< Ii Paralipomenon 36 >

1 tulit ergo populus terrae Ioachaz filium Iosiae et constituit regem pro patre suo in Hierusalem
Sai mutanen ƙasar suka ɗauki Yehoyahaz ɗan Yosiya suka naɗa shi sarki a Urushalima yă gāji mahaifinsa.
2 viginti trium annorum erat Ioachaz cum regnare coepisset et tribus mensibus regnavit in Hierusalem
Yehoyahaz yana da shekara ashirin da uku sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima wata uku.
3 amovit autem eum rex Aegypti cum venisset Hierusalem et condemnavit terram centum talentis argenti et talento auri
Sarkin Masar ya tumɓuke shi a Urushalima, ya tilasta Yahuda su biya haraji talenti ɗari na azurfa da kuma talentin zinariya.
4 constituitque regem pro eo Eliacim fratrem eius super Iudam et Hierusalem et vertit nomen eius Ioacim ipsum vero Ioachaz tulit secum et adduxit in Aegyptum
Sarkin Masar ya naɗa Eliyakim, ɗan’uwan Yehoyahaz, sarki a bisa Yahuda da kuma Urushalima, ya kuma canja sunan Eliyakim zuwa Yehohiyakim. Amma Neko ya ɗauki Yehoyahaz ɗan’uwan Eliyakim ya kai Masar.
5 viginti quinque annorum erat Ioacim cum regnare coepisset et undecim annis regnavit in Hierusalem fecitque malum coram Domino Deo suo
Yehohiyakim yana da shekara ashirin da biyar sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara goma sha ɗaya. Ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji Allahnsa.
6 contra hunc ascendit Nabuchodonosor rex Chaldeorum et vinctum catenis duxit in Babylonem
Nebukadnezzar sarkin Babilon ya hauro ya kara da shi. Ya kama shi, ya daure da sarƙoƙin tagulla, ya kuma kai shi Babilon.
7 ad quam et vasa Domini transtulit et posuit ea in templo suo
Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kuma kwaso kayayyaki daga haikalin Ubangiji ya sa su a haikalinsa a can.
8 reliqua autem verborum Ioacim et abominationum eius quas operatus est et quae inventa sunt in eo continentur in libro regum Israhel et Iuda regnavitque Ioachin filius eius pro eo
Sauran ayyukan mulkin Yehohiyakim, ayyukan banƙyamar da ya aikata da dukan abubuwan da aka same shi da su, suna a rubuce cikin littafin sarakunan Isra’ila da na Yahuda. Sai Yehohiyacin ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.
9 octo annorum erat Ioachin cum regnare coepisset et tribus mensibus ac decem diebus regnavit in Hierusalem fecitque malum in conspectu Domini
Yehohiyacin yana da shekara goma sha takwas sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima wata uku da kwana goma. Ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji.
10 cumque anni circulus volveretur misit Nabuchodonosor rex qui et adduxerunt eum in Babylonem asportatis simul pretiosissimis vasis domus Domini regem vero constituit Sedeciam fratrem eius super Iudam et Hierusalem
Da bazara, Sarki Nebukadnezzar ya aika a kawo Yehohiyacin, aka kuma kawo shi Babilon, tare da kayayyaki masu daraja daga haikalin Ubangiji, sai Sarki Nebukadnezzar ya naɗa kawunsa Zedekiya, sarki a bisa Yahuda da Urushalima.
11 viginti et unius anni erat Sedecias cum regnare coepisset et undecim annis regnavit in Hierusalem
Zedekiya yana da shekara ashirin da ɗaya sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara goma sha ɗaya.
12 fecitque malum in oculis Domini Dei sui nec erubuit faciem Hieremiae prophetae loquentis ad se ex ore Domini
Ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji Allahnsa kuma bai ƙasƙantar da kansa a gaban Irmiya annabi, wanda ya yi magana kalmar Ubangiji ba.
13 a rege quoque Nabuchodonosor recessit qui adiuraverat eum per Deum et induravit cervicem suam et cor ut non reverteretur ad Dominum Deum Israhel
Ya tayar wa Sarki Nebukadnezzar, wanda ya sa ya yi rantsuwa da sunan Allah. Ya zama mai kunnen ƙashi da kuma taurin zuciya, bai kuwa juye ga Ubangiji, Allah na Isra’ila ba.
