kuma za a kawo ta zuwa ga 'yantarwa na yabon daukakar 'ya'yan Allah.
22 scimus enim quod omnis creatura ingemescit et parturit usque adhuc
Gama mun sani dukan halitta na nishi da zafin nakuda tare har ya zuwa yanzu.
23 non solum autem illa sed et nos ipsi primitias Spiritus habentes et ipsi intra nos gemimus adoptionem filiorum expectantes redemptionem corporis nostri
Ba haka kadai ba, amma ko mu kanmu, da ke nunar farko na Ruhu—mu kanmu muna nishi acikin mu, muna jiran diyancinmu, wato ceton jikinmu kenan.
24 spe enim salvi facti sumus spes autem quae videtur non est spes nam quod videt quis quid sperat
Gama ta wanan hakikancewa aka cece mu. Amma dai abin da muke da tabbacin zai faru ba mu gan shi ba tukuna, domin wanene wa ke begen tabbatacce abin da yake gani?
25 si autem quod non videmus speramus per patientiam expectamus
Amma idan muna da tabbacin abin da ba mu gani ba tukuna, to sai mu jjira shi da hakuri.
26 similiter autem et Spiritus adiuvat infirmitatem nostram nam quid oremus sicut oportet nescimus sed ipse Spiritus postulat pro nobis gemitibus inenarrabilibus
Hakanan, Ruhu kuma ke taimako a kasawarmu. Gama ba mu da san yadda zamu yi addu'a ba, amma Ruhu kansa na roko a madadinmu da nishe-nishen da ba'a iya ambatawa.
27 qui autem scrutatur corda scit quid desideret Spiritus quia secundum Deum postulat pro sanctis
Shi da ke bidar zuciya yana sane da tunanin Ruhu, domin yana roko a madadin masu badagaskiya ta wurin nufin Allah.
28 scimus autem quoniam diligentibus Deum omnia cooperantur in bonum his qui secundum propositum vocati sunt sancti
Mun san cewa ga wadanda ke kaunar Allah, yakan aikata dukan al'amura domin su zuwa ga alheri, ga duk wadanda aka kira bisa ga nufinsa. Dukan abubuwa sukan zama alheri.
29 nam quos praescivit et praedestinavit conformes fieri imaginis Filii eius ut sit ipse primogenitus in multis fratribus
Saboda wadanda ya sani tuntuni su ne ya kardara su zama da kamanin dansa, domin ya zama dan fari a cikin 'yan'uwa masu yawa.
30 quos autem praedestinavit hos et vocavit et quos vocavit hos et iustificavit quos autem iustificavit illos et glorificavit
Su da ya kaddara, ya kiraye su. Wadanda ya kira, su ya kubutar. Su da ya kubutar, sune kuma ya daukaka.
31 quid ergo dicemus ad haec si Deus pro nobis quis contra nos
Me zamu ce game da wadannan al'amura? Idan Allah na tare da mu, wake gaba da mu?
32 qui etiam Filio suo non pepercit sed pro nobis omnibus tradidit illum quomodo non etiam cum illo omnia nobis donabit
Shi da baya hana dansa ba, amma ya bada shi a madadinmu dukka, me zai hana shi bamu dukkan abubuwa a yalwace tare da shi?
33 quis accusabit adversus electos Dei Deus qui iustificat
Wa zaya kawo wata tuhuma ga zababbu na Allah? Allah ne ke “yantarwa.
34 quis est qui condemnet Christus Iesus qui mortuus est immo qui resurrexit qui et est ad dexteram Dei qui etiam interpellat pro nobis
Wanene ke hukumtawa? Almasihu ne da ya mutu sabili da mu har ma fiye da haka, shi wanda kuma aka tasar. Yana mulki tare da Allah a wuri mai daukaka, shi ne kuma ya ke roko sabili da mu.
35 quis nos separabit a caritate Christi tribulatio an angustia an persecutio an fames an nuditas an periculum an gladius
Wa za ya raba mu da kaunar Allah? Kunci, ko bacin rai, ko tsanani, ko yunwa, ko tsiraci, ko hadari, ko takobi?
36 sicut scriptum est quia propter te mortificamur tota die aestimati sumus ut oves occisionis
Kamar yadda aka rubuta, “Saboda kai ake kisanmu dukkan yini. An mai da mu kamar tumaki yanka.”
37 sed in his omnibus superamus propter eum qui dilexit nos
A dukan al'amuran nan mun fi karfi a ce da mu masu nasara ta wurin shi da ke kaunar mu.
38 certus sum enim quia neque mors neque vita neque angeli neque principatus neque instantia neque futura neque fortitudines
Gama na tabata cewa ko mutuwa, ko rai, ko mala'iku, ko mulkoki, ko al'amuran yanzu, ko al'amura masu zuwa, ko iko,
39 neque altitudo neque profundum neque creatura alia poterit nos separare a caritate Dei quae est in Christo Iesu Domino nostro
ko tsawo, ko zurfi, kai ko wace irin halitta, ba su isa su raba mu da kaunar Allah, da ke a cikin Almasihu Yesu Ubangijin mu ba.

< Romanos 8 >