< I Paralipomenon 4 >
1 filii Iuda Phares Esrom et Carmi et Ur et Subal
Zuriyoyin Yahuda su ne, Ferez, Hezron, Karmi, Hur da Shobal.
2 Reaia vero filius Subal genuit Ieth de quo nati sunt Ahimai et Laed hae cognationes Sarathi
Reyahiya ɗan Shobal shi ne mahaifin Yahat, Yahat shi ne mahaifin Ahumai da Lahad. Waɗannan su ne gidajen Zoratiyawa.
3 ista quoque stirps Hetam Iezrahel et Iesema et Iedebos nomenque sororis eorum Asalelphuni
Waɗannan su ne’ya’yan Etam. Yezireyel, Ishma da Idbash.’Yar’uwarsu ita ce Hazzelelfoni.
4 Phunihel autem pater Gedor et Ezer pater Osa isti sunt filii Ur primogeniti Ephrata patris Bethleem
Fenuwel shi ne mahaifin Gedor, kuma Ezer shi ne mahaifin Husha. Waɗannan su ne zuriyar Hur, ɗan farin Efrata da mahaifin Betlehem.
5 Asur vero patris Thecue erant duae uxores Halaa et Naara
Asshur mahaifin Tekowa yana da mata biyu, Hela da Na’ara.
6 peperit autem ei Naara Oozam et Epher et Themani et Asthari isti sunt filii Naara
Na’ara ta haifi Ahuzzam, Hefer, Temeni da Hawahashtari. Waɗannan su ne zuriyar Na’ara.
7 porro filii Halaa Sereth Isaar et Ethnan
’Ya’yan Hela maza su ne, Zeret, Zohar, Etnan,
8 Cos autem genuit Anob et Sobaba et cognationem Aral filii Arum
da Koz. Koz ne mahaifin Anub da Hazzobeba, shi ne kuma kakan iyalin da suka fito daga zuriyar Aharhel ɗan Harum.
9 fuit autem Iabes inclitus prae fratribus suis et mater eius vocavit nomen illius Iabes dicens quia peperi eum in dolore
Yabez ya fi’yan’uwansa martaba. Mahaifiyarsa ta sa masa suna Yabez, tana cewa, “Na haife shi da azaba.”
10 invocavit vero Iabes Deum Israhel dicens si benedicens benedixeris mihi et dilataveris terminos meos et fuerit manus tua mecum et feceris me a malitia non opprimi et praestitit Deus quae precatus est
Yabez ya yi kuka ga Allah na Isra’ila ya ce, “Ka yi mini albarka ka fadada yankina! Bari hannunka yă kasance tare da ni, yă kuma kiyaye ni daga abin da zai cuce ni, don kada in shiga wahala.” Sai Allah ya ji roƙonsa.
11 Chaleb autem frater Suaa genuit Machir qui fuit pater Esthon
Kelub, ɗan’uwan Shuha, shi ne mahaifin Mehir, wanda shi ne mahaifin Eshton.
12 porro Esthon genuit Bethrapha et Phesse et Thena patrem urbis Naas hii sunt viri Recha
Eshton shi ne mahaifin Bet-Rafa, Faseya da Tehinna wanda ya haifi Ir Nahash. Waɗannan su ne mutanen Reka.
13 filii autem Cenez Othonihel et Saraia porro filii Othonihel Athath
’Ya’yan Kenaz maza su ne, Otniyel da Serahiya.’Ya’yan Otniyel maza su ne, Hatat da Meyonotai.
14 et Maonathi genuit Ophra Saraias autem genuit Ioab patrem vallis Artificum ibi quippe artifices erant
Meyonotai shi ne mahaifin Ofra. Serahiya shi ne mahaifin Yowab, mahaifin Ge-Harashim. An kira shi haka domin mutanensa masu sana’ar hannu ne.
15 filii vero Chaleb filii Iephonne Hir et Hela et Nahem filiique Hela et Cenez
’Ya’yan Kaleb ɗan Yefunne maza su ne, Iru, Ela da Na’am. Ɗan Ela shi ne, Kenaz.
