< Proverbiorum 1 >

1 Parabolae Salomonis, filii David, regis Israel.
Karin maganar Solomon ɗan Dawuda, sarkin Isra’ila.
2 Ad sciendam sapientiam, et disciplinam:
Ga karin magana da za su taimake ka don samun hikima da horo; don ganewa kalmomi masu zurfi;
3 ad intelligenda verba prudentiae: et suscipiendam eruditionem doctrinae, iustitiam, et iudicium, et aequitatem:
don neman rayuwa ta horo da kuma ta hankali, kana yin abin da yake daidai, mai adalci da kuma wanda ya dace;
4 ut detur parvulis astutia, adolescenti scientia, et intellectus.
don sa marar azanci yă yi hankali, yă sa matasa su sani, su kuma iya rarrabewa,
5 Audiens sapiens, sapientior erit: et intelligens, gubernacula possidebit.
bari masu hikima su saurara, su kuma ƙara ga saninsu, bari masu tunani kuma su sami jagora,
6 Animadvertet parabolam, et interpretationem, verba sapientum, et aenigmata eorum.
don su fahimci karin magana da kuma misalai, kalmomi da kuma kacici-kacici masu hikima.
7 Timor Domini principium sapientiae. Sapientiam, atque doctrinam stulti despiciunt.
Tsoron Ubangiji shi ne masomin ilimi, amma wawaye sun rena hikima da horo.
8 Audi, fili mi, disciplinam patris tui, et ne dimittas legem matris tuae:
Ɗana, ka saurari umarnin mahaifinka kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka.
9 ut addatur gratia capiti tuo, et torques collo tuo.
Za su zama kayan ado don su inganta ka da kuma sarƙar wuya don su yi wa wuyanka ado.
10 Fili mi, si te lactaverint peccatores, ne acquiescas eis.
Ɗana, in masu zunubi sun jarabce ka, kada ka yarda.
11 Si dixerint: Veni nobiscum, insidiemur sanguini, abscondamus tendiculas contra insontem frustra:
In suka ce, “Zo mu tafi; mu yi kwanton ɓauna, mu nemi wani mu kashe, mu fāɗa wa marasa laifi;
12 deglutiamus eum sicut infernus viventem, et integrum quasi descendentem in lacum. (Sheol h7585)
mu haɗiye su da rai gaba ɗaya kamar kabari, kamar waɗanda suke gangarawa zuwa rami; (Sheol h7585)
13 Omnem pretiosam substantiam reperiemus, implebimus domos nostras spoliis.
za mu sami dukiya masu daraja iri-iri, mu kuma cika gidajenmu da ganima;
14 Sortem mitte nobiscum, marsupium unum sit omnium nostrum.
ka haɗa kai da mu, za mu kuwa raba abin da muka sato”
15 Fili mi, ne ambules cum eis, prohibe pedem tuum a semitis eorum.
ɗana, kada ka tafi tare da su, kada ka taka ƙafarka a hanyarsu;
16 Pedes enim illorum ad malum currunt, et festinant ut effundant sanguinem.
gama ƙafafunsu kan yi sauri ga yin zunubi, suna saurin yin kisankai.
17 Frustra autem iacitur rete ante oculos pennatorum.
Ba shi da amfani a kafa tarko a idanun dukan tsuntsaye!
18 Ipsi quoque contra sanguinem suum insidiantur, et moliuntur fraudes contra animas suas.
Waɗannan irin mutane kansu suke kafa wa tarko; ba sa kama kome, sai rayukansu!
19 Sic semitae omnis avari, animas possidentium rapiunt.
Dukan waɗanda suke neman ribar da ba a samu a hanya mai kyau; ƙarshen wannan yakan ɗauke rayukansu.
20 Sapientia foris praedicat, in plateis dat vocem suam:
Hikima tana kira da ƙarfi a kan titi, tana ɗaga muryarta a dandalin taron jama’a;
21 in capite turbarum clamitat, in foribus portarum urbis profert verba sua, dicens:
tana kira da ƙarfi a kan tituna masu surutu, tana yin jawabinta a hanyoyin shiga gari.
22 Usquequo parvuli diligitis infantiam, et stulti ea, quae sibi sunt noxia, cupient, et imprudentes odibunt scientiam?
“Har yaushe ku da kuke marasa azanci za ku ci gaba a hanyoyinku marasa azanci? Har yaushe ku masu ba’a za ku yi ta murna cikin ba’arku wawaye kuma ku ƙi ilimi?
23 Convertimini ad correptionem meam: en proferam vobis spiritum meum, et ostendam vobis verba mea.
Da a ce kun saurari tsawatata, da na faɗa muku dukan abin da yake zuciyata in kuma sanar da ku tunanina.
24 Quia vocavi, et renuistis: extendi manum meam, et non fuit qui aspiceret.
Amma da yake kun ƙi ni sa’ad da na yi kira ba kuma wanda ya saurara sa’ad da na miƙa hannuna,
25 Despexistis omne consilium meum, et increpationes meas neglexistis.
da yake kun ƙi dukan shawarata ba ku kuma yarda da tsawatata ba,
26 Ego quoque in interitu vestro ridebo, et subsannabo, cum vobis id, quod timebatis, advenerit.
Zan yi muku dariya sa’ad da masifa ta same ku, zan yi muku ba’a sa’ad da bala’i ya same ku,
27 Cum irruerit repentina calamitas, et interitus quasi tempestas ingruerit: quando venerit super vos tribulatio, et angustia:
sa’ad da bala’i ya sha kanku kamar hadiri, sa’ad da masifa ta share ku kamar guguwa, sa’ad damuwa da wahala suka mamaye ku.
28 Tunc invocabunt me, et non exaudiam: mane consurgent, et non invenient me:
“Sa’an nan za su kira gare ni amma ba zan amsa ba; za su neme ni amma ba za su same ni ba.
29 eo quod exosam habuerint disciplinam, et timorem Domini non susceperint,
Da yake sun ƙi sani ba su kuwa zaɓi tsoron Ubangiji ba,
30 nec acquieverint consilio meo, et detraxerint universae correptioni meae.
da yake ba su karɓi shawarata ba suka kuwa yi kunnen ƙashi ga tsawatata,
31 Comedent igitur fructus viae suae, suisque consiliis saturabuntur.
za su sami sakayyar abubuwan da suka yi su kuma ƙoshi da sakayyar makircinsu.
32 Aversio parvulorum interficiet eos, et prosperitas stultorum perdet illos.
Gama rashin hankalin marasa azanci zai kashe su, rashin kulawar wawaye kuma zai hallaka su;
33 Qui autem me audierit, absque terrore requiescet, et abundantia perfruetur, timore malorum sublato.
amma duk wanda ya saurare ni, zai zauna lafiya yă kuma kasance da rai kwance, ba tare da tsoron lahani ba.”

< Proverbiorum 1 >