< Thessalonicenses I 1 >
1 Paulus et Silvanus et Timotheus ecclesiae Thessalonicensium in Deo Patre et Domino Iesu Christo gratia vobis et pax
Bulus, Sila, da Timoti zuwa ga Ikilisiyar Tassalonikawa cikin Allah Uba da Ubangiji Yesu Almasihu. Alheri da Salama su kasance a gare ku.
2 gratias agimus Deo semper pro omnibus vobis memoriam facientes in orationibus nostris sine intermissione
Kullum muna bada godiya ga Allah domin ku dukka, kamar yadda muke ambaton ku a addu'o'in mu.
3 memores operis fidei vestrae et laboris et caritatis et sustinentiae spei Domini nostri Iesu Christi ante Deum et Patrem nostrum
Muna tunawa da ku ba fasawa a gaban Allahn mu da Ubanmu kuma ayyukanku na bangaskiya, da kauna. Da hakurin bege na abinda ke gaba cikin Ubangijinmu Yesu Almasihu.
4 scientes fratres dilecti a Deo electionem vestram
'Yan'uwa kaunatattu na Allah, Mun san kiran ku,
5 quia evangelium nostrum non fuit ad vos in sermone tantum sed et in virtute et in Spiritu Sancto et in plenitudine multa sicut scitis quales fuerimus vobis propter vos
yadda bishararmu ta zo gare ku ba ta magana kadai ba, amma da iko, ta wurin Ruhu Mai Tsarki, haka kuma tawurin tabbatarwa. Ta haka kuma, kun san irin mutanen da muke acikin ku kuma domin ku.
6 et vos imitatores nostri facti estis et Domini excipientes verbum in tribulatione multa cum gaudio Spiritus Sancti
Kun zama masu koyi da mu da kuma Ubangiji, kamar yadda kuka karbi kalmar cikin tsanani mai yawa da murna tawurin Ruhu Mai Tsaki.
7 ita ut facti sitis forma omnibus credentibus in Macedonia et in Achaia
Sakamakon haka, kuka zama abin misali ga dukkan wadanda ke Makidoniya da na Akaya wadanda suka bada gaskiya.
8 a vobis enim diffamatus est sermo Domini non solum in Macedonia et in Achaia sed in omni loco fides vestra quae est ad Deum profecta est ita ut non sit nobis necesse quicquam loqui
Gama daga gare kune maganar Allah ta bazu ko ina, ba kuwa Makidoniya da Akaya kadai ba. A maimako, har ma zuwa ko ina bangaskiyarku cikin Allah ta kai. Don haka, bama bukatar muce maku komai.
9 ipsi enim de nobis adnuntiant qualem introitum habuerimus ad vos et quomodo conversi estis ad Deum a simulacris servire Deo vivo et vero
Domin su da kansu suna bada labarin irin zuwan mu gare ku. Suna fadin yadda kuka juyo ga Allah daga bautar gumaka don ku bautawa Allah mai rai.
10 et expectare Filium eius de caelis quem suscitavit ex mortuis Iesum qui eripuit nos ab ira ventura
Suna bayyana cewa kuna jiran bayyanar Dansa daga sama, wanda ya tasar daga matattu. Wannan shine Yesu, wanda ya 'yantad da mu daga fushi mai zuwa.