16 filii quoque Iallelel Ziph et Zipha Thiria et Asrahel
’Ya’yan Yahallelel su ne, Zif, Zifa, Tiriya da Asarel.
17 et filii Ezra Iether et Mered et Epher et Ialon genuitque Mariam et Sammai et Iesba patrem Esthamo
’Ya’yan Ezra maza su ne, Yeter, Mered, Efer da Yalon. Ɗaya daga cikin matan Mered ta haifi Miriyam, Shammai da Ishba wanda ya haifi Eshtemowa.
18 uxor quoque eius Iudaia peperit Iared patrem Gedor et Heber patrem Soccho et Hicuthihel patrem Zano hii autem filii Beththiae filiae Pharaonis quam accepit Mered
(Matarsa mutuniyar Yahuda kuwa ta haifi Yared mahaifin Gedor, Heber mahaifin Soko, da kuma Yekutiyel mahaifin Zanowa.) Waɗannan su ne’ya’yan Bitiya’yar Fir’auna, wadda Mered ya aura.
19 et filii uxoris Odaiae sororis Naham patris Ceila Garmi et Esthamo qui fuit de Machathi
’Ya’yan matar Hodiya,’yar’uwar Naham su ne, suka haifi Keyila Bagarme, da Eshtemowa mutumin Ma’aka.
20 filii quoque Simon Amnon et Rena filius Anan et Thilon et filii Iesi Zoeth et Benzoeth
’Ya’yan Shimon maza su ne, Amnon, Rinna, Ben-Hanan da Tilon. Zuriyar Ishi su ne, Zohet da Ben-Zohet.
21 filii Sela filii Iuda Her pater Lecha et Laada pater Maresa et cognationes Domus operantium byssum in domo Iuramenti
’Ya’yan Shela ɗan Yahuda maza su ne, Er mahaifin Leka, La’ada mahaifin Maresha da kuma gidajen masu aikin lilin a Bet-Ashbeya,
22 et Qui stare fecit solem virique Mendacii et Securus et Incendens qui principes fuerunt in Moab et qui reversi sunt in Leem haec autem verba vetera
da Yokim, mutanen Kozeba, da Yowash da Saraf wanda ya yi mulkin Mowab da kuma Yashubi Lehem (Waɗannan rubutattun tarihi ne na tun dā.)
23 hii sunt figuli habitantes in plantationibus et in praesepibus apud regem in operibus eius commoratique sunt ibi
Su ne maginan tukwane waɗanda suka zauna a Netayim da Gedera; sun zauna a can suka kuma yi wa sarki aiki.
24 filii Symeon Namuhel et Iamin Iarib Zara Saul
Zuriyar Simeyon su ne, Nemuwel, Yamin, Yarib, Zera da Shawulu;
25 Sellum filius eius Mabsam filius eius Masma filius eius
Shawulu ya haifi Shallum, Shallum ya haifi Mibsam. Mibsam ya haifi Mishma.
26 filii Masma Amuhel filius eius Zacchur filius eius Semei filius eius
Zuriyar Mishma su ne, Hammuwel ɗansa, wanda ya haifi Zakkur, shi Zakkur kuma ya haifi Shimeyi.
27 filii Semei sedecim et filiae sex fratres autem eius non habuerunt filios multos et universa cognatio non potuit adaequare summam filiorum Iuda
Shimeyi yana da’ya’ya maza goma sha shida da’ya’ya mata shida, amma’yan’uwansa ba su da’ya’ya da yawa; saboda haka gidansu gaba ɗaya ba tă zama mai mutane da yawa kamar mutanen Yahuda ba.
28 habitaverunt autem in Bersabee et Molada et Asarsual
Sun zauna a Beyersheba, Molada, Hazar Shuwal,
29 et in Ballaa et in Asom et in Tholad
Bilha, Ezem, Tolad
30 et in Bathuhel et in Orma et in Siceleg
Betuwel, Horma, Ziklag,
31 et in Bethmarchaboth et in Asarsusim et in Bethberai et in Saarim hae civitates eorum usque ad regem David
Bet-Markabot, Hazar-Susim, Bet-Biri da Sha’arayim. Waɗannan su ne garuruwansu har lokacin mulkin Dawuda.
