< Ii Samuelis 13 >

1 factum est autem post haec ut Absalom filii David sororem speciosissimam vocabulo Thamar adamaret Amnon filius David
Ana nan sai Amnon ɗan Dawuda ya fara son Tamar, kyakkyawar’yar’uwar Absalom ɗan Dawuda.
2 et deperiret eam valde ita ut aegrotaret propter amorem eius quia cum esset virgo difficile ei videbatur ut quippiam inhoneste ageret cum ea
Amnon ya matsu ƙwarai har abin ya sa shi ciwo saboda ƙanuwarsa Tamar. Ya gane zai zama da wuya yă sadu da Tamar ita kaɗai, gama ba ta taɓa kwana da namiji ba.
3 erat autem Amnonis amicus nomine Ionadab filius Semaa fratris David vir prudens valde
To, Amnon yana da wani aboki mai suna Yonadab, ɗan Shimeya, ɗan’uwan Dawuda. Yonadab dai mai wayo ne ƙwarai.
4 qui dixit ad eum quare sic adtenuaris macie fili regis per singulos dies cur non indicas mihi dixitque ei Amnon Thamar sororem Absalom fratris mei amo
Ya tambayi Amnon ya ce, “Don me kowace safiya fuskarka a ɓace take? Kai ba yaron sarki ba ne? Faɗa mini, me ke faruwa?” Amnon ya ce masa, “Ina son Tamar ƙanuwar wan nawa Absalom ne.”
5 cui respondit Ionadab cuba super lectulum tuum et languorem simula cumque venerit pater tuus ut visitet te dic ei veniat oro Thamar soror mea ut det mihi cibum et faciat pulmentum ut comedam de manu eius
Yonadab ya ce, “Je gado ka kwanta kamar ba ka da lafiya. Sa’ad da mahaifinka ya zo ganinka, sai ka ce masa, ‘Ina so ƙanuwata Tamar tă kawo mini wani abu in ci. Bari tă shirya abincin a gabana don in ganta, in kuma ci daga hannunta.’”
6 accubuit itaque Amnon et quasi aegrotare coepit cumque venisset rex ad visitandum eum ait Amnon ad regem veniat obsecro Thamar soror mea ut faciat in oculis meis duas sorbitiunculas et cibum capiam de manu eius
Sai Amnon ya kwanta sai ka ce yana ciwo. Da sarki ya zo don ganinsa, sai Amnon ya ce, “Zan so ƙanuwata Tamar tă zo tă shirya mini abinci a gabana, don in ci daga hannunta.”
7 misit ergo David ad Thamar domum dicens veni in domum Amnon fratris tui et fac ei pulmentum
Dawuda kuwa ya aika wa Tamar a fada, ya ce, “Ki je gidan Amnon ɗan’uwanki, ki yi masa abinci.”
8 venitque Thamar in domum Amnon fratris sui ille autem iacebat quae tollens farinam commiscuit et liquefaciens in oculis eius coxit sorbitiunculas
Saboda haka Tamar ta tafi gidan ɗan’uwanta Amnon, wanda yake kwance. Ta ɗauki fulawa, ta kwaɓa, ta yi burodi a gabansa ta toya shi.
9 tollensque quod coxerat effudit et posuit coram eo et noluit comedere dixitque Amnon eicite universos a me cumque eiecissent omnes
Sa’an nan ta juye a kasko ta ba shi burodin, amma ya ƙi ci. Amnon ya ce, “A sa kowa yă fita daga nan.” Saboda haka kowa ya fita ya bar shi.
10 dixit Amnon ad Thamar infer cibum in conclave ut vescar de manu tua tulit ergo Thamar sorbitiunculas quas fecerat et intulit ad Amnon fratrem suum in conclave
Sa’an nan Amnon ya ce wa Tamar, “Kawo abincin a nan a cikin ɗakin kwanciyata, don in ci daga hannunki.” Tamar kuwa ta ɗauki burodin da ta toya, ta kawo wa ɗan’uwanta Amnon a ciki ɗakin kwanciyarsa.
11 cumque obtulisset ei cibum adprehendit eam et ait veni cuba mecum soror mea
Amma da ta kai masa don yă ci, sai ya cafke ta ya ce, “Zo in kwana da ke,’yar’uwata.”
12 quae respondit ei noli frater mi noli opprimere me neque enim hoc fas est in Israhel noli facere stultitiam hanc
Ta ce, “Kada ka yi wannan ɗan’uwana! Kada ka tilasta ni. Bai kamata a yi irin wannan abu a Isra’ila ba! Kada ka yi wannan mugun abu.
