< Exodus 29 >

1 sed et hoc facies ut mihi in sacerdotio consecrentur tolle vitulum de armento et arietes duos inmaculatos
“Ga abin da za ka yi don ka keɓe su, don su yi mini hidima a matsayin firistoci. Ka ɗauki ɗan bijimi da raguna biyu marasa lahani.
2 panesque azymos et crustula absque fermento quae conspersa sint oleo lagana quoque azyma oleo lita de simila triticea cuncta facies
Daga garin alkama mai laushi marar yisti kuwa, ka yi burodi, da wainan da aka kwaɓa da mai, da ƙosai waɗanda an barbaɗa mai a kai.
3 et posita in canistro offeres vitulum autem et duos arietes
Ka sa waɗannan a cikin kwando. Sa’an nan ka miƙa su tare da ɗan bijimin da ragunan nan biyu.
4 et Aaron ac filios eius adplicabis ad ostium tabernaculi testimonii cumque laveris patrem cum filiis aqua
Bayan haka sai ka kawo Haruna da’ya’yansa a ƙofar Tentin Sujada ka yi musu wanka.
5 indues Aaron vestimentis suis id est linea et tunica et superumerali et rationali quod constringes balteo
Ka ɗauki rigar ka sa wa Haruna, ka sa masa doguwar rigar, da rigar efod, da efod kanta, da ƙyallen maƙalawa a ƙirji. Ka ɗaura masa efod da ɗamarar da aka yi mata ado.
6 et pones tiaram in capite eius et lamminam sanctam super tiaram
Ka naɗa masa rawani a kai, ka kuma sa kambi mai tsarki a bisa rawanin.
7 et oleum unctionis fundes super caput eius atque hoc ritu consecrabitur
Ka ɗauki man shafewa ka shafe shi, ta wurin zuba man a kansa.
8 filios quoque illius adplicabis et indues tunicis lineis cingesque balteo
Ka kawo’ya’yansa, ka sa musu taguwoyi,
9 Aaron scilicet et liberos eius et inpones eis mitras eruntque sacerdotes mei in religione perpetua postquam initiaveris manus eorum
ka kuma sa musu huluna a kansu. Sa’an nan ka ɗaura wa Haruna da’ya’yansa abin ɗamara. Su kuwa da zuriyarsu, aikin firist kuwa zai zama nasu ta wurin dawwammamiyar farilla. “Ta haka za ka keɓe Haruna da’ya’yansa maza.
10 adplicabis et vitulum coram tabernaculo testimonii inponentque Aaron et filii eius manus super caput illius
“Ka kuma kawo bijimin a gaban Tentin Sujada, sai Haruna da’ya’yansa su ɗora hannuwansu a kansa.
11 et mactabis eum in conspectu Domini iuxta ostium tabernaculi testimonii
Ka yanka shi a gaban Ubangiji a ƙofar Tentin Sujada.
12 sumptumque de sanguine vituli pones super cornua altaris digito tuo reliquum autem sanguinem fundes iuxta basim eius
Ka ɗibi jinin bijimin ka zuba a kan ƙahoni na bagade da yatsanka, sauran jinin kuwa ka zuba a gindin bagaden.
13 sumes et adipem totum qui operit intestina et reticulum iecoris ac duos renes et adipem qui super eos est et offeres incensum super altare
Sa’an nan ka ɗauki dukan kitsen da ya rufe kayan ciki, da kitsen da yake manne da hanta, da ƙoda biyu da kuma kintsen da yake a kansu, ka ƙone su a kan bagade.
14 carnes vero vituli et corium et fimum conbures foris extra castra eo quod pro peccato sit
Amma ka ƙone naman bijimin, da fatarsa, da kayan cikin, a bayan sansani. Hadaya ce ta zunubi.
15 unum quoque arietum sumes super cuius caput ponent Aaron et filii eius manus
“Ka ɗauki ɗaya daga cikin ragunan, Haruna kuwa da’ya’yan maza za su ɗora hannuwansa a kansa.
16 quem cum mactaveris tolles de sanguine eius et fundes circa altare
Ka yanka ragon, ka ɗibi jinin, ka yayyafa shi kewaye da gefen bagaden.
17 ipsum autem arietem secabis in frusta lotaque intestina eius ac pedes pones super concisas carnes et super caput illius
Ka yayyanka rago gunduwa-gunduwa, ka wanke kayan cikin, da ƙafafun, da kan, ka haɗa su da gunduwoyin.
