< Corinthios I 9 >

1 non sum liber non sum apostolus nonne Iesum Dominum nostrum vidi non opus meum vos estis in Domino
Ni ba yantacce bane? Ni ba Manzo ba ne? Ban ga Ubangijinmu Yesu ba? ba ku ne aikin hannuna cikin Ubangiji ba?
2 si aliis non sum apostolus sed tamen vobis sum nam signaculum apostolatus mei vos estis in Domino
Idan ni ba Manzo ba ne ga wadansu, hakika ni Manzo ne a gare ku. Ai kune shedar manzanci na cikin Ubangiji.
3 mea defensio apud eos qui me interrogant haec est
Ga kariya ta zuwa masu zargi na,
4 numquid non habemus potestatem manducandi et bibendi
Ba mu da 'yanci mu ci mu sha?
5 numquid non habemus potestatem sororem mulierem circumducendi sicut et ceteri apostoli et fratres Domini et Cephas
Ba mu da 'yanci mu dauki mace mai bada gaskiya kamar sauran manzanni da Kefas da 'yan'uwan Ubangiji?
6 aut solus ego et Barnabas non habemus potestatem hoc operandi
ko ni da Barnabas ne kawai muka cancanci aiki?
7 quis militat suis stipendiis umquam quis plantat vineam et fructum eius non edit quis pascit gregem et de lacte gregis non manducat
Wake aikin soja daga aljihunsa? Wake shuka gonar inabi baya ci daga 'ya'yan ta ba? Ko kuwa wake kiwon tumaki ba ya shan madarasu?
8 numquid secundum hominem haec dico an et lex haec non dicit
Ina wannan zance da ikon mutum ne? Doka bata fadi haka ba?
9 scriptum est enim in lege Mosi non alligabis os bovi trituranti numquid de bubus cura est Deo
Gama a rubuce yake a attaura ta Musa cewa, Takarkari mai tattake hatsi kada a sa masa takunkumi. Amma shanu ne Ubangiji ke zance a kai?
10 an propter nos utique dicit nam propter nos scripta sunt quoniam debet in spe qui arat arare et qui triturat in spe fructus percipiendi
Ba don mu yake magana ba? An rubuta domin mu ne. Domin wanda yake noma, yayi cikin bege. mai tattake hatsi kuma yayi da begen samu.
11 si nos vobis spiritalia seminavimus magnum est si nos carnalia vestra metamus
Idan mun yi shuka ta ruhaniya a rayuwarku, mai wuya ne mu girbi kayan ku na jiki?
12 si alii potestatis vestrae participes sunt non potius nos sed non usi sumus hac potestate sed omnia sustinemus ne quod offendiculum demus evangelio Christi
Idan wadansu sun mori wannan 'yanci a gurin ku, ba mu fi su cancanta ba? duk da haka bamu yi amfani da wannan 'yancin ba, maimakon haka, mun yi jimriya da duk abin da zaya hana bisharar Yesu Almasihu.
13 nescitis quoniam qui in sacrario operantur quae de sacrario sunt edunt qui altario deserviunt cum altario participantur
Baku sani ba masu bauta a haikali suna samun abincinsu ne daga haikalin? Baku sani ba masu bauta a bagadi, suna da rabo daga abin da ake kawowa kan bagadin?
14 ita et Dominus ordinavit his qui evangelium adnuntiant de evangelio vivere
Haka kuma Ubangiji ya umarta masu aikin bishara zasu ci abincinsu ta hanyar bishara.
15 ego autem nullo horum usus sum non scripsi autem haec ut ita fiant in me bonum est enim mihi magis mori quam ut gloriam meam quis evacuet
Amma ban yi amfani da wannan 'yanci ba, ba kuma ina rubuta maku domin ayi mani wani abu bane, na gwanmace in mutu maimakon wani ya hana ni wannan fahariya.
16 nam si evangelizavero non est mihi gloria necessitas enim mihi incumbit vae enim mihi est si non evangelizavero
Ko nayi shelar bishara, ba ni da dalilin fahariya domin ya zama dole in yi. Kaito na idan ban yi shelar bishara ba
17 si enim volens hoc ago mercedem habeo si autem invitus dispensatio mihi credita est
Idan na yi hidimar nan da yardar zuciyata, ina da sakamako, idan kuma ba da yaddar zuciyata ba, harwa yau akwai nauwaya akai na.
18 quae est ergo merces mea ut evangelium praedicans sine sumptu ponam evangelium ut non abutar potestate mea in evangelio
To menene sakamako na? shi ne in yi shelar bishara kyauta, da haka ba zan yi amfani the 'yanci na cikin bishara ba
19 nam cum liber essem ex omnibus omnium me servum feci ut plures lucri facerem
Ko da shike ni 'yantacce ne ga duka, amma na mai da kaina bawan kowa domin in ribato masu yawa,
20 et factus sum Iudaeis tamquam Iudaeus ut Iudaeos lucrarer
Ga yahudawa, na zama bayahude, domin in ribato yahudawa, ga wadanda ke karkashin shari'a, na maishe kaina kamarsu, domin in ribato wadanda ke karkashinta. Na aikata wannan ko da shike bana karkashin shari'a
21 his qui sub lege sunt quasi sub lege essem cum ipse non essem sub lege ut eos qui sub lege erant lucri facerem his qui sine lege erant tamquam sine lege essem cum sine lege Dei non essem sed in lege essem Christi ut lucri facerem eos qui sine lege erant
Ga wadanda basu karkashin shari'a, na maishe kaina kamar su. Ko da shike ban rabu da shari'ar Allah ba. Amma ina karkashin dokar Almasihu. Na yi haka ne domin in ribato wadanda ba sa karkashin shari'a.
22 factus sum infirmis infirmus ut infirmos lucri facerem omnibus omnia factus sum ut omnes facerem salvos
Ga marasa karfi, na maishe kaina kamar marar karfi, domin in ribato raunana. Na mai da kaina dukan abu ga dukan mutane domin in sami zarafin da zan ribato wadansu zuwa ceto.
23 omnia autem facio propter evangelium ut particeps eius efficiar
Ina dukan abu sabili da bishara, domin kuma in sami albarkar da ke cikinta
24 nescitis quod hii qui in stadio currunt omnes quidem currunt sed unus accipit bravium sic currite ut conprehendatis
Baku sani ba mutane da dama suna shiga tsere amma daya neke karbar sakamakon, saboda haka ku yi tsere domin ku karbi sakamako.
25 omnis autem qui in agone contendit ab omnibus se abstinet et illi quidem ut corruptibilem coronam accipiant nos autem incorruptam
Dan wasa yana motsa jiki da kame kansa. Yana yi saboda ya karbi wannan sakamako mai lalacewa, amma muna tsere domin mu karbi sakamako marar lalacewa.
26 ego igitur sic curro non quasi in incertum sic pugno non quasi aerem verberans
Saboda haka ba na tsere ko fada haka nan kamar mai bugun iska.
27 sed castigo corpus meum et in servitutem redigo ne forte cum aliis praedicaverim ipse reprobus efficiar
Amma ina matse jiki na in maishe shi bawa, kada bayan na yi wa wadansu wa'azi ni kuma a karshe a fitar da ni.

< Corinthios I 9 >