< Mattheum 8 >

1 cum autem descendisset de monte secutae sunt eum turbae multae
Da ya sauko daga dutsen, sai taron mutane mai yawan gaske suka bi shi.
2 et ecce leprosus veniens adorabat eum dicens Domine si vis potes me mundare
Wani mutum mai kuturta ya zo ya durƙusa a gabansa ya ce, “Ubangiji, in kana so, kana iya tsabtacce ni.”
3 et extendens manum tetigit eum Iesus dicens volo mundare et confestim mundata est lepra eius
Yesu ya miƙa hannunsa ya taɓa mutumin. Ya ce, “Ina so, ka tsabtacce!” Nan da nan aka warkar da shi daga kuturtarsa.
4 et ait illi Iesus vide nemini dixeris sed vade ostende te sacerdoti et offer munus quod praecepit Moses in testimonium illis
Sai Yesu ya ce masa, “Ka lura kada ka gaya wa kowa. Sai dai ka tafi, ka nuna kanka ga firist ka kuma yi bayarwar da Musa ya umarta, a matsayin shaida gare su.”
5 cum autem introisset Capharnaum accessit ad eum centurio rogans eum
Da Yesu ya shiga Kafarnahum, sai wani jarumi ya zo wurinsa, yana neman taimako.
6 et dicens Domine puer meus iacet in domo paralyticus et male torquetur
Ya ce, “Ubangiji, bawana yana kwance a gida shanyayye, yana kuma shan azaba ƙwarai.”
7 et ait illi Iesus ego veniam et curabo eum
Yesu ya ce masa, “Zan je in warkar da shi.”
8 et respondens centurio ait Domine non sum dignus ut intres sub tectum meum sed tantum dic verbo et sanabitur puer meus
Jarumin ya amsa, “Ubangiji, ban cancanci in sa ka zo gidana ba, ka dai yi magana kawai, bawana zai warke.
9 nam et ego homo sum sub potestate habens sub me milites et dico huic vade et vadit et alio veni et venit et servo meo fac hoc et facit
Gama ni kaina mutum ne a ƙarƙashin iko, da kuma sojoji a ƙarƙashina. Nakan ce wa wannan, ‘Je ka,’ sai yă tafi; wancan kuma, ‘Zo nan,’ sai yă zo. Nakan ce wa bawana, ‘Yi wannan,’ sai kuwa yă yi.”
10 audiens autem Iesus miratus est et sequentibus se dixit amen dico vobis non inveni tantam fidem in Israhel
Da Yesu ya ji wannan, sai ya yi mamaki ya kuma ce wa waɗanda suke binsa, “Gaskiya nake gaya muku, ban taɓa samun wani a Isra’ila da bangaskiya mai girma haka ba.
11 dico autem vobis quod multi ab oriente et occidente venient et recumbent cum Abraham et Isaac et Iacob in regno caelorum
Ina kuma gaya muku da yawa za su zo daga gabas da kuma yamma, su ɗauki wuraren zamansu a biki tare da Ibrahim, Ishaku, da Yaƙub a cikin mulkin sama.
12 filii autem regni eicientur in tenebras exteriores ibi erit fletus et stridor dentium
Amma za a jefar da’ya’yan mulki waje, zuwa cikin baƙin duhu, inda za a yi kuka da cizon haƙora.”
13 et dixit Iesus centurioni vade et sicut credidisti fiat tibi et sanatus est puer in hora illa
Sa’an nan Yesu ya ce wa jarumin, “Je ka! Za a yi bisa ga bangaskiyarka.” A daidai wannan lokaci bawansa kuwa ya warke.
14 et cum venisset Iesus in domum Petri vidit socrum eius iacentem et febricitantem
Da Yesu ya zo cikin gidan Bitrus, sai ya ga surukar Bitrus tana kwance a gado tana da zazzaɓi.
15 et tetigit manum eius et dimisit eam febris et surrexit et ministrabat eis
Ya taɓa hannunta sai zazzaɓin ya sake ta, ta kuwa tashi ta fara yin masa hidima.
16 vespere autem facto obtulerunt ei multos daemonia habentes et eiciebat spiritus verbo et omnes male habentes curavit
Da yamma ta yi, aka kawo masa masu aljanu da yawa, ya kuwa fitar da ruhohin ta wurin magana, ya kuma warkar da dukan marasa lafiya.
17 ut adimpleretur quod dictum est per Esaiam prophetam dicentem ipse infirmitates nostras accepit et aegrotationes portavit
Wannan ya faru ne domin a cika abin da aka faɗa ta bakin annabi Ishaya cewa, “Ya ɗebi rashin lafiyarmu, ya kuma ɗauki cututtukanmu.”
