< Micha Propheta 7 >

1 vae mihi quia factus sum sicut qui colligit in autumno racemos vindemiae non est botrus ad comedendum praecoquas ficus desideravit anima mea
Tawa ta ƙare! Ina kama da wanda yake tattara’ya’yan itatuwa a lokacin kalar’ya’yan inabi; babu sauran nonon inabin da za a tsinka a ci, babu kuma’ya’yan ɓaure na farko-farkon da raina yake marmari.
2 periit sanctus de terra et rectus in hominibus non est omnes in sanguine insidiantur vir fratrem suum venatur ad mortem
An kawar da masu tsoron Allah daga ƙasar; babu sauran mai adalcin da ya rage. Dukan mutane suna kwanto don su zub da jini; kowa yana farautar ɗan’uwansa da tarko.
3 malum manuum suarum dicunt bonum princeps postulat et iudex in reddendo est et magnus locutus est desiderium animae suae et conturbaverunt eam
Dukan hannuwansu sun gwaninta wajen yin mugunta; shugabanni suna nema a ba su kyautai, alƙalai suna nema a ba su cin hanci, masu iko suna faɗar son zuciyarsu, duk suna ƙulla makirci tare.
4 qui optimus in eis est quasi paliurus et qui rectus quasi spina de sepe dies speculationis tuae visitatio tua venit nunc erit vastitas eorum
Mafi kyau a cikinsu yana kama da ƙaya, mafi gaskiyarsu ya fi shingen ƙaya muni. Ranar da Allah zai ziyarce ku ta zo, ranar da masu gadinku za su hura ƙaho. Yanzu ne lokacin ruɗewarku.
5 nolite credere amico et nolite confidere in duce ab ea quae dormit in sinu tuo custodi claustra oris tui
Kada ka yarda da maƙwabci; kada ka sa begenka ga abokai. Ko ma wadda take kwance a ƙirjinka, ka yi hankali da kalmominka.
6 quia filius contumeliam facit patri filia consurgit adversus matrem suam nurus contra socrum suam inimici hominis domestici eius
Gama ɗa yakan ce wannan ba mahaifinsa ba ne, diya kuma takan tayar wa mahaifiyarta, matar ɗa takan yi gāba da uwar mijinta, abokan gāban mutum su ne iyalin cikin gidansa.
7 ego autem ad Dominum aspiciam expectabo Deum salvatorem meum audiet me Deus meus
Amma game da ni, zan sa bege ga Ubangiji, ina sauraron Allah Mai Cetona; Allahna kuwa zai ji ni.
8 ne laeteris inimica mea super me quia cecidi consurgam cum sedero in tenebris Dominus lux mea est
Kada ku yi farin ciki, ku maƙiyana! Ko da yake na fāɗi, zan tashi. Ko da yake na zauna a cikin duhu, Ubangiji zai zama haskena.
9 iram Domini portabo quoniam peccavi ei donec iudicet causam meam et faciat iudicium meum educet me in lucem videbo in iustitiam eius
Domin na yi masa zunubi, zan fuskanci fushin Ubangiji, har sai ya dubi batuna ya kuma tabbatar da’yancina. Zai kawo ni zuwa wurin haske; zan ga adalcinsa.
10 et aspiciet inimica mea et operietur confusione quae dicit ad me ubi est Dominus Deus tuus oculi mei videbunt in eam nunc erit in conculcationem ut lutum platearum
Sa’an nan maƙiyina zai gani yă kuma sha kunya, shi da yake ce da ni “Ina Ubangiji Allahnka?” Zai gani, yă kuma ji kunya. Ko yanzu ma za a tattake shi kamar taɓo a tituna.
11 dies ut aedificentur maceriae tuae in die illa longe fiet lex
Ranar gina katangarka tana zuwa, a ranar za a fadada iyakokinka.
12 in die illa et usque ad te veniet Assur et usque ad civitates munitas et a civitatibus munitis usque ad flumen et ad mare de mari et ad montem de monte
A wannan rana mutane za su zo gare ka daga Assuriya da kuma biranen Masar, daga Masar ma har zuwa Yuferites daga teku zuwa teku, kuma daga dutse zuwa dutse.
13 et erit terra in desolationem propter habitatores suos et propter fructum cogitationum eorum
Duniya za tă zama kufai saboda mazaunanta, saboda ayyukansu.
14 pasce populum tuum in virga tua gregem hereditatis tuae habitantes solos in saltu in medio Carmeli pascentur Basan et Galaad iuxta dies antiquos
Ka yi kiwon mutanenka da sandarka, garken gādonka, wanda yake zaune shi kaɗai a kurmi, a ƙasa mai kyau ta kiwo, bari su yi kiwo a Bashan da Gileyad kamar a kwanakin dā.
15 secundum dies egressionis tuae de terra Aegypti ostendam ei mirabilia
“Kamar a kwanakin da kuka fito daga Masar, zan nuna musu al’ajabaina.”
16 videbunt gentes et confundentur super omni fortitudine sua ponent manus super os aures eorum surdae erunt
Al’ummai za su gani su kuma ji kunya, za a kuma ƙwace musu dukan ikonsu. Za su kama bakinsu kunnuwansu kuma za su zama kurame.
17 lingent pulverem sicut serpens velut reptilia terrae proturbabuntur de aedibus suis Dominum Deum nostrum desiderabunt et timebunt te
Za su lashi ƙura kamar maciji, kamar dabbobi masu rarrafe a ƙasa. Za su fito daga maɓuyarsu da rawan jiki, za su juya cikin tsoro ga Ubangiji Allahnmu su kuma ji tsoronku.
18 quis Deus similis tui qui aufers iniquitatem et transis peccatum reliquiarum hereditatis tuae non inmittet ultra furorem suum quoniam volens misericordiam est
Wane ne Allah kamar ka, wanda yake yafe zunubi yă kuma gafarta laifofin mutanensa da suka ragu? Ba ka zama mai fushi har abada amma kana marmari ka nuna jinƙai.
19 revertetur et miserebitur nostri deponet iniquitates nostras et proiciet in profundum maris omnia peccata nostra
Za ka sāke jin tausayinmu; za ka tattake zunubanmu a ƙarƙashin sawunka ka kuma tura dukan kurakuranmu zuwa cikin zurfafan teku.
20 dabis veritatem Iacob misericordiam Abraham quae iurasti patribus nostris a diebus antiquis
Za ka yi wa Yaƙub aminci, ka kuma nuna jinƙai ga Ibrahim, kamar yadda ka yi alkawari da rantsuwa ga kakanninmu tun a kwanankin dā.

< Micha Propheta 7 >