< Lucam 13 >

1 aderant autem quidam ipso in tempore nuntiantes illi de Galilaeis quorum sanguinem Pilatus miscuit cum sacrificiis eorum
A yanzun fa, akwai waɗansu da suka kasance a lokacin can, suka ba Yesu labarin Galiliyawa da Bilatus ya gauraye jininsu tare da jinin hadayunsu.
2 et respondens dixit illis putatis quod hii Galilaei prae omnibus Galilaeis peccatores fuerunt quia talia passi sunt
Yesu ya amsa ya ce, “Kuna tsammani waɗannan Galiliyawan sun fi dukan sauran Galiliyawa zunubi ne, shi ya sa suka sha irin wannan wahala?
3 non dico vobis sed nisi paenitentiam habueritis omnes similiter peribitis
Ina gaya muku, a’a! Amma in ba ku tuba ba, ku ma duka za ku hallaka.
4 sicut illi decem et octo supra quos cecidit turris in Siloam et occidit eos putatis quia et ipsi debitores fuerunt praeter omnes homines habitantes in Hierusalem
Ko kuwa kuna tsammani, sha takwas ɗin nan da suka mutu lokacin da hasumiya a Silowam ya fāɗi a kansu, sun fi dukan sauran mutanen Urushalima laifi ne?
5 non dico vobis sed si non paenitentiam egeritis omnes similiter peribitis
Ina gaya muku, a’a! Amma in ba ku tuba ba, ku ma duka za ku hallaka.”
6 dicebat autem hanc similitudinem arborem fici habebat quidam plantatam in vinea sua et venit quaerens fructum in illa et non invenit
Sai ya ba su wannan misali ya ce, “Wani mutum yana da itacen ɓaure, da aka shuka a gonar inabinsa. Da ya je cire’ya’yan itacen, sai ya tarar ba tă yi’ya’ya ba.
7 dixit autem ad cultorem vineae ecce anni tres sunt ex quo venio quaerens fructum in ficulnea hac et non invenio succide ergo illam ut quid etiam terram occupat
Sai ya ce wa mai lura da gonar inabin, ‘Yau shekara uku ke nan ina zuwa neman’ya’yan ɓaure daga itacen nan, amma ba na samun kome. Sare shi! Don me za a bar shi ya tare wuri.’
8 at ille respondens dixit illi domine dimitte illam et hoc anno usque dum fodiam circa illam et mittam stercora
“Mutumin ya amsa ya ce, ‘Ranka yă daɗe, ka bar shi, in yi masa banƙasa, in kuma zuba masa taki har na shekara ɗaya.
9 et si quidem fecerit fructum sin autem in futurum succides eam
In kuwa ya ba da’ya’ya shekara mai zuwa, yana da kyau! In kuwa ba haka ba, sai ka sare shi.’”
10 erat autem docens in synagoga eorum sabbatis
Wata ranar Asabbaci, Yesu yana koyarwa a wata majami’a,
11 et ecce mulier quae habebat spiritum infirmitatis annis decem et octo et erat inclinata nec omnino poterat sursum respicere
a wurin kuwa, akwai wata mace wadda aljani ya gurgunta, har na shekaru goma sha takwas. Duk ta tanƙware, ba ta ma iya miƙewa ko kaɗan.
12 quam cum videret Iesus vocavit ad se et ait illi mulier dimissa es ab infirmitate tua
Da Yesu ya gan ta, sai ya kirata gaba, ya ce mata, “Mace, an’yantar da ke daga rashin lafiyarki.”
13 et inposuit illi manus et confestim erecta est et glorificabat Deum
Sai ya ɗibiya hannuwansa a kanta, nan da nan sai ta miƙe, ta yabi Allah.
14 respondens autem archisynagogus indignans quia sabbato curasset Iesus dicebat turbae sex dies sunt in quibus oportet operari in his ergo venite et curamini et non in die sabbati
Amma mai mulkin majami’ar ya ji haushi da Yesu ya yi warkarwa a ranar Asabbaci. Sai ya ce wa mutanen, “Akwai ranaku shida da ya kamata a yi aiki. Saboda haka, ku zo a ranakun nan a warkar da ku, ba ranar Asabbaci ba.”
15 respondit autem ad illum Dominus et dixit hypocritae unusquisque vestrum sabbato non solvit bovem suum aut asinum a praesepio et ducit adaquare
Ubangiji ya amsa masa ya ce, “Ku munafukai! Ashe, kowannenku ba yakan kunce bijiminsa ko jakinsa, yă kai shi waje yă ba shi ruwa, a ranar Asabbaci ba?
16 hanc autem filiam Abrahae quam alligavit Satanas ecce decem et octo annis non oportuit solvi a vinculo isto die sabbati
Ashe, bai kamata a’yantar da macen nan, diyar zuriyar Ibrahim, wadda Shaiɗan ya daure, har shekara goma sha takwas, a ranar Asabbaci, daga abin da ya daure ta ba?”
17 et cum haec diceret erubescebant omnes adversarii eius et omnis populus gaudebat in universis quae gloriose fiebant ab eo
Sa’ad da ya faɗi wannan, sai duka masu gāba da shi suka kunyata. Amma mutane kuwa suka yi murna saboda dukan abubuwan banmamaki da yake yi.
18 dicebat ergo cui simile est regnum Dei et cui simile esse existimabo illud
Sai Yesu ya yi tambaya ya ce, “Yaya mulkin Allah yake? Da me zan kwatanta shi?