13 et ego enim ferre non potero obprobrium meum et tu eris quasi unus de insipientibus in Israhel quin potius loquere ad regem et non negabit me tibi
Ni fa, ina zan sa kaina saboda kunya? Kai kuma za ka zama kamar wani mugun wawa a Isra’ila. Ina roƙonka ka yi wa sarki magana; ba zai hana ni aurenka ba.”
14 noluit autem adquiescere precibus eius sed praevalens viribus oppressit eam et cubavit cum illa
Amma Amnon ya ƙi yă saurare ta, da yake ya fi ta ƙarfi, sai ya yi mata fyaɗe.
15 et exosam eam habuit Amnon magno odio nimis ita ut maius esset odium quo oderat eam amore quo ante dilexerat dixitque ei Amnon surge vade
Bayan ya yi lalata da ita sai Amnon ya ƙi ta da mummunan ƙiyayya. Zahiri ya ƙi ta fiye da ya ƙaunace ta. Sai Amnon ya ce mata, “Tashi, ki fita!”
16 quae respondit ei maius est hoc malum quod nunc agis adversum me quam quod ante fecisti expellens me et noluit audire eam
Ta ce, “A’a! Korina zai fi muni da abin da ka riga ka yi mini.” Amma ya ƙi yă saurare ta.
17 sed vocato puero qui ministrabat ei dixit eice hanc a me foras et claude ostium post eam
Sai ya kira bawansa ya ce, “Fitar da matan nan daga nan, ka rufe ƙofa.”
18 quae induta erat talari tunica huiuscemodi enim filiae regis virgines vestibus utebantur eiecit itaque eam minister illius foras clausitque fores post eam
Saboda haka bawansa ya fitar da ita, ya kuma sa aka rufe ƙofa. Tana sanye da doguwar riga mai kayan ado masu tsada, gama wannan ne irin kayan da budurwai’ya’yan sarki mata suke sawa.
19 quae aspergens cinerem capiti suo scissa talari tunica inpositisque manibus super caput suum ibat ingrediens et clamans
Sai Tamar ta zuba toka a kanta, ta kuma yayyage doguwar riga mai kayan adon da take sanye da shi. Ta sa hannunta a kai, ta tafi tana kuka da ƙarfi.
20 dixit autem ei Absalom frater suus num Amnon frater tuus concubuit tecum sed nunc soror tace frater tuus est neque adfligas cor tuum pro re hac mansit itaque Thamar contabescens in domo Absalom fratris sui
Absalom ɗan’uwanta ya ce mata, “Amnon, ɗan’uwanki ya ɓata ki ko? To, ki yi shiru’yar’uwata; ai, ɗan’uwanki ne. Kada wannan abu yă dame ki.” Tamar kuwa ta zauna a gidan ɗan’uwanta Absalom, zaman kaɗaici.
21 cum autem audisset rex David verba haec contristatus est valde
Da Sarki Dawuda ya ji dukan abin da ya faru, sai ya husata ƙwarai.
22 porro non est locutus Absalom ad Amnon nec malum nec bonum oderat enim Absalom Amnon eo quod violasset Thamar sororem suam
Absalom kuwa bai yi wa Amnon wata magana ta alheri ko ta mugunta ba; ya ƙi jinin Amnon domin ya ci mutuncin ƙanuwarsa Tamar.
23 factum est autem post tempus biennii ut tonderentur oves Absalom in Baalasor quae est iuxta Ephraim et vocavit Absalom omnes filios regis
Bayan shekaru biyu, sa’ad da masu askin tumakin Absalom suna Ba’al-Hazor, kusa da iyakar Efraim, sai ya gayyaci dukan’ya’yan sarki maza a can.
24 venitque ad regem et ait ad eum ecce tondentur oves servi tui veniat oro rex cum servis suis ad servum suum
Sai Absalom ya je wurin sarki ya ce, “Bawanka ya sa masu askin tumaki sun zo. Ko sarki da fadawansa za su zo tare da ni?”
25 dixitque rex ad Absalom noli fili mi noli rogare ut veniamus omnes et gravemus te cum autem cogeret eum et noluisset ire benedixit ei
Sarki ya ce, “A’a ɗana, bai kamata dukanmu mu tafi ba; don kada nauyi yă yi maka yawa.” Absalom dai ya dāge, duk da haka sarki ya ƙi yă je, sai dai ya albarkace shi.
26 et ait Absalom si non vis venire veniat obsecro nobiscum saltem Amnon frater meus dixitque ad eum rex non est necesse ut vadat tecum
Sa’an nan Absalom ya ce, to, “In ba za ka ba, ina roƙonka bari Amnon ɗan’uwana yă zo tare da mu.” Sarki ya ce masa, “Don me zai tafi tare da kai?”