18 videns autem Iesus turbas multas circum se iussit ire trans fretum
Da Yesu ya ga taron mutane kewaye da shi, sai ya ba da umarni a ƙetare zuwa ɗayan hayin tafkin.
19 et accedens unus scriba ait illi magister sequar te quocumque ieris
Sai wani malamin dokoki ya zo wurinsa ya ce, “Malam, zan bi ka duk inda za ka.”
20 et dicit ei Iesus vulpes foveas habent et volucres caeli tabernacula Filius autem hominis non habet ubi caput reclinet
Sai Yesu ya amsa ya ce, “Yanyawa suna da ramummuka, tsuntsayen sararin sama suna da sheƙuna, amma Ɗan Mutum ba shi da wurin da zai sa kansa.”
21 alius autem de discipulis eius ait illi Domine permitte me primum ire et sepelire patrem meum
Sai wani almajiri ya ce masa, “Ubangiji, da farko bari in je in binne mahaifina.”
22 Iesus autem ait illi sequere me et dimitte mortuos sepelire mortuos suos
Amma Yesu ya ce masa, “Ka bi ni, ka bar matattu su binne matattunsu.”
23 et ascendente eo in navicula secuti sunt eum discipuli eius
Sai ya shiga jirgin ruwa, almajiransa kuwa suka bi shi.
24 et ecce motus magnus factus est in mari ita ut navicula operiretur fluctibus ipse vero dormiebat
Ba zato ba tsammani, sai wani babban hadari ya taso a tafkin, har raƙuman ruwan suka sha kan jirgin. Amma Yesu yana barci.
25 et accesserunt et suscitaverunt eum dicentes Domine salva nos perimus
Almajiran suka je suka tashe shi, suna cewa, “Ubangiji, ka cece mu! Za mu nutse!”
26 et dicit eis quid timidi estis modicae fidei tunc surgens imperavit ventis et mari et facta est tranquillitas magna
Ya amsa ya ce, “Ku masu ƙarancin bangaskiya, me ya sa kuke tsoro haka?” Sa’an nan ya tashi ya tsawata wa iskar da kuma raƙuman ruwan, sai wuri ya yi tsit gaba ɗaya.
27 porro homines mirati sunt dicentes qualis est hic quia et venti et mare oboediunt ei
Mutanen suka yi mamaki suka ce, “Wane irin mutum ne wannan? Har iska da raƙuman ruwa suna masa biyayya!”
28 et cum venisset trans fretum in regionem Gerasenorum occurrerunt ei duo habentes daemonia de monumentis exeuntes saevi nimis ita ut nemo posset transire per viam illam
Da ya isa ɗayan gefen a yankin Gadarenawa (ko kuwa Gerasenawa), sai ga mutum biyu masu aljanu suna fitowa daga kaburbura suka tarye shi. Su abin tsoro ne ƙwarai, har ba mai iya bin wannan hanya.
29 et ecce clamaverunt dicentes quid nobis et tibi Fili Dei venisti huc ante tempus torquere nos
Suka yi ihu suka ce, “Me ya haɗa ka da mu, Ɗan Allah?” Ka zo ne nan don ka ji mana kafin lokaci yă yi?
30 erat autem non longe ab illis grex porcorum multorum pascens
Nesa kaɗan da su kuwa akwai babban garken aladu da yake kiwo.
31 daemones autem rogabant eum dicentes si eicis nos mitte nos in gregem porcorum
Aljanun suka roƙi Yesu suka ce, “In ka fitar da mu, tura mu cikin garken aladun nan.”
32 et ait illis ite at illi exeuntes abierunt in porcos et ecce impetu abiit totus grex per praeceps in mare et mortui sunt in aquis
Ya ce musu, “Ku tafi!” Sai suka fita suka shiga cikin aladun, dukan garken kuwa ya gangara a guje daga kan tudun zuwa cikin tafkin aladun kuma suka mutu a cikin ruwa.
33 pastores autem fugerunt et venientes in civitatem nuntiaverunt omnia et de his qui daemonia habuerant
Masu kiwon aladun suka ruga, suka je cikin gari suka ba da labarin dukan wannan, haɗe da abin da ya faru da mutanen nan masu aljanu.
34 et ecce tota civitas exiit obviam Iesu et viso eo rogabant ut transiret a finibus eorum
Sai dukan garin suka fito don su taryi Yesu. Da suka kuwa gan shi, sai suka roƙe shi yă bar musu yanki.

< Mattheum 8 >