18 et offeres totum arietem in incensum super altare oblatio est Domini odor suavissimus victimae Dei
Sa’an nan ka ƙone ragon ɗungum a kan bagade. Hadaya ta ƙonawa ce ga Ubangiji, mai daɗin ƙanshi, wato, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.
19 tolles quoque arietem alterum super cuius caput Aaron et filii eius ponent manus
“Ka ɗauki ɗayan ragon, sai Haruna da’ya’yansa maza su ɗora hannuwansu a kansa.
20 quem cum immolaveris sumes de sanguine ipsius et pones super extremum dextrae auriculae Aaron et filiorum eius et super pollices manus eorum et pedis dextri fundesque sanguinem super altare per circuitum
Ka yanka ragon, ka ɗibi jinin, ka shafa a bisa leɓen kunnen Haruna na dama, da bisa leɓen kunnuwan’ya’yansa maza na dama, da kan manyan yatsotsin hannuwansu na dama, da kuma a kan manyan yatsotsin ƙafafunsu na dama. Sauran jinin kuwa, sai ka yayyafa shi kewaye da gefen bagaden.
21 cumque tuleris de sanguine qui est super altare et de oleo unctionis asperges Aaron et vestes eius filios et vestimenta eorum consecratisque et ipsis et vestibus
Ka ɗibi jinin da yake a kan bagade, da man shafewa, ka yafa a kan Haruna da rigunansa, da kuma a kan’ya’yansa maza da rigunansu. Sa’an nan shi da’ya’yansa maza da rigunansu za su tsarkake.
22 tolles adipem de ariete et caudam et arvinam quae operit vitalia ac reticulum iecoris et duos renes atque adipem qui super eos est armumque dextrum eo quod sit aries consecrationum
“Ka ɗebi kitse daga wannan rago, ka yanke wutsiyarsa mai kitse, ka kuma ɗebi kitsen da ya rufe kayan ciki, da kitsen da yake bisa hanta, da ƙoda biyu da kitsen da yake kansu, da cinyar dama. (Gama rago ne don naɗi.)
23 tortam panis unius crustulum conspersum oleo laganum de canistro azymorum quod positum est in conspectu Domini
Daga kwandon burodi marar yisti, wanda yake gaban Ubangiji, ka ɗauki dunƙule ɗaya, da waina da aka yi da mai, da kuma ƙosai.
24 ponesque omnia super manus Aaron et filiorum eius et sanctificabis eos elevans coram Domino
Ka sa dukan waɗannan a hannun Haruna da’ya’yansa maza, su kaɗa su a gaban Ubangiji a matsayin hadaya ta kaɗawa.
25 suscipiesque universa de manibus eorum et incendes super altare in holocaustum odorem suavissimum in conspectu Domini quia oblatio eius est
Sa’an nan ka karɓe su daga hannuwansu, ka ƙone su a kan bagade tare da hadaya ta ƙonawa, domin ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji, wato, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.
26 sumes quoque pectusculum de ariete quo initiatus est Aaron sanctificabisque illud elatum coram Domino et cedet in partem tuam
Bayan haka, ka ɗauki ƙirjin ragon domin naɗin Haruna, ka kaɗa shi a gaban Ubangiji kamar hadaya ta kaɗawa. Wannan ƙirji zai zama rabonka.
27 sanctificabis et pectusculum consecratum et armum quem de ariete separasti
“Ka tsarkake ƙirji na hadaya ta kaɗawa, da cinya ta hadaya ta ɗagawa, waɗanda za a kaɗa a kuma ɗaga na ragon naɗin, wanda yake na Haruna da kuma na’ya’yansa maza.
28 quo initiatus est Aaron et filii eius cedentque in partem Aaron et filiorum eius iure perpetuo a filiis Israhel quia primitiva sunt et initia de victimis eorum pacificis quae offerunt Domino
Wannan zai zama rabon Haruna da’ya’yansa maza daga Isra’ilawa. Gama wannan hadaya ta ɗagawa ce daga cikin hadayu na salama da Isra’ilawa za su miƙa wa Ubangiji.
29 vestem autem sanctam qua utitur Aaron habebunt filii eius post eum ut unguantur in ea et consecrentur manus eorum
“Keɓaɓɓun tufafin nan na Haruna za su zama na zuriyarsa bayan mutuwarsa. Da tufafin nan ne za a zuba musu mai, a keɓe su.
30 septem diebus utetur illa qui pontifex pro eo fuerit constitutus de filiis eius et qui ingredietur tabernaculum testimonii ut ministret in sanctuario
Ɗan da ya gāje shi a matsayin firist, shi ne zai sa su har kwana bakwai, lokacin da ya shiga Tentin Sujada, don yă yi aiki a Wuri Mai Tsarki.
