< Romanos 16 >
1 Commendo autem vobis Phoeben sororem nostram, quae est in ministerio Ecclesiae, quae est in Cenchris:
Ina gabatar muku da fibi 'yar'uwarmu, wanda take hidima a Ikilisiya dake cikin Kankiriya.
2 ut eam suscipiatis in Domino digne sanctis: et assistatis ei in quocumque negotio vestri indiguerit: etenim ipsa quoque astitit multis, et mihi ipsi.
Domin ku karbe ta cikin Ubangij. A hanyar da ta dace ga masu bada gaskiya, ku tsaya tare da ita cikin kowacce bukata. Domin ita da kanta ta zama da taimako ga masu yawa, har da ni ma.
3 Salutate Priscam, et Aquilam adiutores meos in Christo Iesu;
Ku gai da Bilkisu da Akila abokan aiki cikin Yesu Almasihu.
4 (qui pro anima mea suas cervices supposuerunt: quibus non solus ego gratias ago, sed et cunctae ecclesiae Gentium)
Wadanda sabo da ni suka sadaukar da ransu. Ina godiya garesu, ba ni kadai ba, amma kuma da dukan Ikilisiyoyin Al 'mmai.
5 et domesticam Ecclesiam eorum. Salutate Ephaenetum dilectum mihi, qui est primitivus Ecclesiae Asiae in Christo Iesu.
Gaida Ikilisiya da ke gidansu. Ku gai da Abainitas kaunataccena. Wanda shi ya fara bada gaskiya ga Almasihu a Asiya.
6 Salutate Mariam, quae multum laboravit in nobis.
Ku gai da Maryamu, wadda ta yi maku aiki tukuru.
7 Salutate Andronicum, et Iuliam cognatos, et concaptivos meos: qui sunt nobiles in Apostolis, qui et ante me fuerunt in Christo.
Ku gai da Andaranikas da Yuniyas, yan'uwana da abokan kurkukuna. Su sanannu ne cikin manzani, wadanda suke cikin Almasihu kafin ni.
8 Salutate Ampliatum dilectissimum mihi in Domino.
Ku gai da Amfiliyas kaunatace na cikin Ubangiji.
9 Salutate Urbanum adiutorem nostrum in Christo Iesu, et Stachyn dilectum meum.
Ku gai da Urbanas abokin aikinmu cikin Almasihu, da Istakis kaunataccena.
10 Salutate Apellen probum in Christo.
Ku gai da Abalis amintacce cikin Almasihu. Ku gai da wadanda su ke gidan Aristobulus.
11 Salutate eos, qui sunt ex Aristoboli domo. Salutate Herodionem cognatum meum. Salutate eos, qui sunt ex Narcissi domo, qui sunt in Domino.
Ku gai da Hirudiya, dan'uwa na, da wadanda ke gidan Narkissa, wadanda ke cikin Ubangiji.
12 Salutate Tryphaenam, et Tryphosam: quae laborant in Domino. Salutate Persidem charissimam, quae multum laboravit in Domino.
Ku gai da Tarafina daTarafusa, masu aikin Ubangiji.
13 Salutate Rufum electum in Domino, et matrem eius, et meam.
Ku gai da Barsisa kaunatacciya, wadda ta yi aikin Ubangiji da yawa. Ku gai da Rufas zababbe cikin Ubangiji da mamarsa da ni.
14 Salutate Asyncritum, Phlegontem, Hermam, Patrobam, Hermen: et qui cum eis sunt, fratres.
Ku gai da Asinkiritas da Filiguna da Hamis da Baturobas da Hamisu da kuma yan'uwa da ke tare da su.
15 Salutate Philologum, et Iuliam, Nereum, et sororem eius, et Olympiadem, et omnes, qui cum eis sunt, sanctos.
Ku gai da Filolugus daYuliya da Niriyas da yan'uwansa, da Ulumfas da kuma dukan tsarkaka da ke tare su.
16 Salutate invicem in osculo sancto. Salutant vos omnes Ecclesiae Christi.
Ku gaggai da juna da tsatsarkar sumba. Dukan Ikilisiyoyin Almasihu na gaishe ku.
17 Rogo autem vos fratres, ut observetis eos, qui dissensiones, et offendicula praeter doctrinam, quam vos didicistis, faciunt, et declinate ab illis.
Yanzu ina rokon ku, yan'wa, ku yi tunani fa game da masu kawo rabuwa da tuntube. Sabanin koyarwar da ku ka koya. Ku yi nesa da su.
18 Huiuscemodi enim Christo Domino nostro non serviunt, sed suo ventri: et per dulces sermones, et benedictiones seducunt corda innocentium.
Domin irin mutanen nan ba sa bauta wa Ubangiji Yesu, sai dai tumbinsu. Ta dadin bakinsu suke rudin zuciyar marasa laifi.
19 Vestra enim obedientia in omnem locum divulgata est. Gaudeo igitur in vobis. Sed volo vos sapientes esse in bono, et simplices in malo.
Domin rayuwar biyayyarku takai ga kunnen kowa, na yi farin ciki da ku, amma ina so ku zama da hikima game da abin ya ke mai kyau, ku zama marasa laifi ga abin da ke na mugunta.
20 Deus autem pacis conterat Satanam sub pedibus vestris velociter. Gratia Domini nostri Iesu Christi vobiscum.
Allah na salama zai sa ku tattake Shaidan da sauri kalkashin sawayen ku. Alherin Ubangijin mu Yesu Almasihu ya kasance tare da ku.
21 Salutat vos Timotheus adiutor meus, et Lucius, et Iason, et Sosipater cognati mei.
Timoti abokin aikina, yana gaishe ku, haka Lukiyas da Yason da Susibataras da kuma yan'uwana.
22 Saluto vos ego Tertius, qui scripsi epistolam, in Domino.
Ni Tartiyas wanda ya rubuta wasikan nan, na gaisheku cikin Ubangiji.
23 Salutat vos Caius hospes meus, et universa Ecclesia. Salutat vos Erastus archarius civitatis, et Quartus, frater.
Gayus mai masaukina da kuma dukan Ikilisiya, suna gaishe ku. Arastas ma'ajin birni na gaishe ku, da Kwartus dan'uwanmu.
24 Gratia Domini nostri Iesu Christi cum omnibus vobis. Amen.
Alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu ya kasance tare da ku dukka. Amin.
25 Ei autem, qui potens est vos confirmare iuxta Evangelium meum, et praedicationem Iesu Christi, secundum revelationem mysterii temporibus aeternis taciti, (aiōnios )
Yanzu ga wanda ke da Ikon karfafa ku bisa ga bisharata da wa'azin Yesu Almasihu, wanda ta gare shi ne aka bayyana asiran nan da suke boye tun da dadewa, (aiōnios )
26 (quod nunc patefactum est per Scripturas Prophetarum secundum praeceptum aeterni Dei, ad obeditionem fidei) in cunctis Gentibus cogniti, (aiōnios )
amma yanzu sanannu ne ta wurin litattafan Annabawa bisa umarnin Allah madauwami, domin biyayyar bangaskiya cikin Al'ummai dukka. (aiōnios )
27 soli sapienti Deo, per Iesum Christum, cui honor, et gloria in saecula saeculorum. Amen. (aiōn )
Ga Allah mai hikima kadai, ta wurin Yesu Almasihu daukaka ta tabbata har abada. Amin. (aiōn )