< Mattheum 25 >

1 tunc simile erit regnum caelorum decem virginibus quae accipientes lampadas suas exierunt obviam sponso et sponsae
Sa'annan mulkin sama zai zama kamar budurwai goma da suka dauki fitilunsu domin su taryi ango.
2 quinque autem ex eis erant fatuae et quinque prudentes
Biyar daga cikin su masu hikima ne biyar kuma wawaye.
3 sed quinque fatuae acceptis lampadibus non sumpserunt oleum secum
Sa'adda wawayen budurwai suka dauki fitilunsu, ba su dauki karin mai ba.
4 prudentes vero acceperunt oleum in vasis suis cum lampadibus
Amma budurwai masu hikimar suka dauki gorar mai tare da fitilunsu.
5 moram autem faciente sponso dormitaverunt omnes et dormierunt
To da angon ya makara, dukkan su sai suka fara gyangyadi sai barci ya dauke su.
6 media autem nocte clamor factus est ecce sponsus venit exite obviam ei
Amma da tsakkar dare sai aka yi shela, 'Ga ango ya iso! Ku fito taryensa.
7 tunc surrexerunt omnes virgines illae et ornaverunt lampades suas
Sai dukka budurwan nan suka tashi suka gyaggyara fitilunsu.
8 fatuae autem sapientibus dixerunt date nobis de oleo vestro quia lampades nostrae extinguntur
Wawayen su ka ce da masu hikimar, 'Ku sammana kadan daga manku gama fitilunmu su na mutuwa.'
9 responderunt prudentes dicentes ne forte non sufficiat nobis et vobis ite potius ad vendentes et emite vobis
“Amma masu hikimar suka ce 'Tun da man ba zai ishe mu tare da ku ba, sai ku je gun ma su sayarwa ku sayo wa kanku.
10 dum autem irent emere venit sponsus et quae paratae erant intraverunt cum eo ad nuptias et clausa est ianua
Sa'adda suka tafi sayan man, sai angon ya shigo, kuma wadanda suke a shirye su ka shiga tare da shi bukin auren, sai aka rufe kofar.
11 novissime veniunt et reliquae virgines dicentes domine domine aperi nobis
Bayan dan lokaci kadan sauran budurwan suka dawo suna cewa, 'Mai gida, mai gida, bude mana kofar.'
12 at ille respondens ait amen dico vobis nescio vos
Amma ya amsa ya ce, 'A gaskiya ina gaya maku, ni ban san ku ba.'
13 vigilate itaque quia nescitis diem neque horam
Don haka sai ku lura, don baku san rana ko sa'a ba.
14 sicut enim homo proficiscens vocavit servos suos et tradidit illis bona sua
Domin yana kama da wani mutum da zai tafi wata kasa. Ya kira barorinsa ya ba su dukiyar sa.
15 et uni dedit quinque talenta alii autem duo alii vero unum unicuique secundum propriam virtutem et profectus est statim
Ga wani ya ba shi talanti biyar, ga wani ya ba shi biyu, ga wani kuma ya ba shi talanti daya. kowa an bashi gwargwadon iyawarsa, sai wannan mutum ya yi tafiyar sa
16 abiit autem qui quinque talenta acceperat et operatus est in eis et lucratus est alia quinque
nan da nan sai wanda ya karbi talanti biyar ya sa nasa a jari, ya sami ribar wasu talanti biyar.
17 similiter qui duo acceperat lucratus est alia duo
Haka ma wanda ya karbi talanti biyu ya sami ribar wasu biyu.
18 qui autem unum acceperat abiens fodit in terra et abscondit pecuniam domini sui
Amma bawan da ya karbi talanti dayan ya yi tafiyar sa, ya haka rami, ya binne kudin mai gidansa.
19 post multum vero temporis venit dominus servorum illorum et posuit rationem cum eis
To bayan tsawon lokaci sai ubangidan barorin nan ya dawo, domin yayi lissafin kudinsu.
20 et accedens qui quinque talenta acceperat obtulit alia quinque talenta dicens domine quinque talenta mihi tradidisti ecce alia quinque superlucratus sum
Bawan da ya karbi talanti biyar, ya kawo nasa da ribar wasu biyar. Yace, 'Maigida, ka bani talanti biyar, gashi na samo ribar karin talanti biyar.'
21 ait illi dominus eius euge bone serve et fidelis quia super pauca fuisti fidelis super multa te constituam intra in gaudium domini tui
Maigidansa yace masa, 'Madalla, bawa na gari mai aminci! Ka yi aminci akan abu kadan. Zan sa ka akan abubuwa masu yawa. Ka shiga cikin farincikin maigidanka.'
22 accessit autem et qui duo talenta acceperat et ait domine duo talenta tradidisti mihi ecce alia duo lucratus sum
Bawan da ya karbi talanti biyun, ya zo yace, 'Maigida, ka ba ni talanti biyu. Gashi kuwa na sami karin ribar wasu biyun.'
23 ait illi dominus eius euge serve bone et fidelis quia super pauca fuisti fidelis supra multa te constituam intra in gaudium domini tui
Ubangidansa yace masa, 'Madalla, kai bawa na gari mai aminci! Ka yi aminci akan abubuwa kadan. Zan saka akan abubuwa masu yawa. Ka shiga cikin farincikin maigidanka.'
24 accedens autem et qui unum talentum acceperat ait domine scio quia homo durus es metis ubi non seminasti et congregas ubi non sparsisti
Sai bawan da ya karbi talanti daya ya zo yace, 'Maigida, na san kai mai tsanani ne. Kana girbi inda baka yi shuka ba, kuma kana tattarawa inda ba ka watsa ba.
25 et timens abii et abscondi talentum tuum in terra ecce habes quod tuum est
Na ji tsoro, don haka sai na je na boye talantinka a rami. Duba, ga abinda yake naka.'
