< Esdræ 7 >

1 post haec autem verba in regno Artarxersis regis Persarum Ezras filius Saraiae filii Azariae filii Helciae
Bayan waɗannan abubuwa, a zamanin Artazerzes sarkin Farisa, sai Ezra ɗan Serahiya, ɗan Azariya, ɗan Hilkiya,
2 filii Sellum filii Sadoc filii Achitob
ɗan Shallum, ɗan Zadok, ɗan Ahitub,
3 filii Amariae filii Azariae filii Maraioth
ɗan Amariya, ɗan Azariya, ɗan Merahiyot,
4 filii Zaraiae filii Ozi filii Bocci
ɗan Zerahiya, ɗan Uzzi, ɗan Bukki,
5 filii Abisue filii Finees filii Eleazar filii Aaron sacerdotis ab initio
ɗan Abishuwa, ɗan Finehas, ɗan Eleyazar, ɗan Haruna babban firist.
6 ipse Ezras ascendit de Babylone et ipse scriba velox in lege Mosi quam dedit Dominus Deus Israhel et dedit ei rex secundum manum Domini Dei eius super eum omnem petitionem eius
Shi Ezra ɗin ya zo daga Babilon. Shi malami ne ya kuma san Dokar Musa sosai wadda Ubangiji, Allah na Isra’ila ya bayar. Sarki ya ba shi duk abin da ya roƙa, gama Ubangiji Allahnsa yana tare da shi.
7 et ascenderunt de filiis Israhel et de filiis sacerdotum et de filiis Levitarum et de cantoribus et de ianitoribus et de Nathinneis in Hierusalem anno septimo Artarxersis regis
Waɗansu Isra’ilawa, haɗe da firistoci, da Lawiyawa, da mawaƙa, da masu tsaron ƙofofi, da masu aiki a haikali su ma suka zo Urushalima a shekara ta bakwai a zamanin mulkin sarki Artazerzes.
8 et venerunt in Hierusalem mense quinto ipse est annus septimus regis
Ezra ya iso Urushalima a wata na biyar na shekara ta bakwai na kama mulkin sarkin.
9 quia in primo die mensis primi coepit ascendere de Babylone et in primo mensis quinti venit in Hierusalem iuxta manum Dei sui bonam super se
Ya fara tafiyarsa daga Babilon a rana ta farko ga watan farko, ya kuma iso Urushalima a rana ta farko ga watan biyar, gama alherin Allahnsa yana tare da shi.
10 Ezras enim paravit cor suum ut investigaret legem Domini et faceret et doceret in Israhel praeceptum et iudicium
Gama Ezra ya miƙa kansa ga bincike da kuma kiyaye Dokar Ubangiji, da kuma koya wa Isra’ilawa dokoki da kuma umarnan Ubangiji.
11 hoc est autem exemplar epistulae edicti quod dedit rex Artarxersis Ezrae sacerdoti scribae erudito in sermonibus et praeceptis Domini et caerimoniis eius in Israhel
Ga wasiƙar da sarki Artazerzes ya ba Ezra wanda yake firist da kuma malami, mutumin da yake cike da sani game da dokoki da kuma umarnan Ubangiji wa Isra’ila.
12 Artarxersis rex regum Ezrae sacerdoti scribae legis Dei caeli doctissimo salutem
Artazerzes, sarkin sarakuna. Zuwa ga Ezra firist, malamin Dokar Allah na sama. Gaisuwa.
13 a me decretum est ut cuicumque placuerit in regno meo de populo Israhel et de sacerdotibus eius et de Levitis ire in Hierusalem tecum vadat
Yanzu ina ba da umarni cewa duk wani mutumin Isra’ilan da yake cikin mulkina, haɗe da firistoci, da Lawiyawa, da suke so su tafi tare da kai zuwa Urushalima za su iya tafiya.
14 a facie enim regis et septem consiliatorum eius missus es ut visites Iudaeam et Hierusalem in lege Dei tui quae est in manu tua
Sarki ne da mashawartansa guda bakwai suka aike ka don ka je ka ga halin da Yahuda da Urushalima suke ciki game da dokokin Allahnka, waɗanda suke a hannunka.
15 et ut feras argentum et aurum quod rex et consiliatores eius sponte obtulerunt Deo Israhel cuius in Hierusalem tabernaculum est
Za ka kuma tafi da zinariya da azurfa waɗanda sarki da mashawartansa suka ba da kyautar yardar rai ga Allah na Isra’ila, wanda haikalinsa ke a Urushalima,
16 et omne argentum et aurum quodcumque inveneris in universa provincia Babylonis et populus offerre voluerit et de sacerdotibus qui sponte obtulerint domui Dei sui quae est in Hierusalem
haɗe da duk zinariya da azurfan da za ka iya samu a Babilon, da kuma duk bayarwar yardar rai daga mutane da firistoci, domin haikalin Allahnsu da yake a Urushalima.
