< Lucam 24 >

1 una autem sabbati valde diluculo venerunt ad monumentum portantes quae paraverant aromata
Da sassafe a ranar farko ta mako, suka zo kabarin, suka kawo kayan kamshi wadda suka shirya.
2 et invenerunt lapidem revolutum a monumento
Sai suka samu dutsen a mirgine shi daga kabarin.
3 et ingressae non invenerunt corpus Domini Iesu
Suka shiga ciki, amma ba su sami jikin Ubangiji Yesu ba.
4 et factum est dum mente consternatae essent de isto ecce duo viri steterunt secus illas in veste fulgenti
Ya faru kuwa, yayin da suke a rikice game da wannan, ba zato, mutane guda biyu suka tsaya a gabansu da tufafi masu walkiya.
5 cum timerent autem et declinarent vultum in terram dixerunt ad illas quid quaeritis viventem cum mortuis
Sa'adda matan suka sunkuyar da kansu kasa domin tsoro, suka ce wa matan, “Don me kuke neman mai rai ciki matattatu?
6 non est hic sed surrexit recordamini qualiter locutus est vobis cum adhuc in Galilaea esset
Baya nan, amma ya tashi! Ku tuna fa yadda ya yi maku magana tun sa'adda ya ke Galili,
7 dicens quia oportet Filium hominis tradi in manus hominum peccatorum et crucifigi et die tertia resurgere
cewa za a ba da Dan Mutum ga mutane masu zunubi su kuma giciye shi, a rana ta uku, zai tashi kuma”
8 et recordatae sunt verborum eius
Sai matan suka tuna da kalmominsa,
9 et regressae a monumento nuntiaverunt haec omnia illis undecim et ceteris omnibus
suka koma daga kabarin sai suka gaya wa sha dayan wadannan abubuwan da dukan sauran.
10 erat autem Maria Magdalene et Iohanna et Maria Iacobi et ceterae quae cum eis erant quae dicebant ad apostolos haec
Su Maryamu Magadaliya, Yuwana, Maryamu uwar Yakubu, da sauran matan da ke tare da su suka ba manzanni rohoton wadannan abubuwan.
11 et visa sunt ante illos sicut deliramentum verba ista et non credebant illis
Amma manzannin suka dauki maganar kamar ba ta da amfani, kuma ba su bada gaskiya ga matan ba.
12 Petrus autem surgens cucurrit ad monumentum et procumbens videt linteamina sola posita et abiit secum mirans quod factum fuerat
Duk da haka Bitrus ya tashi, sai ya gudu zuwa kabarin, ya sunkuya yana kallon ciki, sai ya gan likaftani linin kadai. Sa'annan Bitrus ya tafi gidansa, yana ta mamakin abinda ya faru.
13 et ecce duo ex illis ibant ipsa die in castellum quod erat in spatio stadiorum sexaginta ab Hierusalem nomine Emmaus
A ranan nan, sai ga biyu daga cikinsu suna tafiya zuwa wani kauye suna Imawus, wanda nisansa kimanin mil ne daga Urushalima.
14 et ipsi loquebantur ad invicem de his omnibus quae acciderant
Suna tattaunawa da junansu game da dukan abubuwan da suka faru.
15 et factum est dum fabularentur et secum quaererent et ipse Iesus adpropinquans ibat cum illis
Sai ya zama da cewa, sa'adda su ke tattaunawa tare da tambayoyi, sai Yesu da kansa ya matsa kusa yana tafiya tare da su.
16 oculi autem illorum tenebantur ne eum agnoscerent
Amma idanunsu basu iya ganewa da shi ba.
17 et ait ad illos qui sunt hii sermones quos confertis ad invicem ambulantes et estis tristes
Yesu ya ce masu, “Menene ku ke magana akai sa'adda ku ke tafiya?” Suka tsaya a wurin suna bakin ciki.
18 et respondens unus cui nomen Cleopas dixit ei tu solus peregrinus es in Hierusalem et non cognovisti quae facta sunt in illa his diebus
Daya daga cikinsu, mai suna Kiliyobas, ya amsa masa, “Kai ne kadai mutumin da ke Urushalima wanda bai san abubuwan da suka faru a can a wannan kwanakin ba?”