26 respondens autem dominus eius dixit ei serve male et piger sciebas quia meto ubi non semino et congrego ubi non sparsi
Amma ubangidansa ya amsa yace, kai mugu malalacin bawa, ka san cewa ni mai girbi ne inda ban shuka ba kuma ina tattarawa inda ban zuba ba.
27 oportuit ergo te mittere pecuniam meam nummulariis et veniens ego recepissem utique quod meum est cum usura
To da ba sai ka kai kudina a banki ba, da bayan na dawo da sai in karbi abina da riba.
28 tollite itaque ab eo talentum et date ei qui habet decem talenta
Saboda haka ku kwace talantin daga gare shi ku baiwa mai talanti goman nan.
29 omni enim habenti dabitur et abundabit ei autem qui non habet et quod videtur habere auferetur ab eo
Gama ga wanda yake da shi za'a kara masa har ma a yalwace za'a kara bashi. Amma ga wanda bashi da komai abinda ke nasa ma za'a kwace.
30 et inutilem servum eicite in tenebras exteriores illic erit fletus et stridor dentium
Ku jefa wannan mugun bawan marar amfani, cikin duhu mai zurfi, inda ake kuka da cizon hakora.'
31 cum autem venerit Filius hominis in maiestate sua et omnes angeli cum eo tunc sedebit super sedem maiestatis suae
Sa'adda Dan mutum zai zo cikin daukakarsa da dukan Mala'iku tare da shi, sa'annan zai zauna kursiyinsa na daukaka.
32 et congregabuntur ante eum omnes gentes et separabit eos ab invicem sicut pastor segregat oves ab hedis
A gabansa za'a tattara dukkan al'ummai, zai rarraba mutanen daya'daya, kamar yadda makiyayi yake rarraba tumaki daga awaki.
33 et statuet oves quidem a dextris suis hedos autem a sinistris
Zai sa tumakin a hannunsa na dama, amma awakin a hannunsa na hagu.
34 tunc dicet rex his qui a dextris eius erunt venite benedicti Patris mei possidete paratum vobis regnum a constitutione mundi
Sa'annan sarkin zai ce wa na hannun damarsa, 'Ku zo ku da Ubana ya albarkata, ku gaji mulkin da aka shirya maku kafin a kafa duniya.
35 esurivi enim et dedistis mihi manducare sitivi et dedistis mihi bibere hospes eram et collexistis me
Gama na ji yunwa kuka bani abinci; Na ji kishi kuka bani ruwa; Na yi bakunci kun bani masauki;
36 nudus et operuistis me infirmus et visitastis me in carcere eram et venistis ad me
Na yi huntanci kuka tufasar dani; Na yi ciwo kuka kula dani; Ina kurkuku kuka ziyarceni.'
37 tunc respondebunt ei iusti dicentes Domine quando te vidimus esurientem et pavimus sitientem et dedimus tibi potum
Sa'annan masu adalcin za su amsa su ce, 'Ubangiji, yaushe muka ganka kana jin yunwa muka baka abinci? Ko kana jin kishi muka baka ruwan sha?
38 quando autem te vidimus hospitem et colleximus te aut nudum et cooperuimus
Kuma yaushe muka ganka kana bakunci har muka baka masauki? Ko kuma kana huntanci da muka tufatar da kai?
39 aut quando te vidimus infirmum aut in carcere et venimus ad te
Yaushe kuma muka ganka kana ciwo ko a kurkuku har muka ziyarce ka?'
40 et respondens rex dicet illis amen dico vobis quamdiu fecistis uni de his fratribus meis minimis mihi fecistis
Sa'annan Sarkin zai amsa masu yace, 'Hakika Ina gaya maku, duk abinda kuka yi wa daya mafi kakanta daga cikin 'yan'uwana a nan ni kuka yi wa.'
41 tunc dicet et his qui a sinistris erunt discedite a me maledicti in ignem aeternum qui paratus est diabolo et angelis eius (aiōnios g166)
Sa'annan zai cewa wadanda suke hannunsa na hagu, 'Ku rabu da ni, ku la'anannu, ku tafi cikin wutar jahannama da aka shirya wa Shaidan da aljannunsa, (aiōnios g166, questioned)
42 esurivi enim et non dedistis mihi manducare sitivi et non dedistis mihi potum
domin ina jin yunwa baku bani abinci ba; ina jin kishi ba ku bani ruwa ba;
43 hospes eram et non collexistis me nudus et non operuistis me infirmus et in carcere et non visitastis me
Ina bakunci amma baku bani masauki ba; ina huntanci, baku tufasar da ni ba; ina ciwo kuma ina kurkuku, baku kula da ni ba.'
44 tunc respondebunt et ipsi dicentes Domine quando te vidimus esurientem aut sitientem aut hospitem aut nudum aut infirmum vel in carcere et non ministravimus tibi
Sa'annan suma zasu amsa su ce, 'Ubangiji, yaushe muka ganka kana jin yunwa, ko kishin ruwa, ko kana bakunci, ko kana huntanci, ko ciwo, kuma a kurkuku, da bamu yi maka hidima ba?'
45 tunc respondebit illis dicens amen dico vobis quamdiu non fecistis uni de minoribus his nec mihi fecistis
Sa'annan zai amsa ya ce masu, 'Ina gaya maku hakika abin da baku iya yiwa mafi karanta daga cikin wadannan ba, ba ku yi mani ba.'
46 et ibunt hii in supplicium aeternum iusti autem in vitam aeternam (aiōnios g166)
Wadannan kuwa zasu tafi cikin madawwamiyar azaba amma adalai zuwa rai madawwami.” (aiōnios g166)

< Mattheum 25 >