< Mattheum 23 >
1 tunc Iesus locutus est ad turbas et discipulos suos
Sai Yesu yayi wa taron da alamajiransa magana.
2 dicens super cathedram Mosi sederunt scribae et Pharisaei
Ya ce, “Marubuta da Farisawa suna zaune a mazaunin Musa.
3 omnia ergo quaecumque dixerint vobis servate et facite secundum opera vero eorum nolite facere dicunt enim et non faciunt
Don haka, duk abinda suka umarceku kuyi, kuyi wadannan abubuwa ku kuma kiyaye su. Amma kada kuyi koyi da ayyukansu, gama suna fadar abubuwa amma kuma ba su aikata su.
4 alligant autem onera gravia et inportabilia et inponunt in umeros hominum digito autem suo nolunt ea movere
I, sukan daura kaya masu nauyi, masu wuyar dauka, daga nan su dauka su jibga wa mutane a kafada. Amma su kan su baza su mika danyatsa ba su dauka.
5 omnia vero opera sua faciunt ut videantur ab hominibus dilatant enim phylacteria sua et magnificant fimbrias
Duk ayyukan su suna yi ne don mutane su gani, suna dinka aljihunan nassinsu da fadi, suna fadada iyakokin rigunansu.
6 amant autem primos recubitus in cenis et primas cathedras in synagogis
Su na son mafifitan wuraren zama a gidan biki, da mafifitan wuraren zama a majami'u,
7 et salutationes in foro et vocari ab hominibus rabbi
da kuma gaisuwar musamman a wuraren kasuwanci, a kuma rika ce da su 'mallam.'
8 vos autem nolite vocari rabbi unus enim est magister vester omnes autem vos fratres estis
Amma ba sai an kira ku 'mallam, ba' domin malami daya kuke da shi, ku duka kuwa 'yan'uwan juna ne.
9 et patrem nolite vocare vobis super terram unus enim est Pater vester qui in caelis est
Kada ku kira kowa 'Ubanku' a duniya, domin Uba daya ne ku ke da shi, kuma yana sama.
10 nec vocemini magistri quia magister vester unus est Christus
Kada kuma a kira ku malamai, saboda malamin ku daya ne, shi ne Almasihu.
11 qui maior est vestrum erit minister vester
Amma wanda yake babba a cikin ku zaya zama bawanku.
12 qui autem se exaltaverit humiliabitur et qui se humiliaverit exaltabitur
Duk wanda ya daukaka kansa za a kaskantar dashi. Duk wanda ya kaskantar da kansa kuma za a daukaka shi.
13 vae autem vobis scribae et Pharisaei hypocritae quia clauditis regnum caelorum ante homines vos enim non intratis nec introeuntes sinitis intrare
Amma kaiton ku marubuta da Farisawa, munafukai! Kun toshewa mutane kofar mulkin sama. Baku shiga ba, kuma ba ku bar wadanda suke so su sami shiga ba.
kaiton ku marubuta da Farisawa, domin kuna hallaka gwauraya -
15 vae vobis scribae et Pharisaei hypocritae quia circuitis mare et aridam ut faciatis unum proselytum et cum fuerit factus facitis eum filium gehennae duplo quam vos (Geenna )
Kaiton ku marubuta da Farisawa, munafukai! Kuna tafiya ketaren tekuna da kasashe domin samun almajiri daya tak, in kwa kun samu kukan mai da shi biyunku danwuta. (Geenna )
16 vae vobis duces caeci qui dicitis quicumque iuraverit per templum nihil est qui autem iuraverit in aurum templi debet
Kaiton ku, makafin jagora, kuda kuke cewa, Kowa ya rantse da Haikali, ba komai. Amma duk wanda ya rantse da zinariyar Haikalin, rantsuwarsa ta daure shi.'
17 stulti et caeci quid enim maius est aurum an templum quod sanctificat aurum
Ku wawayen makafi! wanene yafi girma, zinariyar ko kuwa Haikalin da yake tsarkake zinariyar?
18 et quicumque iuraverit in altari nihil est quicumque autem iuraverit in dono quod est super illud debet
Kuma, 'Kowa ya rantse da bagadi, ba komai bane. Amma duk wanda ya rantse da baikon da aka dora a kai, sai rantsuwarsa ta kama shi.'
19 caeci quid enim maius est donum an altare quod sanctificat donum
Ku makafi! Wanene yafi girma, baikon ko kuwa bagadin da yake kebe baikon ga Allah?
20 qui ergo iurat in altare iurat in eo et in omnibus quae super illud sunt
Saboda haka, duk wanda ya rantse da bagadi, ya rantse da shi da duk abinda ke kansa.
21 et qui iuraverit in templo iurat in illo et in eo qui inhabitat in ipso
Kuma duk wanda ya rantse da Haikali ya rantse dashi da kuma wanda yake cikin sa.
22 et qui iurat in caelo iurat in throno Dei et in eo qui sedet super eum
Kuma duk wanda ya rantse da sama, ya rantse da kursiyin Allah da kuma wanda yake zaune akai.