19 quibus ille dixit quae et dixerunt de Iesu Nazareno qui fuit vir propheta potens in opere et sermone coram Deo et omni populo
Yesu ya ce masu, “Wadanne abubuwa?” Suka amsa masa, “Abubuwa game da Yesu ba Nazarat, wanda ya ke annabi ne, mai manyan ayuka da kalmomi daga Allah da kuma mutane.
20 et quomodo eum tradiderunt summi sacerdotum et principes nostri in damnationem mortis et crucifixerunt eum
Da yadda manyan firistoci da masu mulkinmu suka bada shi domin a hukunta shi ga mutuwa a kuma giciye shi.
21 nos autem sperabamus quia ipse esset redempturus Israhel et nunc super haec omnia tertia dies hodie quod haec facta sunt
Amma mun yi begen cewa shine wanda za ya yantar da Isra'ila. I, bayan wannan kuma, yanzu kwana uku kenan tunda wadannan abubuwan suka faru.
22 sed et mulieres quaedam ex nostris terruerunt nos quae ante lucem fuerunt ad monumentum
Amma har'ila yau, wadansu mata da ke tare da mu sun yi mana abin al'ajabi, da suka kasance a kabarin tunda sassafe.
23 et non invento corpore eius venerunt dicentes se etiam visionem angelorum vidisse qui dicunt eum vivere
Sa'adda ba su sami jikinsa ba, suka zo, da cewa su ma sun ga wahayin mala'iku wadanda suka ce masu ya na da rai.
24 et abierunt quidam ex nostris ad monumentum et ita invenerunt sicut mulieres dixerunt ipsum vero non viderunt
Wasu maza wadanda ke tare da mu suka tafi kabarin, suka tarar da shi kamar yadda matan suka fada. Amma ba su ganshi ba.”
25 et ipse dixit ad eos o stulti et tardi corde ad credendum in omnibus quae locuti sunt prophetae
Yesu ya ce masu, “Ku mutane masu wauta da marasa ba da gaskiya ga abin da annabawa suka fada!
26 nonne haec oportuit pati Christum et ita intrare in gloriam suam
Bai zama dole ne Almasihu ya sha wahalan wadannan abubuwan ba, ya kuma shiga cikin daukakarsa?”
27 et incipiens a Mose et omnibus prophetis interpretabatur illis in omnibus scripturis quae de ipso erant
Sa'annan da farko daga Musa da har zuwa dukan annabawa, Yesu ya fasara masu duka abubuwa da ke game da kansa a dukan littattafai.
28 et adpropinquaverunt castello quo ibant et ipse se finxit longius ire
Da suka yi kusa da kauyen, inda suke tafiya, ko da yake Yesu ya yi kamar zai wuce su.
29 et coegerunt illum dicentes mane nobiscum quoniam advesperascit et inclinata est iam dies et intravit cum illis
Amma suka tilasta shi, cewa, “Ka zauna da mu, gama yamma ta yi kusa rana kuma ta kusa karewa.” Sai Yesu ya tafi ya zauna da su.
30 et factum est dum recumberet cum illis accepit panem et benedixit ac fregit et porrigebat illis
Ya faru cewa, sa'adda ya zauna tare da su domin ya ci abinci, sai ya dauki gurasan, ya albarkace shi, ya kakkarya, sai ya ba su.
31 et aperti sunt oculi eorum et cognoverunt eum et ipse evanuit ex oculis eorum
Sa'annan idanunsu suka bude, da suka gane shi, sai ya bace daga garesu,
32 et dixerunt ad invicem nonne cor nostrum ardens erat in nobis dum loqueretur in via et aperiret nobis scripturas
Suka ce wa junansu, ashe zuciyarmu ba ta yi kuna a cikinmu ba, sa'adda yake magana da mu a hanya, sa'adda ya bude mana littattafai?”
33 et surgentes eadem hora regressi sunt in Hierusalem et invenerunt congregatos undecim et eos qui cum ipsis erant
Suka tashi a wancan sa'a, sai suka koma Urushalima. Suka sami sha dayan nan tare, da wadanda suke tare da su,
34 dicentes quod surrexit Dominus vere et apparuit Simoni
cewa, “Lalle ne Ubangiji ya tashi, ya kuma bayyana ga Siman.”