19 simile est grano sinapis quod acceptum homo misit in hortum suum et crevit et factum est in arborem magnam et volucres caeli requieverunt in ramis eius
Yana kama da ƙwayar mustad, wadda wani mutum ya ɗauka, kuma ya shuka a gonarsa. Ta yi girma, ta zama itace, kuma tsuntsayen sararin sama suka huta a rassansa.”
20 et iterum dixit cui simile aestimabo regnum Dei
Ya sāke tambaya, “Da me zan kwatanta mulkin Allah?
21 simile est fermento quod acceptum mulier abscondit in farinae sata tria donec fermentaretur totum
Yana kama da yisti wadda mace ta ɗauka, ta kwaɓa garin alkama mai yawa da shi, har sai da yistin ya gauraye kullun duka.”
22 et ibat per civitates et castella docens et iter faciens in Hierusalem
Sa’ad da Yesu yana kan hanyarsa zuwa Urushalima, sai ya bi ta cikin garuruwan da ƙauyukan, yana koyarwa.
23 ait autem illi quidam Domine si pauci sunt qui salvantur ipse autem dixit ad illos
Sai wani ya tambaye shi ya ce, “Ya Ubangiji, shin, wai mutane kima ne kawai za su sami ceto?” Ya ce musu,
24 contendite intrare per angustam portam quia multi dico vobis quaerunt intrare et non poterunt
“Ku yi matuƙar ƙoƙari ku shiga ta matsattsiyar ƙofa, domin ina faɗa muku, mutane da yawa za su yi ƙoƙarin shiga, amma ba za su iya ba.
25 cum autem intraverit pater familias et cluserit ostium et incipietis foris stare et pulsare ostium dicentes Domine aperi nobis et respondens dicet vobis nescio vos unde sitis
Da zaran maigidan ya tashi ya rufe ƙofar, za ku tsaya a waje kuna ƙwanƙwasawa, kuna roƙo cewa, ‘Ranka yă daɗe, buɗe mana ƙofa.’ “Amma shi zai amma ya ce, ‘Ni ban san ku, ko inda kuka fito ba.’
26 tunc incipietis dicere manducavimus coram te et bibimus et in plateis nostris docuisti
“Sa’an nan za ku ce, ‘Haba, mu da muka ci, muka sha tare da kai, har ka yi koyarwa a cikin titi-titi namu.’
27 et dicet vobis nescio vos unde sitis discedite a me omnes operarii iniquitatis
“Amma shi zai amma ya ce, ‘Ban san ku, ko inda kuka fito ba. Ku rabu da ni, dukan ku masu aikata mugunta!’
28 ibi erit fletus et stridor dentium cum videritis Abraham et Isaac et Iacob et omnes prophetas in regno Dei vos autem expelli foras
“Za a yi kuka a can, da cizon haƙora, sa’ad da kuka ga Ibrahim, da Ishaku, da Yaƙub, da dukan annabawa a mulkin Allah, amma ku kuwa, za a jefar da ku a waje.
29 et venient ab oriente et occidente et aquilone et austro et accumbent in regno Dei
Mutane za su zo daga gabas, da yamma, da kudu, da arewa, su ɗauki wuraren zamansu a bikin, a cikin mulkin Allah.
30 et ecce sunt novissimi qui erunt primi et sunt primi qui erunt novissimi
Tabbatacce, akwai waɗansu da suke na ƙarshe, da za su zama na farko, na farko kuma, da za su zama na ƙarshe.”
31 in ipsa die accesserunt quidam Pharisaeorum dicentes illi exi et vade hinc quia Herodes vult te occidere
A wannan lokaci, waɗansu Farisiyawa suka zo suka ce wa Yesu, “Ka bar nan ka tafi wani wuri dabam. Hiridus yana so ya kashe ka.”
32 et ait illis ite dicite vulpi illi ecce eicio daemonia et sanitates perficio hodie et cras et tertia consummor
Ya amsa ya ce, “Ku je ku gaya wa dilan nan, wato, mai makirci cewa, ‘Da yau da kuma gobe, zan fitar da aljanu, in kuma warkar da mutane, sa’an nan a rana ta uku in cika burin aikina.
33 verumtamen oportet me hodie et cras et sequenti ambulare quia non capit prophetam perire extra Hierusalem
Duk da haka, dole in ci gaba da aikin a yau, da kuma gobe, sa’an nan in ci gaba da yin haka kashegari kuma, gama tabbatacce, ba annabi da yakan mutu a bayan birnin Urushalima!’
34 Hierusalem Hierusalem quae occidis prophetas et lapidas eos qui mittuntur ad te quotiens volui congregare filios tuos quemadmodum avis nidum suum sub pinnis et noluisti
“Urushalima, ayya Urushalima, ke da kika kashe annabawa, kuma kika jefa wa waɗanda aka aika gare ki da duwatsu. Sau da yawa na yi kewan in tattara’ya’yanki wuri ɗaya, kamar yadda kaza takan tattara’ya’yanta cikin fikafikanta, amma ba ki yarda ba!
35 ecce relinquitur vobis domus vestra dico autem vobis quia non videbitis me donec veniat cum dicetis benedictus qui venit in nomine Domini
Duba, an bar muku gidanku fanko. Ina kuwa faɗa muku, ba za ku sāke ganina ba, sai kun ce, ‘Mai albarka ne shi wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji.’”

< Lucam 13 >