17 libere accipe et studiose eme de hac pecunia vitulos arietes agnos et sacrificia et libamina eorum et offer ea super altare templi Dei vestri quod est in Hierusalem
Ka tabbata ka yi amfani da kuɗin nan don ka sayi bijimai, da raguna, da’yan raguna, da hadayu na gari, da na sha, ka kuma miƙa su a kan bagade na haikalin Allahnka a Urushalima.
18 sed et si quid tibi et fratribus tuis placuerit de reliquo argento et auro ut faciatis iuxta voluntatem Dei vestri facite
Sa’an nan kai da’yan’uwanka Yahudawa ku yi abin da kuka ga ya fi kyau da sauran zinariya da azurfa ɗin bisa ga nufin Allah.
19 vasa quoque quae dantur tibi in ministerium domus Dei tui trade in conspectu Dei Hierusalem
Ka kai wa Allah na Urushalima duk kayan da aka ba ka amanarsu don yin sujada a haikalin Allahnka.
20 sed et cetera quibus opus fuerit in domo Dei tui quantumcumque necesse est ut expendas dabis de thesauro et de fisco regis
Duk kuma wani abin da ake bukata domin haikalin Allahnka, daga ɗakunan ajiya sarki za ka fitar da kuɗin.
21 et a me ego Artarxersis rex statui atque decrevi omnibus custodibus arcae publicae qui sunt trans Flumen ut quodcumque petierit a vobis Ezras sacerdos scriba legis Dei caeli absque mora detis
Yanzu fa ni, Sarki Artazerzes, ina ba da umarni ga kowane ma’aji na Kewayen Kogin Yuferites su tanada duk abin da Ezra firist, wanda kuma yake malamin Dokar Allah na sama zai bukaci,
22 usque ad argenti talenta centum et usque ad frumenti choros centum et usque ad vini batos centum et usque ad batos olei centum sal vero absque mensura
har zuwa talenti ɗari na azurfa, da mudu ɗari na alkama, da garwa ɗari na ruwan inabi, da garwa ɗari na man zaitun, da kuma gishiri ba iyaka.
23 omne quod ad ritum Dei caeli pertinet tribuatur diligenter in domo Dei caeli ne forte irascatur contra regnum regis et filiorum eius
A yi duk abin da Allah na sama ya ce don haikalin Allah na sama, sai a yi shi da himma. Me zai sa a jawo wa sarki da’ya’yansa fushin Allah?
24 vobisque notum facimus de universis sacerdotibus et Levitis cantoribus ianitoribus Nathinneis et ministris domus Dei huius ut vectigal et tributum et annonas non habeatis potestatem inponendi super eos
Ku kuma san cewa, ba ku da ikon sa firistoci, da Lawiyawa, da mawaƙa, da masu tsaron ƙofofin haikali, da masu aiki a gidan Allah, ko waɗansu masu aiki a haikali su biya haraji, ko kuɗin shiga.
25 tu autem Ezras secundum sapientiam Dei tui quae est in manu tua constitue iudices et praesides ut iudicent omni populo qui est trans Flumen his videlicet qui noverunt legem Dei tui sed et inperitos docete libere
Kai kuma Ezra, bisa ga hikimar da Allah ya ba ka, sai ka zaɓi mahukunta da alƙalai waɗanda za su zama masu yanke hukunci ga dukan mutanen Kewayen Kogin Yuferites, duk waɗanda suka san dokokin Allahnka, ka kuma koya wa duk waɗanda ba su san dokokin ba.
26 et omnis qui non fecerit legem Dei tui et legem regis diligenter iudicium erit de eo sive in mortem sive in exilium sive in condemnationem substantiae eius vel certe in carcerem
Ba shakka duk wanda bai yi biyayya da dokokin Allahnka ba, da kuma dokokin sarki ba dole a yanke masa hukuncin kisa, ko hukuncin kora, ko hukuncin raba shi da mallakarsa, ko kuma hukuncin kulle shi a kurkuku.
27 benedictus Dominus Deus patrum nostrorum qui dedit hoc in corde regis ut glorificaret domum Domini quae est in Hierusalem
Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allah na kakanninmu, ya taɓa zuciyar sarki don yă kawo ɗaukaka ga haikalin Allah a Urushalima ta wannan hanya.
28 et in me inclinavit misericordiam coram rege et consiliatoribus eius et universis principibus regis potentibus et ego confortatus manu Domini Dei mei quae erat in me congregavi de Israhel principes qui ascenderent mecum
Wanda kuma ya sa na sami tagomashi a gaban sarki da mashawartansa, da kuma duk manyan masu muƙami nasa. Gama Ubangiji Allahna yana tare da ni, sai na sami ƙarfin hali na tattara shugabannin mutane daga Isra’ila, don mu tafi tare.

< Esdræ 7 >