23 vae vobis scribae et Pharisaei hypocritae quia decimatis mentam et anethum et cyminum et reliquistis quae graviora sunt legis iudicium et misericordiam et fidem haec oportuit facere et illa non omittere
Kaiton ku Farisawa da marubuta, munafukai! Kukan fitar da zakkar doddoya, da karkashi, da lamsur, amma kun yar da al'amuran attaura mafi nauyi-, wato, hukunci, da jinkai da bangaskiya. Wadannan ne ya kamata kuyi, ba tare da kunyi watsi da sauran ba.
24 duces caeci excolantes culicem camelum autem gluttientes
Makafin jagora, ku kan burtsar da kwaro dan mitsil, amma kukan hadiye rakumi!
25 vae vobis scribae et Pharisaei hypocritae quia mundatis quod de foris est calicis et parapsidis intus autem pleni sunt rapina et inmunditia
Kaiton ku marubuta da Farisawa, munafukai! kuna wanke bayan moda da kwano, amma aciki cike suke da zalunci da keta.
26 Pharisaee caece munda prius quod intus est calicis et parapsidis ut fiat et id quod de foris est mundum
Kai makahon Bafarise! Sai ka fara tsarkake cikin modar da kwanon domin bayansu ma su tsarkaka.
27 vae vobis scribae et Pharisaei hypocritae quia similes estis sepulchris dealbatis quae a foris parent hominibus speciosa intus vero plena sunt ossibus mortuorum et omni spurcitia
Kaiton ku marubuta da Farisawa, munafukai! Kamar kaburburan da aka shafa wa farar kasa kuke, masu kyaun gani daga waje, daga ciki kuwa sai kasusuwan matattu da kazanta iri iri.
28 sic et vos a foris quidem paretis hominibus iusti intus autem pleni estis hypocrisi et iniquitate
Haka nan kuke a idanun mutane ku adalai ne, amma a ciki sai munafunci da mugun aiki.
29 vae vobis scribae et Pharisaei hypocritae quia aedificatis sepulchra prophetarum et ornatis monumenta iustorum
Kaiton ku marubuta da Farisawa, munafukai! Ku kan gina kaburburan annabawa, kuna kuma kawata kaburburan adalai.
30 et dicitis si fuissemus in diebus patrum nostrorum non essemus socii eorum in sanguine prophetarum
Kuna cewa, 'Da muna nan a zamanin Ubanninmu, da bamu basu goyon baya ba wajen zubar da jinin annabawa.'
31 itaque testimonio estis vobismet ipsis quia filii estis eorum qui prophetas occiderunt
Domin haka kun shaida kanku ku ne 'ya'yan masu kisan annabawa.
32 et vos implete mensuram patrum vestrorum
Sai kuma kuka cika ma'aunin ubanninku!
33 serpentes genimina viperarum quomodo fugietis a iudicio gehennae (Geenna )
macizai, Ku 'ya'yan ganshekai, Yaya zaku tsere wa hukuncin Gidan wuta? (Geenna )
34 ideo ecce ego mitto ad vos prophetas et sapientes et scribas ex illis occidetis et crucifigetis et ex eis flagellabitis in synagogis vestris et persequemini de civitate in civitatem
Saboda haka, duba, ina aiko maku da annabawa, da masu hikima da marubuta. Za ku kashe wadansun su kuma ku gicciye su. Zaku yiwa wasu bulala a majami'un ku, kuna bin su gari gari.
35 ut veniat super vos omnis sanguis iustus qui effusus est super terram a sanguine Abel iusti usque ad sanguinem Zacchariae filii Barachiae quem occidistis inter templum et altare
Sakamakon hakan alhakin jinin dukkan adalai da aka zubar a duniya ya komo a kan ku, tun daga jinin Habila adali har ya zuwa na Zakariya dan Barakiya, wanda kuka kashe a tsakanin Haikali da bagadi.
36 amen dico vobis venient haec omnia super generationem istam
Hakika, Ina gaya maku, duk wannan zai auko wa mutanen wannan zamani.
37 Hierusalem Hierusalem quae occidis prophetas et lapidas eos qui ad te missi sunt quotiens volui congregare filios tuos quemadmodum gallina congregat pullos suos sub alas et noluisti
Urushalima, Urushalima, keda kika kashe annabawa kika kuma jejjefi wadanda aka turo maki da duwatsu! Sau nawa ne naso in tattaro ki kamar yadda kaza take tattara 'yan tsakinta cikin fukafukanta, amma kin ki.
38 ecce relinquitur vobis domus vestra deserta
Ga shi an bar maku gidan ku a yashe!
39 dico enim vobis non me videbitis amodo donec dicatis benedictus qui venit in nomine Domini
Ina dai gaya maku, ba za ku kara gani na ba, sai ran da kuka ce, 'Albarka ta tabbata ga mai zuwa cikin sunan Ubangiji.”'