< Leviticus 2 >

1 Anima cum obtulerit oblationem sacrificii Domino, simila erit eius oblatio. fundetque super eam oleum, et ponet thus,
“‘Sa’ad da wani ya kawo hadaya ta gari ga Ubangiji, hadayarsa za tă zama gari mai laushi ne. Zai zuba mai a kai, yă sa turare a kansa
2 ac deferet ad filios Aaron sacerdotis: quorum unus tollet pugillum plenum similae et olei, ac totum thus, et ponet memoriale super altare in odorem suavissimum Domino.
yă kai wa’ya’yan Haruna maza waɗanda suke firistoci. Firist zai ɗiba gari mai laushin a tafin hannu da kuma man, tare da dukan turaren, yă ƙone wannan a sashen tunawa a kan bagade, hadaya ce da aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
3 quod autem reliquum fuerit de sacrificio, erit Aaron et filiorum eius, Sanctum sanctorum de oblationibus Domini.
Sauran hadaya ta garin zai zama na Haruna da’ya’yansa; sashe mafi tsarki ne na hadayar da aka yi ga Ubangiji ta wuta.
4 Cum autem obtuleris sacrificium coctum in clibano: de simila, panes scilicet absque fermento, conspersos oleo, et lagana azyma oleo lita.
“‘In kuka kawo toyayyen hadayar gari da aka yi daga matoya, zai ƙunshi gari mai laushi, toyayye ba tare da yisti ba, gauraye kuma da mai, ko kuwa ƙosai da aka yi ba tare da yisti ba, aka kuma kwaɓa da mai.
5 Si oblatio tua fuerit de sartagine, similae conspersae oleo et absque fermento,
In an toya hadaya ta garinku a kasko, sai a yi shi da gari mai laushi haɗe da mai, ba kuwa da yisti ba.
6 divides eam minutatim, et fundes super eam oleum.
A gutsuttsura shi, a zuba mai a kansa, hadaya ce ta hatsi.
7 Sin autem de craticula fuerit sacrificium, aeque simila oleo conspergetur:
In hadayarku ta hatsin da aka dafa ne a tukunya, sai a yi shi da gari mai laushi da kuma mai.
8 quam offerens Domino, trades manibus sacerdotis.
A kawo hatsin da aka yi da waɗannan abubuwa ga Ubangiji; a ba wa firist wanda zai ɗauka yă kai bagade.
9 Qui cum obtulerit eam, tollet memoriale de sacrificio, et adolebit super altare in odorem suavitatis Domino,
Zai fid da sashen tunawa daga hadaya ta gari, yă ƙone shi a kan bagade kamar hadayar da ka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
10 quidquid autem reliquum est, erit Aaron, et filiorum eius, Sanctum sanctorum de oblationibus Domini.
Sauran hadaya ta garin za tă zama ta Haruna da’ya’yansa; sashe mafi tsarki ne na hadayun da aka yi ga Ubangiji ta wuta.
11 Omnis oblatio, quae offeretur Domino, absque fermento fiet, nec quidquam fermenti aut mellis adolebitur in sacrificio Domini.
“‘Kowace hadaya ta garin da kuka kawo ga Ubangiji, dole a yi shi ba tare da yisti ba, gama ba za ku ƙone wani yisti, ko zuma a cikin hadayar da aka yi ga Ubangiji ta wuta ba.
12 Primitias tantum eorum offeretis ac munera: super altare vero non imponentur in odorem suavitatis.
Za ku iya kawo su ga Ubangiji kamar hadaya ta’ya’yan fari, amma ba za a miƙa su a bagade kamar turare mai ƙanshi ba.
13 Quidquid obtuleris sacrificii, sale condies, nec auferes sal foederis Dei tui de sacrificio tuo. In omni oblatione offeres sal.
A sa gishiri a dukan hadayunku na hatsi. Kada a rasa sa gishirin alkawari na Allahnku a hadayunku na hatsi, a sa gishiri a dukan hadayunku.
14 Si autem obtuleris munus primarum frugum tuarum Domino de spicis adhuc virentibus, torrebis eas igni, et confringes in morem farris, et sic offeres primitias tuas Domino,
“‘In kuka kawo hadaya ta gari na’ya’yan fari ga Ubangiji, sai ku miƙa ɓarzajjen kawunan sabon hatsin da aka gasa a wuta.
15 fundens super ea oleum, et tus imponens, quia oblatio Domini est.
A sa mai da turare a kansa, hadaya ce ta hatsi.
16 de qua adolebit sacerdos in memoriam muneris partem farris fracti, et olei, ac totum tus.
Firist zai ƙone sashe na ɓarzajjen hatsin da kuma mai, tare da turare don tunawa, gama hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.

< Leviticus 2 >