< Jeremiæ 34 >
1 verbum quod factum est ad Hieremiam a Domino quando Nabuchodonosor rex Babylonis et omnis exercitus eius universaque regna terrae quae erant sub potestate manus eius et omnes populi bellabant contra Hierusalem et contra omnes urbes eius dicens
Yayinda Nebukadnezzar sarkin Babilon da dukan sojojinsa da kuma dukan mulkokinsa da mutanen masarautar da yake mulki suna yaƙi da Urushalima da dukan garuruwan da suke kewaye, sai wannan magana ta zo wa Irmiya daga wurin Ubangiji cewa,
2 haec dicit Dominus Deus Israhel vade et loquere ad Sedeciam regem Iuda et dices ad eum haec dicit Dominus ecce ego tradam civitatem hanc in manu regis Babylonis et succendet eam igni
“Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana cewa ka tafi wurin Zedekiya sarkin Yahuda ka faɗa masa, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, ina gab da ba da wannan birni ga sarkin Babilon, zai kuwa ƙone ta.
3 et tu non effugies de manu eius sed conprehensione capieris et in manu eius traderis et oculi tui oculos regis Babylonis videbunt et os eius cum ore tuo loquetur et Babylonem introibis
Ba za ka tsere daga hannunsa ba amma tabbatacce za a kama ka a kuma ba da kai gare shi. Za ka ga sarkin Babilon da idanunka, zai kuwa yi magana da kai fuska da fuska. Za ka kuwa tafi Babilon.
4 attamen audi verbum Domini Sedecia rex Iuda haec dicit Dominus ad te non morieris in gladio
“‘Duk da haka ka ji alkawarin Ubangiji, ya Zedekiya sarkin Yahuda. Ga abin da Ubangiji yake cewa game da kai. Ba za ka mutu ta takobi ba;
5 sed in pace morieris et secundum conbustiones patrum tuorum regum priorum qui fuerunt ante te sic conburent te et vae domine plangent te quia verbum ego locutus sum dicit Dominus
za ka mutu cikin salama. Yadda mutane suka ƙuna wutar jana’iza don girmama kakanninka, sarakunan da suka riga ka, haka za su ƙuna wuta don girmama da kuma makokinka suna cewa, “Kaito, ya maigida!” Ni kaina na yi wannan alkawari, in ji Ubangiji.’”
6 et locutus est Hieremias propheta ad Sedeciam regem Iuda universa verba haec in Hierusalem
Sa’an nan annabi Irmiya ya faɗi dukan wannan wa Zedekiya sarkin Yahuda, a Urushalima,
7 et exercitus regis Babylonis pugnabat contra Hierusalem et contra omnes civitates Iuda quae reliquae erant contra Lachis et contra Azeca haec enim supererant de civitatibus Iuda urbes munitae
yayinda sojojin sarkin Babilon suna yaƙi da Urushalima da sauran garuruwan Yahuda waɗanda suka ragu, Lakish da Azeka. Waɗannan su ne birane masu katanga kaɗai a Yahuda.
8 verbum quod factum est ad Hieremiam a Domino postquam percussit rex Sedecias foedus cum omni populo in Hierusalem praedicans
Maganar ta zo wa Irmiya daga Ubangiji bayan Sarki Zedekiya ya yi yarjejjeniya da duka mutane a Urushalima ya yi shelar’yanci wa bayi.
9 ut dimitteret unusquisque servum suum et unusquisque ancillam suam hebraeum et hebraeam liberos et nequaquam dominarentur eis id est in Iudaeo et fratre suo
Kowa ya’yantar da bayinsa da suke Ibraniyawa, maza da mata; kada kowa ya riƙe bawa wanda yake mutumin Yahuda.
10 audierunt ergo omnes principes et universus populus qui inierant pactum ut dimitteret unusquisque servum suum et unusquisque ancillam suam liberos et ultra non dominarentur in eis audierunt igitur et dimiserunt
Saboda haka dukan fadawa da mutane suka yi yarjejjeniyar cewa za su’yantar da bayinsu maza da mata ba za su kuwa ƙara riƙe su bayi ba. Suka yarda, suka kuma sake su.
11 et conversi sunt deinceps et retraxerunt servos et ancillas suas quos dimiserant liberos et subiugaverunt in famulos et in famulas
Amma daga baya suka canja ra’ayoyinsu suka maido bayinsu suka kuma sāke bautar da su.
