< Leviticus 12 >
1 locutus est Dominus ad Mosen dicens
Ubangiji ya ce wa Musa,
2 loquere filiis Israhel et dices ad eos mulier si suscepto semine pepererit masculum inmunda erit septem diebus iuxta dies separationis menstruae
“Faɗa wa Isra’ilawa, ‘Macen da ta yi ciki ta kuma haihu ɗa namiji za tă ƙazantu kwana bakwai, kamar yadda takan ƙazantu a lokacin al’adarta.
3 et die octavo circumcidetur infantulus
A rana ta takwas, za a yi wa yaron kaciya.
4 ipsa vero triginta tribus diebus manebit in sanguine purificationis suae omne sanctum non tanget nec ingredietur sanctuarium donec impleantur dies purificationis eius
Sa’an nan dole macen ta jira kwana talatin don a tsabtacce ta daga zub da jini. Ba za tă taɓa wani abu mai tsarki, ko ta je wuri mai tsarki ba sai kwanakin tsabtaccewarta sun cika.
5 sin autem feminam pepererit inmunda erit duabus ebdomadibus iuxta ritum fluxus menstrui et sexaginta ac sex diebus manebit in sanguine purificationis suae
In ta haifi’ya ta mace ce, makoni biyu macen za tă ƙazantu kamar yadda takan kasance a lokacin al’adarta. Sa’an nan dole tă jira kwana sittin don a tsabtacce ta daga zub da jininta.
6 cumque expleti fuerint dies purificationis eius pro filio sive pro filia deferet agnum anniculum in holocaustum et pullum columbae sive turturem pro peccato ad ostium tabernaculi testimonii et tradet sacerdoti
“‘Sa’ad da kwanakin tsabtaccewarta don ɗa namiji ko’ya ta mace suka cika, sai ta kawo ɗan rago bana ɗaya wa firist a bakin ƙofar Tentin Sujada don hadaya ta ƙonawa da tattabara ko kurciya na hadaya don zunubi.
7 qui offeret illa coram Domino et rogabit pro ea et sic mundabitur a profluvio sanguinis sui ista est lex parientis masculum ac feminam
Firist zai miƙa su a gaban Ubangiji don yă yi kafara dominta, sa’an nan tă tsabtacce daga zub da jininta. “‘Waɗannan su ne ƙa’idodi domin macen da ta haifi ɗa namiji ko’ya ta mace.
8 quod si non invenerit manus eius nec potuerit offerre agnum sumet duos turtures vel duos pullos columbae unum in holocaustum et alterum pro peccato orabitque pro ea sacerdos et sic mundabitur
In ba za tă iya kawo ɗan rago ba, sai ta kawo kurciyoyi biyu ko tattabarai biyu, ɗaya domin hadaya ta ƙonawa ɗayan kuma domin hadaya don zunubi. Ta haka firist zai yi kafara dominta, za tă kuwa zama tsabtacciya.’”