32 villae quoque eorum Etham et Aen et Remmon et Thochen et Asan civitates quinque
Ƙauyukan da suke kewayensu su ne Etam, Ayin, Rimmon, Token da Ashan, garuruwa biyar;
33 et universi viculi eorum per circuitum civitatum istarum usque ad Baal haec est habitatio eorum et sedum distributio
da kuma dukan ƙauyuka kewaye da waɗannan garuruwa har zuwa Ba’al. Waɗannan ne wuraren zamansu. Suka kuma ajiye tarihin zuriya.
34 Masobab quoque et Iemlech et Iosa filius Amasiae
Zuriyar Simeyon ta ƙunshi Meshobab, da Yamlek, da Yosha ɗan Amaziya.
35 et Iohel et Ieu filius Iosabiae filii Saraiae filii Asihel
Akwai Yowel, da Yehu ɗan Yoshibiya. Yoshibiya ɗan Seraya ne. Serahiya kuma ɗan Asiyel ne.
36 et Helioenai et Iacoba et Isuaia et Asaia et Adihel et Isimihel et Banaia
Akwai Eliyohenai da Ya’akoba, da Yeshohahiya, da Asahiya, da Adiyel, da Yesimiyel, da Benahiya.
37 Ziza quoque filius Sephei filii Allon filii Idaia filii Semri filii Samaia
Akwai Ziza ɗan Shifi. Shifi ɗan Allon ne. Allon ɗan Yedahiya ne. Yedahiya ɗan Shimri ne. Shimri kuma ɗan Shemahiya ne.
38 isti sunt nominati principes in cognationibus suis et in domo adfinitatum suarum multiplicati sunt vehementer
Mutanen da aka jera sunayensu a bisa, shugabannin gidajensu ne. Iyalansu sun ƙaru sosai,
39 et profecti sunt ut ingrederentur in Gador usque ad orientem vallis et ut quaererent pascua gregibus suis
suka tafi bayan garin Gedor wajajen gabashin kwari suna neman makiyaya domin garkunansu.
40 inveneruntque pascuas uberes et valde bonas et terram latissimam et quietam et fertilem in qua ante habitaverunt de stirpe Ham
Suka sami makiyaya mai ciyawa mai kyau, ƙasar kuma tana da fāɗi, da salama, kuma zaman lafiya. A dā waɗansu mutanen Ham sun zauna a can.
41 hii ergo venerunt quos supra descripsimus nominatim in diebus Ezechiae regis Iuda et percusserunt tabernacula eorum et habitatores qui inventi fuerant ibi et deleverunt eos usque in praesentem diem habitaveruntque pro eis quoniam uberrimas ibidem pascuas reppererunt
Mutanen da aka jera sunayensu sun zo ne a zamanin Hezekiya sarkin Yahuda. Suka yaƙi mutanen Ham a wuraren zamansu, haka kuma suka yi da Meyunawa da suke can, suka hallaka su ƙaƙaf, yadda yake har yă zuwa yau. Sa’an nan suka zauna a wurin, gama akwai makiyaya domin garkunansu.
42 de filiis quoque Symeon abierunt in montem Seir viri quingenti habentes principes Phaltiam et Nahariam et Raphaiam et Ozihel filios Iesi
Mutum ɗari biyar na waɗannan mutane Simeyon, waɗanda Felatiya, Neyariya, Refahiya da Uzziyel,’ya’yan Ishi maza suka jagorance, sun mamaye ƙasar tudu ta Seyir.
43 et percusserunt reliquias quae evadere potuerant Amalechitarum et habitaverunt ibi pro eis usque ad diem hanc
Suka karkashe raguwar Amalekawan da suka tsere, suka kuma zauna a can har yă zuwa yau.