< Iohannem 10 >
1 amen amen dico vobis qui non intrat per ostium in ovile ovium sed ascendit aliunde ille fur est et latro
“Hakika, Hakika, ina ce maku, wanda bai shiga ta kofa zuwa garken tumaki ba, amma ya haura ta wata hanya, wannan mutum barawo ne da dan fashi.
2 qui autem intrat per ostium pastor est ovium
Wanda ya shiga ta kofa shine makiyayin tumakin.
3 huic ostiarius aperit et oves vocem eius audiunt et proprias oves vocat nominatim et educit eas
Mai gadin kofar zai bude masa. Tumakin suna jin muryarsa, ya na kuma kiran tumakinsa da sunayensu, ya kuma kai su waje.
4 et cum proprias oves emiserit ante eas vadit et oves illum sequuntur quia sciunt vocem eius
Bayanda ya kawo su duka a waje, yana tafiya a gabansu, sai tumakin su bi shi, domin sun san muryarsa.
5 alienum autem non sequuntur sed fugient ab eo quia non noverunt vocem alienorum
Ba za su bi bako ba amma sai dai su guje shi, domin basu san muryar baki ba.”
6 hoc proverbium dixit eis Iesus illi autem non cognoverunt quid loqueretur eis
Yesu ya yi masu magana da wannan misali, amma basu gane wadannan abubuwa da yake gaya masu ba.
7 dixit ergo eis iterum Iesus amen amen dico vobis quia ego sum ostium ovium
Sai Yesu ya ce masu kuma, “Hakika, Hakika, Ina ce maku, Ni ne kofar tumaki.
8 omnes quotquot venerunt fures sunt et latrones sed non audierunt eos oves
Dukan wadanda suka zo kamin ni barayi ne da yan fashi, amma tumakin ba su ji su ba.
9 ego sum ostium per me si quis introierit salvabitur et ingredietur et egredietur et pascua inveniet
Ni ne kofa, In kowa ya shiga ta wurina, zai sami ceto, zai shiga ya fita ya kuma sami wurin kiwo.
10 fur non venit nisi ut furetur et mactet et perdat ego veni ut vitam habeant et abundantius habeant
Barawo ba ya zuwa sai don ya yi sata, ya kashe, ya kuma hallakar. Na zo ne domin su sami rai su kuma same shi a yalwace.
11 ego sum pastor bonus bonus pastor animam suam dat pro ovibus
Ni ne makiyayi mai kyau. Makiyayi mai kyau yana bada ransa domin tumakinsa.
12 mercennarius et qui non est pastor cuius non sunt oves propriae videt lupum venientem et dimittit oves et fugit et lupus rapit et dispergit oves
Wanda yake dan sako kuma, ba makiyayi ba, wanda ba shine mai tumakin ba, in ya ga kyarkeci na zuwa sai ya saki tumakin ya gudu. Sai kyarkecin ya dauke su ya kuma warwatsa su.
13 mercennarius autem fugit quia mercennarius est et non pertinet ad eum de ovibus
Ya gudu domin shi mai aikin kudi ne kuma bai damu da tumakin ba.
14 ego sum pastor bonus et cognosco meas et cognoscunt me meae
Nine makiyayi mai kyau, na kuma san nawa, nawa kuma sun san ni.
15 sicut novit me Pater et ego agnosco Patrem et animam meam pono pro ovibus
Uban ya san ni, ni ma na san Uban, na kuma bada raina domin tumakin.
16 et alias oves habeo quae non sunt ex hoc ovili et illas oportet me adducere et vocem meam audient et fiet unum ovile unus pastor
Ina da wadansu tumaki wadanda ba na wannan garken ba. Wadannan, kuma, dole in kawo su, su ma za su ji muryata saboda za su zama garke daya da makiyayi daya.
17 propterea me Pater diligit quia ego pono animam meam ut iterum sumam eam
Domin wannan ne Uban yake kauna ta: Na bada raina domin in same shi kuma.
18 nemo tollit eam a me sed ego pono eam a me ipso potestatem habeo ponendi eam et potestatem habeo iterum sumendi eam hoc mandatum accepi a Patre meo
Babu wanda zai dauke shi daga wurina, amma ina bayar da shi da kaina. Ina da ikon bada shi, ina da iko in dauke shi kuma. Na karbi wannan umarnin daga wurin Ubana.”
19 dissensio iterum facta est inter Iudaeos propter sermones hos
Tsattsaguwa ta sake tashi tsakanin Yahudawa domin wadannan kalmomin.
20 dicebant autem multi ex ipsis daemonium habet et insanit quid eum auditis
Dayawa a cikinsu suka ce, yana da aljani, kuma mahaukaci ne. Don me ku ke sauraronsa?”