27 coegit itaque eum Absalom et dimisit cum eo Amnon et universos filios regis
Amma Absalom ya nace don sarki yă yarda, saboda haka sarki ya bar Amnon da sauran’ya’yan sarki maza su tafi tare da shi.
28 praeceperat autem Absalom pueris suis dicens observate cum temulentus fuerit Amnon vino et dixero vobis percutite eum et interficite nolite timere ego enim sum qui praecepi vobis roboramini et estote viri fortes
Absalom ya umarci mutanensa ya ce, “Ku saurara! Sa’ad da Amnon ya bugu sosai da giya na kuma ce muku, ‘Ku bugi Amnon,’ sai ku kashe shi. Kada ku ji tsoro. Ashe, ba ni ne na ba ku wannan umarni ba? Ku yi ƙarfin hali, ku kuma yi jaruntaka.”
29 fecerunt ergo pueri Absalom adversum Amnon sicut praeceperat eis Absalom surgentesque omnes filii regis ascenderunt singuli mulas suas et fugerunt
Saboda haka mutanen Absalom suka yi wa Amnon abin da Absalom ya umarta. Sai dukan sauran’ya’yan sarki maza suka hau dawakansu suka gudu.
30 cumque adhuc pergerent in itinere fama praevenit ad David dicens percussit Absalom omnes filios regis et non remansit ex eis saltem unus
Yayinda suke kan hanyarsu, sai labari ya kai kunnen Dawuda cewa, “Absalom ya kashe dukan’ya’yan sarki maza; ko ɗayansu Absalom bai rage ba.”
31 surrexit itaque rex et scidit vestimenta sua et cecidit super terram et omnes servi ipsius qui adsistebant ei sciderunt vestimenta sua
Sai sarki ya tashi, ya yage tufafinsa, ya kuma kwanta a ƙasa; dukan bayinsa kuwa suka tsaya da rigunansu yagaggu.
32 respondens autem Ionadab filius Samaa fratris David dixit ne aestimet dominus meus quod omnes pueri filii regis occisi sint Amnon solus mortuus est quoniam in ore Absalom erat positus ex die qua oppressit Thamar sororem eius
Amma Yonadab, ɗan Shimeya ɗan’uwan Dawuda ya ce, “Kada ranka yă daɗe yă yi tunani cewa an kashe dukan’ya’yan sarki maza; Amnon ne kaɗai ya mutu. Wannan ce niyyar Absalom tun lokacin da Amnon ya yi wa Tamar’yar’uwansa fyaɗe.
33 nunc ergo ne ponat dominus meus rex super cor suum verbum istud dicens omnes filii regis occisi sunt quoniam Amnon solus mortuus est
Kada mai girma sarki yă damu da jita-jitan nan cewa an kashe dukan’ya’yan sarki maza. Amnon ne kaɗai ya mutu.”
34 fugit autem Absalom et levavit puer speculator oculos suos et aspexit et ecce populus multus veniebat per iter devium ex latere montis
Ana cikin haka, sai Absalom ya gudu. To, mutumin da yake tsaro a wannan lokaci ya ɗaga kai sai ya ga mutane da yawa a hanya, yamma da shi, suna gangarowa daga gefen tudu. Sai mai tsaron ya je ya gaya wa sarki cewa, “Na ga mutane ta wajen Horonayim, a gefen tudu.”
35 dixit autem Ionadab ad regem ecce filii regis adsunt iuxta verbum servi tui sic factum est
Yonadab ya ce wa Sarki, “Duba, ga’ya’yan sarki maza sun zo; ya faru kamar dai yadda bawanka ya faɗa.”
36 cumque cessasset loqui apparuerunt et filii regis et intrantes levaverunt vocem suam et fleverunt sed et rex et omnes servi eius fleverunt ploratu magno nimis
Yana gama magana, sai ga’ya’yan sarki maza suka shigo suna kuka da ƙarfi. Sarki ma da dukan bayinsa suka yi kuka mai zafi.
37 porro Absalom fugiens abiit ad Tholomai filium Amiur regem Gessur luxit ergo David filium suum cunctis diebus
Absalom ya gudu ya tafi wurin Talmai ɗan Ammihud, sarkin Geshur. Amma Sarki Dawuda ya yi ta makokin ɗansa kowace rana.
38 Absalom autem cum fugisset et venisset in Gessur fuit ibi tribus annis
Bayan Absalom ya gudu sai ya je wurin Geshur, ya zauna a can shekara uku.
39 cessavitque David rex persequi Absalom eo quod consolatus esset super Amnon interitu
Sai zuciyar sarki Dawuda ya komo kan Absalom, gama an yi masa ta’aziyya game da mutuwar Amnon.

< Ii Samuelis 13 >