< Ii Paralipomenon 22 >
1 constituerunt autem habitatores Hierusalem Ochoziam filium eius minimum regem pro eo omnes enim maiores natu qui ante eum fuerant interfecerant latrones Arabum qui inruerant in castra regnavitque Ochozias filius Ioram regis Iuda
Mutanen Urushalima suka mai da Ahaziya, autan Yehoram, sarki a madadinsa, da yake’yan hari, waɗanda suka zo tare da Larabawa cikin sansani, sun kashe dukan manyan’ya’yansa. Saboda haka Ahaziya ɗan Yeroham sarkin Yahuda ya fara mulki.
2 filius quadraginta duo annorum erat Ochozias cum regnare coepisset et uno anno regnavit in Hierusalem nomen matris eius Otholia filia Amri
Ahaziya yana da shekara ashirin da biyu sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara guda. Sunan mahaifiyarsa Ataliya ce, jikanyar Omri.
3 sed et ipse ingressus est per vias domus Ahab mater enim eius inpulit eum ut impie ageret
Shi ma ya yi tafiya a hanyoyin gidan Ahab, gama mahaifiyarsa ta ƙarfafa shi yă yi abin da ba shi da kyau.
4 fecit igitur malum in conspectu Domini sicut domus Ahab ipsi enim fuerunt ei consiliarii post mortem patris sui in interitum eius
Ya aikata mugayen ayyuka a gaban Ubangiji, yadda gidan Ahab ta yi, gama bayan mutuwar mahaifinsa, sai gidan Ahab ta zama masu ba shi shawara, shawarar da ta kai shi ga lalacewa.
5 ambulavitque in consiliis eorum et perrexit cum Ioram filio Ahab rege Israhel in bellum contra Azahel regem Syriae in Ramoth Galaad vulneraveruntque Syri Ioram
Ya kuma bi shawararsu sa’ad da ya tafi tare da Yoram ɗan Ahab sarkin Isra’ila don yă yaƙi Hazayel sarkin Aram a Ramot Gileyad. Sai Arameyawa suka yi wa Yoram rauni;
6 qui reversus est ut curaretur in Hiezrahel multas enim plagas acceperat in supradicto certamine igitur Azarias filius Ioram rex Iuda descendit ut inviseret Ioram filium Ahab in Hiezrahel aegrotantem
saboda haka ya dawo Yezireyel don yă yi jinyar raunin da suka yi masa a Rama cikin yaƙinsa da Hazayel sarkin Aram. Sa’an nan Azariya ɗan Yehoram sarkin Yahuda ya gangara zuwa Yezireyel don yă ga Yoram ɗan Ahab domin ya ji rauni.
7 voluntatis quippe fuit Dei adversum Ochoziam ut veniret ad Ioram et cum venisset egrederetur cum eo adversum Hieu filium Namsi quem unxit Dominus ut deleret domum Ahab
Ta wurin ziyarar Yoram, Allah ya kawo fāɗuwar Ahaziya. Sa’ad da Ahaziya ya iso, ya tafi tare da Yoram domin yă sadu da Yehu ɗan Nimshi, wanda Ubangiji ya shafe don yă hallaka gidan Ahab.
8 cum ergo subverteret Hieu domum Ahab invenit principes Iuda et filios fratrum Ochoziae qui ministrabant ei et interfecit illos
Yayinda Yehu yake hukunta wa gidan Ahab, sai ya sami fadawan Yahuda da kuma’ya’yan dangin Ahaziya maza, waɗanda suke yi wa Ahaziya hidima, sai ya kashe su.
9 ipsumque perquirens Ochoziam conprehendit latentem in Samaria adductumque ad se occidit et sepelierunt eum eo quod esset filius Iosaphat qui quaesierat Dominum in toto corde suo nec erat ultra spes aliqua ut de stirpe regnaret Ochoziae
Ya kuma sa aka nemi Ahaziya. Aka kamo shi sa’ad da ya ɓuya a Samariya, suka kawo shi wurin Yehu, suka kashe shi, suka binne shi, gama sun ce, “Shi jikan Yehoshafat ne, wanda ya nemi Ubangiji da dukan zuciyarsa.” Ta haka babu wani a gidan Ahaziya da yake da ƙarfin cin gaba da mulkin.
10 siquidem Otholia mater eius videns quod mortuus esset filius suus surrexit et interfecit omnem stirpem regiam domus Ioram
Sa’ad da Ataliya mahaifiyar Ahaziya ta ga cewa ɗanta ya mutu, sai ta tashi ta hallaka dukan’yan gidan sarautar Yahuda.
11 porro Iosabeth filia regis tulit Ioas filium Ochoziae et furata est eum de medio filiorum regis cum interficerentur absconditque cum nutrice sua in cubiculo lectulorum Iosabeth autem quae absconderat eum erat filia regis Ioram uxor Ioiadae pontificis soror Ochoziae et idcirco Otholia non interfecit eum
Amma Yehosheba,’yar Sarki Yehoram, ta ɗauki Yowash ɗan Ahaziya ta sace shi daga cikin’ya’yan gidan sarauta waɗanda ake shiri a kashe, ta sa shi tare da mai renonsa a ɗakin kwana. Haka fa, Yehosheba’yar sarki Yoram, matar Yehohiyada firist, ta yi, gama ita’yar’uwar Ahaziya ce, ta ɓoye Yowash don kada Ataliya tă kashe shi.
12 fuit ergo cum eis in domo Dei absconditus sex annis quibus regnavit Otholia super terram
Ya kasance a ɓoye tare da su a haikalin Allah shekara shida, yayinda Ataliya take mulkin ƙasar.