< Isaiæ 39 >
1 in tempore illo misit Marodach Baladan filius Baladan rex Babylonis libros et munera ad Ezechiam audierat enim quod aegrotasset et convaluisset
A wannan lokaci Merodak-Baladan ɗan Baladan sarkin Babilon ya aika wa Hezekiya wasiƙu da kuma kyauta, domin ya ji rashin lafiyarsa da kuma warkarwarsa.
2 laetatus est autem super eis Ezechias et ostendit eis cellam aromatum et argenti et auri et odoramentorum et unguenti optimi et omnes apothecas supellectilis suae et universa quae inventa sunt in thesauris eius non fuit verbum quod non ostenderet eis Ezechias in domo sua et in omni potestate sua
Hezekiya ya marabci jakadun da murna ya kuma nuna musu abin da gidajen ajiyarsa sun ƙunsa, azurfa, zinariya, yaji, tatsatsen mai, dukan kayan yaƙinsa da kuma kome da yake a ma’ajinsa. Babu abin da yake a cikin fadansa ko cikin dukan masarautarsa da Hezekiya bai nuna musu ba.
3 introiit autem Isaias propheta ad regem Ezechiam et dixit ei quid dixerunt viri isti et unde venerunt ad te et dixit Ezechias de terra longinqua venerunt ad me de Babylone
Sai Ishaya annabi ya tafi wurin Sarki Hezekiya ya kuma tambaye shi ya ce, “Mene ne waɗannan mutane suka faɗa, kuma daga ina suka fito?” Hezekiya ya amsa ya ce, “Daga ƙasa mai nisa. Sun zo ne daga Babilon.”
4 et dixit quid viderunt in domo tua et dixit Ezechias omnia quae in domo mea sunt viderunt non fuit res quam non ostenderim eis in thesauris meis
Annabi ya yi tambaya ya ce, “Mene ne suka gani a fadanka?” Hezekiya ya ce, “Sun ga kome da kome a fadana. Babu abin da ban nuna musu a cikin ma’ajina ba.”
5 et dixit Isaias ad Ezechiam audi verbum Domini exercituum
Sai Ishaya ya ce wa Hezekiya, “Ka ji maganar Ubangiji Maɗaukaki.
6 ecce dies venient et auferentur omnia quae in domo tua sunt et quae thesaurizaverunt patres tui usque ad diem hanc in Babylonem non relinquetur quicquam dicit Dominus
Tabbatacce lokaci yana zuwa sa’ad da kome da yake cikin fadanka, da kuma dukan abin da kakanninka suka ajiye har yă zuwa yau, za a kwashe zuwa Babilon babu abin da za a bari, in ji Ubangiji.
7 et de filiis tuis qui exibunt de te quos genueris tollent et erunt eunuchi in palatio regis Babylonis
Waɗansu cikin zuriyarka, nama da jininka waɗanda za a haifa maka, za a kwashe su a tafi, za su zama bābānni a fadan sarkin Babilon.”
8 et dixit Ezechias ad Isaiam bonum verbum Domini quod locutus est et dixit fiat tantum pax et veritas in diebus meis
Hezekiya ya ce, “Maganar Ubangiji da ka yi tana da kyau.” Gama ya yi tunani a ransa cewa, “Salama da kāriya za su kasance a zamanina.”