14 sed et universi principes sacerdotum et populus praevaricati sunt inique iuxta universas abominationes gentium et polluerunt domum Domini quam sanctificaverat sibi in Hierusalem
Bugu da ƙari, dukan shugabannin firistoci da mutane suka ƙara zama marasa aminci, suna bin dukan abubuwan banƙyama na al’ummai, suka ƙazantar da haikalin Ubangiji, wanda ya tsarkake a Urushalima.
15 mittebat autem Dominus Deus patrum suorum ad illos per manum nuntiorum suorum de nocte consurgens et cotidie commonens eo quod parceret populo et habitaculo suo
Sai Ubangiji Allah na kakanninsu, ya yi ta aika da magana gare su ta wurin’yan saƙonsa sau da sau, domin ya ji tausayi mutanensa da mazauninsa.
16 at illi subsannabant nuntios Dei et parvipendebant sermones eius inludebantque prophetis donec ascenderet furor Domini in populum eius et esset nulla curatio
Amma suka yi wa’yan saƙon Allah ba’a, suka rena maganarsa, suka yi wa annabawansa dariyar reni, har sai da fushin Ubangiji ya tasar a kan mutanensa babu makawa.
17 adduxit enim super eos regem Chaldeorum et interfecit iuvenes eorum gladio in domo sanctuarii sui non est misertus adulescentis et virginis et senis nec decrepiti quidem sed omnes tradidit manibus eius
Ya bashe su ga sarkin Babiloniyawa wanda ya karkashe samarinsu da takobi a wuri mai tsarki, bai yi juyayin saurayi, ko budurwa, ko tsoho, ko gajiyayye ba. Allah ya bashe su duka ga Nebukadnezzar.
18 universaque vasa domus Domini tam maiora quam minora et thesauros templi et regis et principum transtulit in Babylonem
Nebukadnezzar ya kwashe dukan kayayyaki daga haikalin Allah, babba da ƙarami, da ma’ajin haikalin Ubangiji da kuma ma’ajin sarki da na fadawansa zuwa Babilon.
19 incenderunt hostes domum Dei destruxerunt murum Hierusalem universas turres conbuserunt et quicquid pretiosum fuerat demoliti sunt
Suka cinna wa haikalin Allah wuta, suka rurrushe katangar Urushalima; suka ƙone dukan fada, suka kuma lalace kome mai amfani da yake can.
20 si quis evaserat gladium ductus in Babylonem servivit regi et filiis eius donec imperaret rex Persarum
Waɗanda ba a kashe ba kuwa Nebukadnezzar ya kwashe su, ya kai Babilon, suka zama bayinsa da na’ya’yansa maza har zuwa kahuwar mulkin Farisa.
21 et conpleretur sermo Domini ex ore Hieremiae et celebraret terra sabbata sua cunctis enim diebus desolationis egit sabbatum usque dum conplerentur septuaginta anni
Ƙasar ta more hutun Asabbacinta; a dukan lokacin zamanta kango ta huta, har sai da shekaru saba’in nan suka cika bisa ga maganar Ubangiji da Irmiya ya faɗi.
22 anno autem primo Cyri regis Persarum ad explendum sermonem Domini quem locutus fuerat per os Hieremiae suscitavit Dominus spiritum Cyri regis Persarum qui iussit praedicari in universo regno suo etiam per scripturam dicens
Don a cika maganar da Ubangiji ya yi ta wurin Irmiya, a shekara farko ta Sairus sarkin Farisa, sai Ubangiji ya motsa zuciyar Sairus na Farisa don yă yi shela a dukan masarautarsa, ya kuma sa shi a rubuce cewa,
23 haec dicit Cyrus rex Persarum omnia regna terrae dedit mihi Dominus Deus caeli et ipse praecepit mihi ut aedificarem ei domum in Hierusalem quae est in Iudaea quis ex vobis est in omni populo eius sit Dominus Deus suus cum eo et ascendat
“Ga abin da Sairus sarkin Farisa ya ce, “‘Ubangiji Allah na sama, ya ba ni dukan mulkokin duniya, ya kuma naɗa ni in gina masa haikali a Urushalima a Yahuda. Duk wani na mutanensa a cikinku, bari yă haura yă tafi, bari kuma Ubangiji Allahnsa yă kasance tare da shi.’”

< Ii Paralipomenon 36 >