< Exodus 5 >

1 post haec ingressi sunt Moses et Aaron et dixerunt Pharaoni haec dicit Dominus Deus Israhel dimitte populum meum ut sacrificet mihi in deserto
Daga bisani sai Musa da Haruna suka tafi wurin Fir’auna suka ce, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Bari mutanena su tafi domin su yi mini biki a hamada.’”
2 at ille respondit quis est Dominus ut audiam vocem eius et dimittam Israhel nescio Dominum et Israhel non dimittam
Fir’auna ya ce, “Wane ne Ubangiji da zan yi biyayya da shi, har in bar Isra’ila su tafi? Ban san Ubangiji ba, kuma ba zan bar Isra’ila su tafi ba.”
3 dixerunt Deus Hebraeorum vocavit nos ut eamus viam trium dierum in solitudinem et sacrificemus Domino Deo nostro ne forte accidat nobis pestis aut gladius
Sai suka ce, “Allah na Ibraniyawa ya sadu da mu. Yanzu bari mu ɗauki tafiyar kwana uku cikin hamada domin mu miƙa hadaya ga Ubangiji Allahnmu, don kada yă buga mu da annoba ko takobi.”
4 ait ad eos rex Aegypti quare Moses et Aaron sollicitatis populum ab operibus suis ite ad onera vestra
Amma sarkin Masar ya ce wa, “Musa da Haruna, don me kuke hana mutane yin aikinsu? Ku koma wurin aikinku!”
5 dixitque Pharao multus est populus terrae videtis quod turba succreverit quanto magis si dederitis eis requiem ab operibus
Sa’an nan Fir’auna ya ce, “Ga shi mutane sun yi yawa a ƙasar Masar, ku kuma yanzu kuna so ku hana su yin aiki.”
6 praecepit ergo in die illo praefectis operum et exactoribus populi dicens
A wannan rana Fir’auna ya ba da wannan umarni wa shugabannin masu gandu,
7 nequaquam ultra dabitis paleas populo ad conficiendos lateres sicut prius sed ipsi vadant et colligant stipulam
“Kada ku ƙara ba wa mutanen ciyawar tattaka domin su yi tubula, bari su tafi su tattara tattaka da kansu.
8 et mensuram laterum quos prius faciebant inponetis super eos nec minuetis quicquam vacant enim et idcirco vociferantur dicentes eamus et sacrificemus Deo nostro
Ku kuma bukace su su yi tubula daidai yawan tubalin da suka saba yi, kada ku rage. Ragwaye ne, shi ya sa suke kuka cewa, ‘Bari mu tafi mu yi hadaya ga Allahnmu.’
9 opprimantur operibus et expleant ea ut non adquiescant verbis mendacibus
Ku sa waɗannan mutane su yi aiki mai tsanani sosai, don kada su sami zarafin kasa kunne ga maganganun ƙarya.”
10 igitur egressi praefecti operum et exactores ad populum dixerunt sic dicit Pharao non do vobis paleas
Sai shugabannin masu aikin gandu suka fita suka gaya wa mutanen Isra’ila, “Ga abin da Fir’auna ya ce, ‘Ba zan ƙara ba ku tattaka ba.
11 ite et colligite sicubi invenire potueritis nec minuetur quicquam de opere vestro
Ku tafi ku nemo wa kanku tattaka duk inda za ku samu, amma ba za a rage aikinku ba ko kaɗan.’”
12 dispersusque est populus per omnem terram Aegypti ad colligendas paleas
Saboda haka mutane suka warwatsu ko’ina a Masar domin tattara bunnun da za su yi amfani da su, maimakon tattaka.
13 praefecti quoque operum instabant dicentes conplete opus vestrum cotidie ut prius facere solebatis quando dabantur vobis paleae
Shugabannin gandu suka dinga matsa musu suna cewa, “Ku cika aikin da aka bukace ku na kowace rana kamar yadda kuke yi sa’ad da kuke da tattaka.”
14 flagellatique sunt qui praeerant operibus filiorum Israhel ab exactoribus Pharaonis dicentibus quare non impletis mensuram laterum sicut prius nec heri nec hodie
Manyan Isra’ilawa waɗanda shugabannin gandun Fir’auna suka naɗa, suka sha dūka, aka kuma yi musu tambayoyi ana cewa, “Don me ba ku cika yawan tubula na jiya da na yau kamar yadda kuka saba ba?”
15 veneruntque praepositi filiorum Israhel et vociferati sunt ad Pharaonem dicentes cur ita agis contra servos tuos
Sai manyan Isra’ila masu bi da aikin gandu suka tafi wurin Fir’auna suka yi roƙo suna cewa, “Don me kake yi wa bayinka haka?
16 paleae non dantur nobis et lateres similiter imperantur en famuli tui flagellis caedimur et iniuste agitur contra populum tuum
Ba a ba wa bayinka tattaka, duk da haka ana ce mana, ‘Ku yi tubula!’ Ana wa bayinka dūka, amma fa laifin na mutanenka ne.”
17 qui ait vacatis otio et idcirco dicitis eamus et sacrificemus Domino
Fir’auna ya ce, “Ku ragwaye ne! Shi ya sa kuke cewa, ‘Bari mu tafi mu yi hadaya wa Ubangiji.’
18 ite ergo et operamini paleae non dabuntur vobis et reddetis consuetum numerum laterum
Ku ɓace yanzu daga nan, ku koma wurin aikinku. Ba za a ba ku tattaka ba, kuma dole ku fid da tubula kamar yadda kuka saba.”
19 videbantque se praepositi filiorum Israhel in malo eo quod diceretur eis non minuetur quicquam de lateribus per singulos dies
Manyan Isra’ilawa da suke bi da aikin gandu suka gane cewa sun shiga uku, sa’ad da aka gaya musu, “Ba za ku rage yawan tubulan da aka bukace ku ku yi na kowace rana ba.”
20 occurreruntque Mosi et Aaron qui stabant ex adverso egredientes a Pharaone
Da suka bar Fir’auna, sai suka sadu da Musa da Haruna suna jira su sadu da su,
21 et dixerunt ad eos videat Dominus et iudicet quoniam fetere fecistis odorem nostrum coram Pharao et servis eius et praebuistis ei gladium ut occideret nos
sai suka ce, “Bari Ubangiji yă duba, yă kuma hukunta ku! Kun maishe mu abin ƙyama ga Fir’auna da bayinsa, kuka kuma sa musu takobi a hannunsu don su kashe mu.”
22 reversusque Moses ad Dominum ait Domine cur adflixisti populum istum quare misisti me
Musa ya koma wurin Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji, don me ka kawo wahala a kan mutanen nan? Abin da ya sa ka aiko ni ke nan?
23 ex eo enim quo ingressus sum ad Pharaonem ut loquerer nomine tuo adflixit populum tuum et non liberasti eos
Gama tun da na tafi wurin Fir’auna, na yi masa magana da sunanka, sai ya fara gasa wa mutanen nan azaba, ba ka kuma ceci mutanenka.”

< Exodus 5 >