< Iudicum 1 >

1 post mortem Iosue consuluerunt filii Israhel Dominum dicentes quis ascendet ante nos contra Chananeum et erit dux belli
Bayan da Yoshuwa ya rasu, Isra’ilawa suka tambayi Ubangiji suka ce, “Wane ne zai fara tafiya don yă yaƙi Kan’aniyawa dominmu?”
2 dixitque Dominus Iudas ascendet ecce tradidi terram in manus eius
Sai Ubangiji ya ce, “Yahuda zai tafi. Na riga na ba da ƙasar a hannunsu.”
3 et ait Iudas Symeoni fratri suo ascende mecum in sorte mea et pugna contra Chananeum ut et ego pergam tecum in sorte tua et abiit cum eo Symeon
Sa’an nan mutane Yahuda suka ce wa mutanen Simeyon “Ku zo tare da mu a yankin da aka ba mu rabon mu don mu yaƙi Kan’aniyawa. Mu ma mu bi ku wurin naku.” Saboda haka mutanen Simeyon suka tafi tare da su.
4 ascenditque Iudas et tradidit Dominus Chananeum ac Ferezeum in manus eorum et percusserunt in Bezec decem milia virorum
Sa’ad da Yahuda ya fāɗa musu, Ubangiji kuwa ya ba da Kan’aniyawa da Ferizziyawa a hannunsu, suka kuwa kashe mutum dubu goma a Bezek.
5 inveneruntque Adonibezec in Bezec et pugnaverunt contra eum ac percusserunt Chananeum et Ferezeum
A can suka iske Adoni-Bezek, suka yaƙe shi, suka fatattaki Kan’aniyawa da Ferizziyawa.
6 fugit autem Adonibezec quem secuti conprehenderunt caesis summitatibus manuum eius ac pedum
Sai Adoni-Bezek ya gudu, amma suka bi shi suka kama shi, suka yayyanka manyan yatsotsinsa na hannu da na ƙafa.
7 dixitque Adonibezec septuaginta reges amputatis manuum ac pedum summitatibus colligebant sub mensa mea ciborum reliquias sicut feci ita reddidit mihi Deus adduxeruntque eum in Hierusalem et ibi mortuus est
Sa’an nan Adoni-Bezek ya ce, “Sarakuna saba’in waɗanda aka yayyanka manyan yatsotsinsu na hannu da na ƙafa, sun yi kalan abinci a ƙarƙashin teburina. Ga shi yanzu Allah ya rama abin da na yi musu.” Suka zo da shi Urushalima, a can kuwa ya mutu.
8 obpugnantes ergo filii Iuda Hierusalem ceperunt eam et percusserunt in ore gladii tradentes cunctam incendio civitatem
Mutanen Yahuda suka yaƙi Urushalima ita ma suka ci ta. Suka karkashe mutanen birnin suka cinna mata wuta.
9 et postea descendentes pugnaverunt contra Chananeum qui habitabat in montanis et ad meridiem et in campestribus
Bayan wannan, mutanen Yahuda suka gangara suka yaƙi Kan’aniyawan da suke zaune a ƙasar tudu, Negeb, da gindin tuddai a yammanci.
10 pergensque Iudas contra Chananeum qui habitabat in Hebron cui nomen fuit antiquitus Cariatharbe percussit Sisai et Ahiman et Tholmai
Suka ci gaba suka yaƙi Kan’aniyawan da suke zaune a Hebron (wadda dā ake kira Kiriyat Arba) suka kuma ci Sheshai, Ahiman da Talmai da yaƙi.
11 atque inde profectus abiit ad habitatores Dabir cuius nomen vetus erat Cariathsepher id est civitas Litterarum
Daga nan kuma suka ci gaba suka yaƙi mutanen da suke zaune a Debir (da ake kira a dā Kiriyat Sefer).
