< Ii Samuelis 4 >

1 audivit autem filius Saul quod cecidisset Abner in Hebron et dissolutae sunt manus eius omnisque Israhel perturbatus est
Sa’ad da Ish-Boshet ya ji labari cewa Abner ya mutu a Hebron, sai ya karaya, sai dukan hankalin Isra’ila ya tashi.
2 duo autem viri principes latronum erant filio Saul nomen uni Baana et nomen alteri Rechab filii Remmon Berothitae de filiis Beniamin siquidem et Beroth reputata est in Beniamin
To, ɗan Shawulu yana da’ya’ya maza biyu da suke shugabannin’yan hari. Ana kiran ɗaya Ba’ana, ɗayan kuma Rekab. Su’ya’yan Rimmon mutumin Benyamin ne daga Beyerot, an lissafta Beyerot a ɓangaren Benyamin,
3 et fugerunt Berothitae in Getthaim fueruntque ibi advenae usque in tempus illud
domin mutanen Beyerot sun gudu zuwa Gittayim inda suke zaman baƙunci har wa yau.
4 erat autem Ionathan filio Saul filius debilis pedibus quinquennis enim fuit quando venit nuntius de Saul et Ionathan ex Iezrahel tollens itaque eum nutrix sua fugit cumque festinaret ut fugeret cecidit et claudus effectus est habuitque vocabulum Mifiboseth
(Yonatan ɗan Shawulu yana da ɗa mai suna Mefiboshet wanda yake gurgu a duka ƙafafu. Yana da shekara biyar ne sa’ad da labarin mutuwar Shawulu da Yonatan ya zo daga Yezireyel. Sai mai renonsa ta ɗauke shi ta gudu, amma yayinda take hanzari tă gudu, sai ya fāɗo, ya gurgunce.)
5 venientes igitur filii Remmon Berothitae Rechab et Baana ingressi sunt fervente die domum Hisboseth qui dormiebat super stratum suum meridie
To, Rekab da Ba’ana,’ya’yan Rimmon mutumin Beyerot, suka tafi gidan Ish-Boshet, suka isa can da tsakar rana yayinda yake hutun tsakar rana.
6 ingressi sunt autem domum adsumentes spicas tritici et percusserunt eum in inguine Rechab et Baana frater eius et fugerunt
Suka shiga sashe na cikin gida sai ka ce suna so su ɗibo alkama ne, suka soke shi a ciki. Sa’an nan Rekab da Ba’ana ɗan’uwansa suka zame suka ɓace.
7 cum autem ingressi fuissent domum ille dormiebat super lectulum suum in conclavi et percutientes interfecerunt eum sublatoque capite eius abierunt per viam deserti tota nocte
Sun shiga gidan yayinda yake kwance a gado a ɗakin barcinsa. Bayan sun soke shi sai suka kashe shi, suka kuma datse kansa. Suka ɗauke shi, suka yi tafiya dukan dare suka bi ta Araba.
8 et adtulerunt caput Hisboseth ad David in Hebron dixeruntque ad regem ecce caput Hisboseth filii Saul inimici tui qui quaerebat animam tuam et dedit Dominus domino meo regi ultiones hodie de Saul et de semine eius
Suka kawo kan Ish-Boshet wa Dawuda a Hebron, suka ce wa sarki, “Ga kan Ish-Boshet ɗan Shawulu, maƙiyinka, wanda ya nemi yă kashe ka. A yau Ubangiji ya rama wa ranka yă daɗe sarki, a kan Shawulu da zuriyarsa.”
9 respondens autem David Rechab et Baana fratri eius filiis Remmon Berothei dixit ad eos vivit Dominus qui eruit animam meam de omni angustia
Dawuda ya ce wa Rekab da ɗan’uwansa Ba’ana,’ya’yan Rimmon mutumin Beyerot, “Muddin Ubangiji yana a raye, wanda ya kuɓutar da ni daga wahala,
10 quoniam eum qui adnuntiaverat mihi et dixerat mortuus est Saul qui putabat se prospera nuntiare tenui et occidi in Siceleg cui oportebat me dare mercedem pro nuntio
sa’ad da wani mutum ya ce mini, ‘Shawulu ya mutu,’ yana tsammani ya kawo labari mai daɗi ne, na kama shi na kashe a Ziklag. Ladar da na ba shi ke nan saboda labarinsa!
11 quanto magis nunc cum homines impii interfecerint virum innoxium in domo sua super lectulum suum non quaeram sanguinem eius de manu vestra et auferam vos de terra
Balle fa, sa’ad da mugayen mutane suka kashe marar laifi a gidansa, a bisa gadonsa, ashe, ba zan nemi jininsa daga hannunku in kawar da ku a duniya ba!”
12 praecepit itaque David pueris et interfecerunt eos praecidentesque manus et pedes eorum suspenderunt eos super piscinam in Hebron caput autem Hisboseth tulerunt et sepelierunt in sepulchro Abner in Hebron
Saboda haka Dawuda ya umarci mutanensa, suka kuwa kashe su. Suka yayyanka hannuwansu da ƙafafunsu, suka kuma rataye jikunansu kusa da tafki a Hebron. Amma suka ɗauki kan Ish-Boshet suka binne a kabarin Abner a Hebron.

< Ii Samuelis 4 >