21 alii dicebant haec verba non sunt daemonium habentis numquid daemonium potest caecorum oculos aperire
Wadansu suka ce, wadannan ba kalmomin wanda yake da aljani ba ne. Ko mai aljani zai iya bude idanun makaho?”
22 facta sunt autem encenia in Hierosolymis et hiemps erat
Sai lokacin idin Tsarkakewa a Urushalima ya zo.
23 et ambulabat Iesus in templo in porticu Salomonis
A lokacin damuna ne, Yesu kuwa yana tafiya a shirayi cikin haikalin Sulaimanu.
24 circumdederunt ergo eum Iudaei et dicebant ei quousque animam nostram tollis si tu es Christus dic nobis palam
Sai Yahudawa suka zagaye shi suka ce masa, “Har yaushe ne za ka bar mu cikin shakka? In kai ne Almasihun, ka gaya mana dalla-dalla.”
25 respondit eis Iesus loquor vobis et non creditis opera quae ego facio in nomine Patris mei haec testimonium perhibent de me
Yesu ya ce masu, “Na gaya maku, amma baku gaskata ba. Ayyukan da nake yi a cikin sunan Ubana, su ke yin shaida a kaina.
26 sed vos non creditis quia non estis ex ovibus meis
Duk da haka baku gaskata ba domin ku ba tumakina ba ne.
27 oves meae vocem meam audiunt et ego cognosco eas et sequuntur me
Tumakina suna jin murya ta; Na san su, suna kuma bi na.
28 et ego vitam aeternam do eis et non peribunt in aeternum et non rapiet eas quisquam de manu mea (aiōn , aiōnios )
Ina ba su rai na har abada; ba za su taba mutuwa ba, babu wanda zai kwace su daga hannu na. (aiōn , aiōnios )
29 Pater meus quod dedit mihi maius omnibus est et nemo potest rapere de manu Patris mei
Ubana, wanda ya bani su, ya fi kowa girma, kuma ba mai iya kwace su daga hannun Uban.
30 ego et Pater unum sumus
Ni da Uban daya ne.”
31 sustulerunt lapides Iudaei ut lapidarent eum
Sai Yahudawa suka dauki duwatsu kuma domin su jajjefe shi.
32 respondit eis Iesus multa opera bona ostendi vobis ex Patre meo propter quod eorum opus me lapidatis
Yesu ya amsa masu, “Na nuna maku kyawawan ayyuka masu yawa daga wurin Uban. Saboda wane daga cikin wadannan ayyukan kuke jefe ni?”
33 responderunt ei Iudaei de bono opere non lapidamus te sed de blasphemia et quia tu homo cum sis facis te ipsum Deum
Sai Yahudawa suka amsa masa, “ba don wani aiki mai kyau muke son mu jefe ka ba, amma don sabo, domin kai, mutum ne, amma kana mayar da kanka Allah.”
34 respondit eis Iesus nonne scriptum est in lege vestra quia ego dixi dii estis
Yesu ya amsa masu, “Ba a rubuce yake a shari'arku ba, 'Na ce, “ku alloli ne”'?”
35 si illos dixit deos ad quos sermo Dei factus est et non potest solvi scriptura
In ya kira su alloli, su wadanda maganar Allah ta zo gare su (kuma ba za a iya karya nassi ba),
36 quem Pater sanctificavit et misit in mundum vos dicitis quia blasphemas quia dixi Filius Dei sum
kuna gaya wa wanda Uban ya kebe ya kuma aiko cikin duniya, 'Kana sabo', domin Na ce, 'Ni dan Allah ne'?
37 si non facio opera Patris mei nolite credere mihi
In ba na aikin Ubana, kada ku gaskata ni.
38 si autem facio et si mihi non vultis credere operibus credite ut cognoscatis et credatis quia in me est Pater et ego in Patre
Amma, idan ina yin su, ko ba ku gaskata da ni ba, ku gaskata da ayyukan saboda ku sani, ku kuma gane cewa Uban yana ciki na, ni kuma ina cikin Uban.”
39 quaerebant ergo eum prendere et exivit de manibus eorum
Suka sake kokarin kama shi, amma ya yi tafiyarsa, ya fita daga hannunsu.
40 et abiit iterum trans Iordanen in eum locum ubi erat Iohannes baptizans primum et mansit illic
Ya yi tafiyarsa kuma har gaba da kogin Urdun zuwa inda Yahaya ke yin baftisma ada, ya kuma zauna a wurin.
41 et multi venerunt ad eum et dicebant quia Iohannes quidem signum fecit nullum
Mutane masu yawa suka zo wurinsa, suka ce,”Hakika Yahaya bai yi wasu alamu ba, amma dukan abubuwan da Yahaya ya ce game da wannan mutum gaskiya ne.”
42 omnia autem quaecumque dixit Iohannes de hoc vera erant et multi crediderunt in eum
Mutane dayawa suka bada gaskiya gare shi a wurin.