12 dixitque Chaleb qui percusserit Cariathsepher et vastaverit eam dabo ei Axam filiam meam uxorem
Sai Kaleb ya ce, “Duk wanda ya fāɗa wa Kiriyat Sefer ya kuma ci ta da yaƙi, zan ba shi’yata Aksa yă aura.”
13 cumque cepisset eam Othonihel filius Cenez frater Chaleb minor dedit ei filiam suam coniugem
Sai Otniyel ɗan Kenaz, ƙanen Kaleb ya ci birnin, saboda haka Kaleb ya ba shi’yarsa Aksa ya aura.
14 quam pergentem in itinere monuit vir suus ut peteret a patre suo agrum quae cum suspirasset sedens asino dixit ei Chaleb quid habes
Wata rana da ta zo wurin Otniyel, sai ta zuga shi yă roƙi mahaifinta fili. Sa’ad da ta sauko daga jakinta, sai Kaleb ya ce mata, “Me zan yi miki?”
15 at illa respondit da mihi benedictionem quia terram arentem dedisti mihi da et inriguam aquis dedit ergo ei Chaleb inriguum superius et inriguum inferius
Sai ta ce, “Ka yi mini alheri na musamman. Da yake ka ba ni ƙasa a Negeb, to, sai ka ba ni maɓulɓulan ruwa kuma.” Sai Kaleb ya ba ta maɓulɓulan bisa da kuma na ƙasa.
16 filii autem Cinei cognati Mosi ascenderunt de civitate Palmarum cum filiis Iuda in desertum sortis eius quod est ad meridiem Arad et habitaverunt cum eo
Zuriyar surukin Musa, Keniyawa, suka haura daga Birnin dabino tare da mutanen Yahuda don su zauna cikin mutanen Hamadan Yahuda a cikin Negeb kusa da Arad.
17 abiit autem Iudas cum Symeone fratre suo et percusserunt simul Chananeum qui habitabat in Sephath et interfecerunt eum vocatumque est nomen urbis Horma id est anathema
Sa’an nan mutanen Yahuda suka tafi tare da’yan’uwansu mutanen Simeyon suka fāɗa wa Kan’aniyawan da suke zaune cikin Zefat, suka kuwa hallaka birnin gaba ɗaya. Saboda haka aka kira wurin Horma.
18 cepitque Iudas Gazam cum finibus suis et Ascalonem atque Accaron cum terminis suis
Mutanen Yahuda kuma suka ci Gaza, Ashkelon, da Ekron, kowace birni tare da yankinsa.
19 fuitque Dominus cum Iuda et montana possedit nec potuit delere habitatores vallis quia falcatis curribus abundabant
Ubangiji kuwa yana tare da mutane Yahuda. Suka mallaki ƙasar tudu, amma ba su iya suka kori mutanen daga filaye ba, domin suna da keken yaƙin ƙarfe.
20 dederuntque Chaleb Hebron sicut dixerat Moses qui delevit ex ea tres filios Enach
Yadda Musa ya yi alkawari, sai aka ba Kaleb Hebron, wanda ya kori daga cikinta’ya’ya maza uku na Anak.
21 Iebuseum autem habitatorem Hierusalem non deleverunt filii Beniamin habitavitque Iebuseus cum filiis Beniamin in Hierusalem usque in praesentem diem
Ko da yake mutanen Benyamin sun kāsa su kori Yebusiyawa, waɗanda suke zaune a Urushalima; har yă zuwa yau, Yebusiyawa suna zaune a can tare da mutanen Benyamin.
22 domus quoque Ioseph ascendit in Bethel fuitque Dominus cum eis
To, gidan Yusuf suka auka wa Betel, Ubangiji kuwa yana tare da su.
23 nam cum obsiderent urbem quae prius Luza vocabatur
Sa’ad da suka aike mutane don su leƙi asirin Betel (da dā ake kira Luz),
24 viderunt hominem egredientem de civitate dixeruntque ad eum ostende nobis introitum civitatis et faciemus tecum misericordiam
’yan leƙen asirin suka ga wani ya fito daga birnin sai suka ce masa, “Ka nuna mana yadda za mu shiga birnin, mu kuwa za mu yi maka alheri.”