12 et factum est verbum Domini ad Hieremiam a Domino dicens
Sai maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya cewa,
13 haec dicit Dominus Deus Israhel ego percussi foedus cum patribus vestris in die qua eduxi eos de terra Aegypti de domo servitutis dicens
“Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana cewa na yi alkawari da kakanni-kakanninku sa’ad da na fitar da su daga Masar, daga ƙasar bauta. Na ce,
14 cum conpleti fuerint septem anni dimittat unusquisque fratrem suum hebraeum qui venditus est ei et serviet tibi sex annis et dimittes eum a te liberum et non audierunt patres vestri me nec inclinaverunt aurem suam
‘A kowace shekara ta bakwai dole kowannenku yă’yantar da duk wani ɗan’uwa mutumin Ibraniyawa wanda aka sayar masa. Bayan ya yi muku hidima shekaru shida, dole ku bar shi yă tafi’yantacce.’ Amma kakanninku ba su saurare ni ba, ba su ji ni ba.
15 et conversi estis vos hodie et fecistis quod rectum est in oculis meis ut praedicaretis libertatem unusquisque ad amicum suum et inistis pactum in conspectu meo in domo in qua invocatum est nomen meum super eam
Bai daɗe ba da kuka tuba, kuka kuma yi abin da yake mai kyau a idona. Kowannenku ya yi shelar’yanci ga ɗan’uwansa. Kun ma yi yarjejjeniya a gabana a gidan da ake kira da Sunana.
16 et reversi estis et commaculastis nomen meum et reduxistis unusquisque servum suum et unusquisque ancillam suam quos dimiseratis ut essent liberi et suae potestatis et subiugastis eos ut sint vobis servi et ancillae
Amma yanzu kun juya kun kuma ɓata sunana; kowannenku ya mayar da bayi maza da matan da kuka’yantar su tafi inda suka ga dama. Kun sāke tilasta su su zama bayinku.
17 propterea haec dicit Dominus vos non audistis me ut praedicaretis libertatem unusquisque fratri suo et unusquisque amico suo ecce ego praedico libertatem ait Dominus ad gladium et pestem et famem et dabo vos in commotionem cunctis regnis terrae
“Saboda haka, ga abin da Ubangiji yana cewa, kun yi mini rashin biyayya; ba ku yi shelar’yanci don’yan’uwanku ba. Saboda haka yanzu na yi muku shelar’yanci in ji Ubangiji,’yanci ga mutuwa ta takobi, annoba da kuma yunwa. Zan sa ku zama abin ƙyama ga sauran mulkokin duniya.
18 et dabo viros qui praevaricantur foedus meum et non observaverunt verba foederis quibus adsensi sunt in conspectu meo vitulum quem ceciderunt in duas partes et transierunt inter divisiones eius
Mutanen da suka keta alkawarina da ba su cika sharuɗan alkawarin da suka yi a gabana ba, zan yi da su kamar ɗan maraƙin da suka yanka biyu suka bi ta tsakiyarsa.
19 principes Iuda et principes Hierusalem eunuchi et sacerdotes et omnis populus terrae qui transierunt inter divisiones vituli
Shugabannin Yahuda da Urushalima, fadawa, firistoci da kuma dukan mutanen ƙasar waɗanda suka bi tsakanin ɗan maraƙin da aka yanka,
20 et dabo eos in manu inimicorum suorum et in manu quaerentium animam eorum et erit morticinum eorum in escam volucribus caeli et bestiis terrae
zan ba da su ga abokan gābansu waɗanda suke neman ransu. Gawawwakinsu za su zama abincin tsuntsayen sararin sama da na namun jeji.
21 et Sedeciam regem Iuda et principes eius dabo in manu inimicorum suorum et in manu quaerentium animam eorum et in manu exercituum regis Babylonis qui recesserunt a vobis
“Zan ba da Zedekiya sarkin Yahuda da fadawansa ga abokan gābansu waɗanda suke neman ransu, ga sojojin sarkin Babilon, waɗanda suke janye daga gare ku.
22 ecce ego praecipio dicit Dominus et reducam eos in civitatem hanc et proeliabuntur adversum eam et capient eam et incendent igni et civitates Iuda dabo in solitudinem eo quod non sit habitator
Zan yi umarni, in ji Ubangiji, zan kuma komo da su wannan birni. Za su kuwa yi yaƙi da ita, su ƙwace ta su kuma ƙone ta. Zan kuma mai da garuruwan Yahuda kufai don kada wani ya zauna a can.”