35 et ipsi narrabant quae gesta erant in via et quomodo cognoverunt eum in fractione panis
Sai suka fadi abubuwan da suka faru a hanya, da yadda aka bayyana masu Yesu sa'adda ya kakkarya gurasa.
36 dum haec autem loquuntur Iesus stetit in medio eorum et dicit eis pax vobis ego sum nolite timere
Sa'adda suke fadin wadannan abubuwan, sai Yesu ya tsaya a sakaninsu, sai ya ce masu, “Salama a gareku.”
37 conturbati vero et conterriti existimabant se spiritum videre
Amma suka firgita suna cike da tsoro, suna tsammani sun ga fatalwa.
38 et dixit eis quid turbati estis et cogitationes ascendunt in corda vestra
Yesu ya ce masu, don me ku ke damuwa? Don me tambayoyi ke tasowa a zuciyarku?
39 videte manus meas et pedes quia ipse ego sum palpate et videte quia spiritus carnem et ossa non habet sicut me videtis habere
Duba hannayena da kafafuna, cewa nine da kaina. Taba ni ku gani. Gama ruhu ba shi da jiki da kashi, kamar yadda ku ka ga nake da su.”
40 et cum hoc dixisset ostendit eis manus et pedes
Bayan da ya fadi wannan, sai ya nuna masu hannayensa da kafafunsa.
41 adhuc autem illis non credentibus et mirantibus prae gaudio dixit habetis hic aliquid quod manducetur
Sa'adda suke cike da farin ciki, da mamaki, Yesu ya ce masu, “Kuna da wani abinci?”
42 at illi obtulerunt ei partem piscis assi et favum mellis
Sai suka bashi gasasshen kifi.
43 et cum manducasset coram eis sumens reliquias dedit eis
Yesu ya karba, ya ci a gabansu.
44 et dixit ad eos haec sunt verba quae locutus sum ad vos cum adhuc essem vobiscum quoniam necesse est impleri omnia quae scripta sunt in lege Mosi et prophetis et psalmis de me
Sai ya ce masu, “Sa'adda nake tare da ku na gaya maku cewa duka abin da aka rubuta a cikin dokokin Musa da na annabawa da Zabura dole su cika.”
45 tunc aperuit illis sensum ut intellegerent scripturas
Sai ya bude hankalinsu, saboda su gane littattafai.
46 et dixit eis quoniam sic scriptum est et sic oportebat Christum pati et resurgere a mortuis die tertia
Ya ce masu, “A rubuce yake, cewa Almasihu za ya sha wuya, zai tashi kuma daga matattu a rana ta uku.
47 et praedicari in nomine eius paenitentiam et remissionem peccatorum in omnes gentes incipientibus ab Hierosolyma
Ku yi wa'azin tuba da gafarar zunubai a cikin sunansa ga dukan al'ummai, ku fara daga Urushalima.
48 vos autem estis testes horum
Ku shaidu ne ga wadannan abubuwan.
49 et ego mitto promissum Patris mei in vos vos autem sedete in civitate quoadusque induamini virtutem ex alto
Duba, ina aiko da alkawarin Ubana a kanku. Amma ku jira a birni, sai an suturta ku da iko daga sama.”
50 eduxit autem eos foras in Bethaniam et elevatis manibus suis benedixit eis
Sa'annan Yesu ya tafi tare da su har sai da suka kai kusa da Betanya. Sai ya daga hannunsa ya albarkace su.
51 et factum est dum benediceret illis recessit ab eis et ferebatur in caelum
Ya zama sa'adda yake sa masu albarka, ya bar su sai aka dauke shi zuwa cikin sama.
52 et ipsi adorantes regressi sunt in Hierusalem cum gaudio magno
Sai suka yi masa sujada, suka komo Urushalima da murna mai yawa.
53 et erant semper in templo laudantes et benedicentes Deum amen
Kullayaumin suna cikin haikali, suna albarkatar Allah.

< Lucam 24 >