< Actuum Apostolorum 24 >
1 post quinque autem dies descendit princeps sacerdotum Ananias cum senioribus quibusdam et Tertullo quodam oratore qui adierunt praesidem adversus Paulum
Bayan kwanaki biyar, sai Ananiyas babban firist, Wasu dattawa da wani masanin shari'a mai suna Tartilus, sun tafi can. Suka kai karar Bulus gaban gwamna.
2 et citato Paulo coepit accusare Tertullus dicens cum in multa pace agamus per te et multa corrigantur per tuam providentiam
Lokacin da Bulus ya tsaya gaban gwamna, Tartilus ya fara zarginsa yace wa gwamnan, “Saboda kai mun sami zaman lafiya; sa'annan hangen gabanka ya kawo gyara a kasarmu;
3 semper et ubique suscipimus optime Felix cum omni gratiarum actione
don haka duk abin da ka yi mun karba da godiya, ya mai girma Filikus.
4 ne diutius autem te protraham oro breviter audias nos pro tua clementia
Domin kada in wahalsheka, ina roko a yi mani nasiha don in yi magana kadan.
5 invenimus hunc hominem pestiferum et concitantem seditiones omnibus Iudaeis in universo orbe et auctorem seditionis sectae Nazarenorum
An iske mutumin nan yana barna irir iri, yana kuma zuga jama'ar Yahudawa a dukan duniya su yi tayarwa.
6 qui etiam templum violare conatus est quem et adprehendimus
Har ma ya yi kokarin kazantar da haikali; saboda haka muka kama shi. [Mun so mu shari'anta masa bisa ga dokarmu.]
Amma Lisiyas jami'i ya zo ya kwace shi da karfi daga hannunmu.
8 a quo poteris ipse iudicans de omnibus istis cognoscere de quibus nos accusamus eum
Idan ka binciki Bulus game da wadannan al'amura, kai ma, zai tabbatar maka abin da muke zarginsa a kai.
9 adiecerunt autem et Iudaei dicentes haec ita se habere
Dukan Yahudawa suna zargin Bulus cewa wadannan abubuwa gaskiya ne.
10 respondit autem Paulus annuente sibi praeside dicere ex multis annis esse te iudicem genti huic sciens bono animo pro me satisfaciam
lokacin da gwamnan ya alamta wa Bulus ya yi magana sai yace, “Yanzu na fahimci cewar da dadewa kana mulkin kasarnan, don haka da farin ciki zan yi maka bayani.
11 potes enim cognoscere quia non plus sunt dies mihi quam duodecim ex quo ascendi adorare in Hierusalem
Zaka iya tabbatarwa cewa bai kai kwana sha biyu ba tun da nake zuwa Urushalima don yin sujada.
12 et neque in templo invenerunt me cum aliquo disputantem aut concursum facientem turbae neque in synagogis neque in civitate
Da suka same ni a haikali, ban yi jayayya ko kawo rudami a tsakanin jama'a ba.
13 neque probare possunt tibi de quibus nunc accusant me
Don haka ba su da tabbas akan abinda suke zargina a kansa yau.
14 confiteor autem hoc tibi quod secundum sectam quam dicunt heresim sic deservio patrio Deo meo credens omnibus quae in lege et prophetis scripta sunt
Amma na sanar da kai, bisa ga abin da suke kira darika, haka ni ma nake bautawa Allah na kakanninmu. Na yi aminci wajen kiyaye dukan abin da ke a rubuce a Attaurat da litattafan annabawa.
15 spem habens in Deum quam et hii ipsi expectant resurrectionem futuram iustorum et iniquorum
Ina sa bege ga Allah, kamar yadda za a yi tashin matattu, masu adalci da miyagu;
16 in hoc et ipse studeo sine offendiculo conscientiam habere ad Deum et ad homines semper
a kan haka kuma, nake kokarin zama mara abin zargi a gaban Allah da mutane ina yin haka cikin dukan al'amura.
17 post annos autem plures elemosynas facturus in gentem meam veni et oblationes et vota
Bayan wadansu shekaru na zo in kawo wasu sadakoki da baikon yardar rai.
18 in quibus invenerunt me purificatum in templo non cum turba neque cum tumultu
Cikin kudurin yin haka, sai wasu Yahudawa daga kasar Asiya suka iske ni a cikin ka'idodin tsarkakewa a haikali, ba da taro ko ta da hargitsi ba.
19 quidam autem ex Asia Iudaei quos oportebat apud te praesto esse et accusare si quid haberent adversum me
Yakamata wadannan mutanen su zo gabarka a yau, har idan suna da wani zargi a kai na.
20 aut hii ipsi dicant si quid invenerunt in me iniquitatis cum stem in concilio
In kuwa ba haka ba bari mutanennan su fada in sun taba iske ni da wani aibu a duk lokacin da na gurfana a gaban majalisar Yahudawa;
21 nisi de una hac solummodo voce qua clamavi inter eos stans quoniam de resurrectione mortuorum ego iudicor hodie a vobis
sai dai ko a kan abu daya da na fada da babbar murya sa'adda na tsaya a gabansu, 'Wato batun tashin matattu wanda ake tuhumata ake neman yi mani hukunci yau.'”
22 distulit autem illos Felix certissime sciens de via dicens cum tribunus Lysias descenderit audiam vos
Filikus yana da cikakken sanin tafarkin Hanyar, shi yasa ya daga shari'ar. Yace da su, “Duk sa'anda Lisiyas mai ba da umarni ya zo daga Urushalima, zan yanke hukunci.”
23 iussitque centurioni custodiri eum et habere requiem nec quemquam prohibere de suis ministrare ei
Sa'annan ya umarci jarumin ya lura da Bulus, amma ya yi sassauci, kada ya hana abokansa su ziyarce shi ko su taimake shi.
24 post aliquot autem dies veniens Felix cum Drusilla uxore sua quae erat Iudaea vocavit Paulum et audivit ab eo fidem quae est in Iesum Christum
Bayan wadansu kwanaki, Filikus da mai dakinsa Druskila, ita Bayahudiya ce, ya kuma aika a kira Bulus ya saurare shi game da bangaskiya cikin Kristi Yesu.
25 disputante autem illo de iustitia et castitate et de iudicio futuro timefactus Felix respondit quod nunc adtinet vade tempore autem oportuno accersiam te
Amma sa'adda Bulus yake bayyana zancen adalci, kamunkai, da hukunci mai zuwa, Filikus ya firgita ya ce, “Yanzu ka tafi. Amma idan na sami zarafi an jima, zan sake neman ka.”
26 simul et sperans quia pecunia daretur a Paulo propter quod et frequenter accersiens eum loquebatur cum eo
A wannan lokacin, yasa zuciya Bulus zai bashi kudi, yayi ta nemansa akai-akai domin yayi magana da shi.
27 biennio autem expleto accepit successorem Felix Porcium Festum volens autem gratiam praestare Iudaeis Felix reliquit Paulum vinctum
Bayan shekaru biyu, Borkiyas Festas ya zama gwamna bayan Filikus, domin neman farin jini a wurin Yahudawa, ya ci gaba da tsaron Bulus a gidan yari.