< Timotheum I 2 >

1 obsecro igitur primo omnium fieri obsecrationes orationes postulationes gratiarum actiones pro omnibus hominibus
Don haka da farko dai, Ina roko a yi roke-roke da addu'o'i, da yin roko domin jama, a dukka, da ba da godiya, a yi haka domin dukkan mutane,
2 pro regibus et omnibus qui in sublimitate sunt ut quietam et tranquillam vitam agamus in omni pietate et castitate
domin sarakuna da dukkan masu mulki, domin mu yi zaman salama da rayuwa a natse cikin Allahntaka da daraja.
3 hoc enim bonum est et acceptum coram salutari nostro Deo
Wannan yana da kyau da karbuwa a gaban Allah mai cetonmu.
4 qui omnes homines vult salvos fieri et ad agnitionem veritatis venire
Yana so dukkan mutane su sami ceto, su kai ga sanin gaskiya.
5 unus enim Deus unus et mediator Dei et hominum homo Christus Iesus
Domin Allah daya ne, Matsakanci kuma daya ne, tsakanin Allah da mutum, wannan mutum Almasihu Yesu ne.
6 qui dedit redemptionem semet ipsum pro omnibus testimonium temporibus suis
Ya bada kansa fansa domin kowa, domin shaida a daidaitaccen lokaci.
7 in quo positus sum ego praedicator et apostolus veritatem dico non mentior doctor gentium in fide et veritate
Sabo da wannan dalilin, aka sa ni kaina, na zama mai shelar bishara da manzo. Gaskiya nake fada. Ba karya nake yi ba. Ni mai koyarwa ne na al'ummai cikin gaskiya da kuma imani.
8 volo ergo viros orare in omni loco levantes puras manus sine ira et disceptatione
Saboda haka, ina so maza da ke a kowanne wuri suyi addu'a, kuma suna daga hannuwa masu tsarki a sama ba tare da fushi da gardama ba.
9 similiter et mulieres in habitu ornato cum verecundia et sobrietate ornantes se non in tortis crinibus aut auro aut margaritis vel veste pretiosa
Kazalika, ina so mata su sa kayan da ya cancanta, da adon da ya dace da kamun kai. Kada su zama masu kitson gashi da zinariya da azurfa da tufafi masu tsada.
10 sed quod decet mulieres promittentes pietatem per opera bona
Ina so su sa tufafin da ya cancanci matan da ke rayuwar Allahntaka ta wurin kyawawan ayyuka.
11 mulier in silentio discat cum omni subiectione
Mace ta koya cikin natsuwa da saukin kai a cikin komai.
12 docere autem mulieri non permitto neque dominari in virum sed esse in silentio
Ban ba da izini mace ta koyar ko ta nuna iko a kan namiji ba, amma ta zauna da natsuwa.
13 Adam enim primus formatus est deinde Eva
Adamu ne aka fara halitta, kafin Hauwa'u.
14 et Adam non est seductus mulier autem seducta in praevaricatione fuit
Ba Adamu ne aka yaudara ba, amma macen ce aka yaudara cikin laifi.
15 salvabitur autem per filiorum generationem si permanserint in fide et dilectione et sanctificatione cum sobrietate
Duk da haka, zata sami ceto ta wurin haifuwar 'ya'ya, idan suka ci gaba cikin bangaskiya, da kauna da tsarki da sahihiyar zuciya.

< Timotheum I 2 >