< Psalmorum 46 >
1 in finem pro filiis Core pro arcanis psalmus Deus noster refugium et virtus adiutor in tribulationibus quae invenerunt nos nimis
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta’Ya’yan Kora maza. Bisa ga alamot Waƙa ce. Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu, kullum yana a shirye yă taimaka a lokacin wahala.
2 propterea non timebimus dum turbabitur terra et transferentur montes in cor maris
Saboda haka ba za mu ji tsoro ba, ko da ƙasa ta girgiza duwatsu kuma suka fāɗi cikin zurfin teku,
3 sonaverunt et turbatae sunt aquae eorum conturbati sunt montes in fortitudine eius diapsalma
ko da ruwansa suna ruri suna kumfa duwatsu kuma suna girgiza da tumbatsansu. (Sela)
4 fluminis impetus laetificat civitatem Dei sanctificavit tabernaculum suum Altissimus
Akwai kogi mai rafuffukan da suke sa birnin Allah murna, tsattsarkan wuri inda Mafi Ɗaukaka ke zama.
5 Deus in medio eius non commovebitur adiuvabit eam Deus mane diluculo
Allah yana cikinta, ba za tă fāɗi ba; Allah zai taimake ta da safe.
6 conturbatae sunt gentes inclinata sunt regna dedit vocem suam mota est terra
Al’ummai suna hayaniya, mulkoki sun fāɗi; ya ɗaga muryarsa, duniya ta narke.
7 Dominus virtutum nobiscum susceptor noster Deus Iacob diapsalma
Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu; Allah na Yaƙub ne kagararmu. (Sela)
8 venite et videte opera Domini quae posuit prodigia super terram
Zo ku ga ayyukan Ubangiji, kangon da ya kawo a kan duniya.
9 auferens bella usque ad finem terrae arcum conteret et confringet arma et scuta conburet in igne
Ya sa yaƙoƙi suka yi tsit ko’ina a duniya. Ya kakkarya bakkuna ya kuma ragargaza māsu, ya ƙone garkuwoyi da wuta.
10 vacate et videte quoniam ego sum Deus exaltabor in gentibus exaltabor in terra
“Ku natsu ku kuma san cewa ni ne Allah; za a ɗaukaka ni a cikin al’ummai, za a ɗaukaka ni cikin duniya.”
11 Dominus virtutum nobiscum susceptor noster Deus Iacob
Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu; Allah na Yaƙub ne kagararmu. (Sela)