25 qui cum ostendisset eis percusserunt urbem in ore gladii hominem autem illum et omnem cognationem eius dimiserunt
Saboda haka ya nuna musu, suka kuwa hallaka birnin, suka bar mutumin da dukan iyalinsa da rai.
26 qui dimissus abiit in terram Etthim et aedificavit ibi civitatem vocavitque eam Luzam quae ita appellatur usque in praesentem diem
Sa’an nan ya tafi ƙasar Hittiyawa, inda ya gina birni ya kuma kira shi Luz, haka ake kira birnin har wa yau.
27 Manasses quoque non delevit Bethsan et Thanach cum viculis suis et habitatores Dor et Ieblaam et Mageddo cum viculis suis coepitque Chananeus habitare cum eis
Amma Manasse ba su kori mutane Bet-Sheyan ko Ta’anak ko Dor ko Ibileyam ko Megiddo tare da ƙauyukansu ba, gama Kan’aniyawa sun dāge su zauna a wannan ƙasa.
28 postquam autem confortatus est Israhel fecit eos tributarios et delere noluit
Sa’ad da Isra’ila ta yi ƙarfi, sai suka tilasta Kan’aniyawa yin aikin gandu amma ba su kore su gaba ɗaya ba.
29 Ephraim etiam non interfecit Chananeum qui habitabat in Gazer sed habitavit cum eo
Haka Efraim ma bai kori Kan’aniyawa da suke zaune a Gezer ba, amma Kan’aniyawa suka ci gaba da zama tare da su.
30 Zabulon non delevit habitatores Cetron et Naalon sed habitavit Chananeus in medio eius factusque est ei tributarius
Haka kuma Zebulun bai kori Kan’aniyawa da suke zaune a Kitron da Nahalol, waɗanda suka rage a cikinsu ba; sai dai sun sa su aikin gandu.
31 Aser quoque non delevit habitatores Achcho et Sidonis Alab et Achazib et Alba et Afec et Roob
Haka Asher ma bai kori waɗanda suke zama a Akko ko Sidon ko Ahlab ko Akzib ko Helba ko Afik ko kuma Rehob ba,
32 habitavitque in medio Chananei habitatoris illius terrae nec interfecit eum
kuma saboda wannan ne mutanen Asher suke zaune cikin mazaunan ƙasar Kan’aniyawa.
33 Nepthali non delevit habitatores Bethsemes et Bethanath et habitavit inter Chananeum habitatorem terrae fueruntque ei Bethsemitae et Bethanitae tributarii
Haka kuma Naftali bai kori waɗanda suke zaune a Bet-Shemesh ko Bet-Anat; amma mutanen Naftali su ma suna zama a ciki Kan’aniyawa mazaunan ƙasar, waɗanda suke zaune a Bet-Shemesh da Bet-Anat kuwa suka zama masu yi musu aikin gandu.
34 artavitque Amorreus filios Dan in monte nec dedit eis locum ut ad planiora descenderent
Amoriyawa suka matsa wa mutanen Dan a ƙasar tudu, ba su yarda musu su gangaro zuwa filaye ba.
35 habitavitque in monte Hares quod interpretatur testaceo in Ahilon et Salabim et adgravata est manus domus Ioseph factusque est ei tributarius
Su Amoriyawa kuma suka dāge su zauna a Dutsen-Heres, Aiyalon, da Sha’albim. Amma yayinda mutanen Yusuf suka ƙara ƙarfi, sai suka su yin musu aikin gandu.
36 fuit autem terminus Amorrei ab ascensu Scorpionis Petra et superiora loca
Iyakar Amoriyawa kuwa daga Mashigin Kunama zuwa Sela da kuma zuwa gaba.

< Iudicum 1 >