< Mattheum 2 >
1 cum ergo natus esset Iesus in Bethleem Iudaeae in diebus Herodis regis ecce magi ab oriente venerunt Hierosolymam
Bayanda aka haifi Yesu a Baitalami ta kasar Yahudiya, a zamanin sarki Hirudus, sai ga wadansu masana daga gabas suka zo Urushalima, suna cewa,
2 dicentes ubi est qui natus est rex Iudaeorum vidimus enim stellam eius in oriente et venimus adorare eum
''Ina wanda aka haifa sarkin Yahudawa? Mun ga tauraronsa a gabas mun kuma zo mu yi masa sujada.''
3 audiens autem Herodes rex turbatus est et omnis Hierosolyma cum illo
Da sarki Hirudus ya ji haka, sai ya damu kwarai, haka kuma dukan mutanen Urushalima.
4 et congregans omnes principes sacerdotum et scribas populi sciscitabatur ab eis ubi Christus nasceretur
Hirudus ya tara dukan manyan firistoci da marubuta na jama'a, ya tambaye su, “Ina za a haifi Almasihun?”
5 at illi dixerunt ei in Bethleem Iudaeae sic enim scriptum est per prophetam
Suka ce masa, ''A Baitalami ne ta kasar Yahudiya, domin haka annabin ya rubuta,
6 et tu Bethleem terra Iuda nequaquam minima es in principibus Iuda ex te enim exiet dux qui reget populum meum Israhel
'Ke kuma, Baitalami, ta kasar Yahudiya, ba ke ce mafi kankanta ba a cikin shugabanin Yahudiya, domin daga cikin ki mai mulki zai fito wanda zai zama makiyayin jama'a ta Isra'ila.'''
7 tunc Herodes clam vocatis magis diligenter didicit ab eis tempus stellae quae apparuit eis
Sai Hirudus ya kira masanan a asirce ya tambaye su aininhin lokacin da tauraron ya bayyana.
8 et mittens illos in Bethleem dixit ite et interrogate diligenter de puero et cum inveneritis renuntiate mihi ut et ego veniens adorem eum
Ya aike su Baitalami, ya ce, ''Ku je ku binciko mani dan yaron da kyau. Idan kun same shi, ku kawo mani labari, don ni ma in je in yi masa sujada.”
9 qui cum audissent regem abierunt et ecce stella quam viderant in oriente antecedebat eos usque dum veniens staret supra ubi erat puer
Bayan sun ji maganar sarkin, sai suka yi tafiyar su, ga shi kuwa, tauraron da suka gani a gabas yana tafe a gaban su, har ya zo ya tsaya bisa inda dan yaron nan yake.
10 videntes autem stellam gavisi sunt gaudio magno valde
Da suka ga tauraron, sai suka yi matukar farin ciki.
11 et intrantes domum invenerunt puerum cum Maria matre eius et procidentes adoraverunt eum et apertis thesauris suis obtulerunt ei munera aurum tus et murram
Sai suka shiga gidan, suka ga dan yaron tare da mahaifiyarsa Maryamu. Suka rusuna gabansa suka yi masa sujada. Sa'an nan suka kwance kayansu, suka mika masa kyautar su ta zinariya da lubban, da mur.
12 et responso accepto in somnis ne redirent ad Herodem per aliam viam reversi sunt in regionem suam
Allah kuma ya gargade su a mafarki kada su koma wurin Hirudus, sai suka koma kasarsu ta wata hanya dabam.
13 qui cum recessissent ecce angelus Domini apparuit in somnis Ioseph dicens surge et accipe puerum et matrem eius et fuge in Aegyptum et esto ibi usque dum dicam tibi futurum est enim ut Herodes quaerat puerum ad perdendum eum
Bayan sun tashi, sai ga wani mala'ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusufu a mafarki, ya ce, ''Tashi, ka dauki dan yaron da mahaifiyarsa, ka gudu zuwa kasar Masar, ka zauna a can sai na fada maka, don Hirudus yana shirin binciko dan yaron ya hallaka shi.”
14 qui consurgens accepit puerum et matrem eius nocte et recessit in Aegyptum
A wannan dare fa Yusufu ya tashi ya dauki dan yaron da mahafiyarsa ya tafi Masar.
15 et erat ibi usque ad obitum Herodis ut adimpleretur quod dictum est a Domino per prophetam dicentem ex Aegypto vocavi filium meum
Ya zauna a can har mutuwar Hirudus. Wannan kuwa domin a cika abin da Ubangiji ya fada ne ta bakin annabin, ''Daga Masar na kirawo Da na.''
16 tunc Herodes videns quoniam inlusus esset a magis iratus est valde et mittens occidit omnes pueros qui erant in Bethleem et in omnibus finibus eius a bimatu et infra secundum tempus quod exquisierat a magis
Da Hirudus ya ga masanan nan sun shashantar da shi, sai ya hasala kwarai, ya aika a karkashe dukan 'yan yara maza da suke Baitalami da kewayenta, daga masu shekara biyu zuwa kasa, gwargwadon lokacin da ya tabbatar a gun masanan.
17 tunc adimpletum est quod dictum est per Hieremiam prophetam dicentem
A lokacin ne aka cika fadar Annabi Irmiya,
18 vox in Rama audita est ploratus et ululatus multus Rachel plorans filios suos et noluit consolari quia non sunt
''An ji wata murya a Rama, tana kuka da bakin ciki mai zafi, Rahila ce take kuka saboda 'ya'yanta, kuma ta ki ta ta'azantu, domin ba su.
19 defuncto autem Herode ecce apparuit angelus Domini in somnis Ioseph in Aegypto
Sa'adda Hirudus ya mutu, sai ga mala'ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusufu a mafarki a Masar ya ce,
20 dicens surge et accipe puerum et matrem eius et vade in terram Israhel defuncti sunt enim qui quaerebant animam pueri
''Tashi ka dauki dan yaron da mahaifiyarsa, ka tafi kasar Isra'ila, domin masu neman ran dan yaron sun mutu.''
21 qui surgens accepit puerum et matrem eius et venit in terram Israhel
Yusufu ya tashi, ya dauki dan yaron da mahaifiyarsa, ya zo kasar Isra'ila.
22 audiens autem quod Archelaus regnaret in Iudaea pro Herode patre suo timuit illo ire et admonitus in somnis secessit in partes Galilaeae
Amma da ya ji Arkilayus ya gaji mahaifinsa Hirudus, yana mulkin kasar Yahudiya, sai ya ji tsoron isa can. Bayan da Allah ya yi masa gargadi a mafarki, sai ya ratse zuwa kasar Galili
23 et veniens habitavit in civitate quae vocatur Nazareth ut adimpleretur quod dictum est per prophetas quoniam Nazareus vocabitur
sai ya je ya zauna a wani gari da ake kira Nazarat. Wannan ya cika abin da aka fada ta bakin annabawa, cewa, za a kira shi Banazare.