31 arietem autem consecrationum tolles et coques carnes eius in loco sancto
“Ka ɗauki ragon naɗi, ka dafa naman a tsattsarkan wuri.
32 quibus vescetur Aaron et filii eius panes quoque qui sunt in canistro in vestibulo tabernaculi testimonii comedent
A ƙofar Tentin Sujada, Haruna da’ya’yansa maza za su ci wannan rago da burodin da yake cikin kwandon.
33 ut sit placabile sacrificium et sanctificentur offerentium manus alienigena non vescetur ex eis quia sancti sunt
Za su ci abubuwan nan da aka yi kafara da su a lokacin tsarkakewarsu da keɓewarsu. Ba wanda zai ci, sai su kaɗai, gama abubuwan nan tsarkaka ne.
34 quod si remanserit de carnibus consecratis sive de panibus usque mane conbures reliquias igni non comedentur quia sanctificata sunt
In naman ragon naɗi ko wani burodin ya ragu har safiya, a ƙone shi, kada a ci gama tsarkake ne.
35 omnia quae praecepi tibi facies super Aaron et filiis eius septem diebus consecrabis manus eorum
“Ka yi wa Haruna da’ya’yansa maza duk abin da na umarce ka, ka ɗauki kwana bakwai don naɗinsu.
36 et vitulum pro peccato offeres per singulos dies ad expiandum mundabisque altare cum immolaris expiationis hostiam et ungues illud in sanctificationem
Ka miƙa bijimi ɗaya kowace rana domin hadaya don zunubi ta yin kafara. Ka tsarkake bagade ta wuri yin kafara dominsa, ka shafe shi da mai don ka tsarkake shi.
37 septem diebus expiabis altare et sanctificabis et erit sanctum sanctorum omnis qui tetigerit illud sanctificabitur
Kwana bakwai za ka yi kafara saboda bagaden, ka kuma tsarkake shi. Sa’an nan bagaden zai zama mafi tsarki, kuma duk abin da ya taɓa bagaden zai tsarkaka.
38 hoc est quod facies in altari agnos anniculos duos per singulos dies iugiter
“Ga abin da za ka miƙa a bisa bagaden kowace rana.’Yan raguna biyu masu shekara ɗaya-ɗaya.
39 unum agnum mane et alterum vespere
Ka miƙa ɗaya da safe, ɗaya kuma da yamma.
40 decimam partem similae conspersae oleo tunso quod habeat mensuram quartam partem hin et vinum ad libandum eiusdem mensurae in agno uno
Haɗe da ɗan rago na farkon, ka miƙa mudun gari mai laushi wanda an gauraye da kwalaba ɗaya na tataccen mai zaitun, da kwalaba ɗaya na ruwan inabi don hadaya ta sha.
41 alterum vero agnum offeres ad vesperam iuxta ritum matutinae oblationis et iuxta ea quae diximus in odorem suavitatis
Ka miƙa ɗaya ragon da yamma, tare da hadaya ta gari da hadaya ta sha kamar aka yi ta safe, mai daɗin ƙanshi, wato, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.
42 sacrificium Domino oblatione perpetua in generationes vestras ad ostium tabernaculi testimonii coram Domino ubi constituam ut loquar ad te
“Wannan za tă zama hadaya ta ƙonawar da za a dinga yi kowace rana, daga tsara zuwa tsara. Za a yi ta miƙa hadayar a ƙofar Tentin Sujada a gaban Ubangiji. A can zan sadu da kai, in yi magana da kai;
43 ibique praecipiam filiis Israhel et sanctificabitur altare in gloria mea
a can kuma zan sadu da Isra’ilawa, in kuma tsarkake wurin da ɗaukakata.
44 sanctificabo et tabernaculum testimonii cum altari et Aaron cum filiis eius ut sacerdotio fungantur mihi
“Ta haka zan tsarkake Tentin Sujada da bagaden, in kuma tsarkake Haruna da’ya’yansa maza su yi mini hidima a matsayin firistoci.
45 et habitabo in medio filiorum Israhel eroque eis Deus
Sa’an nan zan zauna a cikin Isra’ilawa, in kuma zama Allahnsu.
46 et scient quia ego Dominus Deus eorum qui eduxi eos de terra Aegypti ut manerem inter illos ego Dominus Deus ipsorum
Za su san cewa ni ne Ubangiji Allahnsu, wanda ya fitar da su daga Masar saboda in zauna a cikinsu. Ni ne Ubangiji Allahnsu.

< Exodus 29 >