< Leviticus 10 >

1 Arreptisque Nadab, et Abiu filii Aaron thuribulis, posuerunt ignem, et incensum desuper, offerentes coram Domino ignem alienum: quod eis praeceptum non erat.
’Ya’yan Haruna maza, Nadab da Abihu suka ɗauki farantansu, suka sa wuta a ciki, suka zuba turare a kai; suka kuma miƙa haramtacciyar wuta a gaban Ubangiji, ba irin wadda Ubangiji ya umarta ba.
2 Egressusque ignis a Domino, devoravit eos, et mortui sunt coram Domino.
Sai wuta ta fito daga Ubangiji ta cinye su, suka kuma mutu a gaban Ubangiji.
3 Dixitque Moyses ad Aaron: Hoc est quod locutus est Dominus: Sanctificabor in iis, qui appropinquant mihi, et in conspectu omnis populi glorificabor. Quod audiens tacuit Aaron.
Sai Musa ya ce Haruna, “Ga abin da Ubangiji yake nufi sa’ad da ya ce, “‘A cikin waɗanda suka kusace ni za a tabbata ni mai tsarki ne; a fuskar dukan mutane za a kuwa girmama ni.’” Haruna ya yi shiru.
4 Vocatis autem Moyses Misaele, et Elisaphan filiis Oziel, patrui Aaron, ait ad eos: Ite et tollite fratres vestros de conspectu Sanctuarii, et asportate extra castra.
Sai Musa ya kira Mishayel da Elzafan,’ya’yan Uzziyel kawun Haruna, ya ce musu, “Ku zo nan; ku ɗauki’yan’uwanku waje da sansani, daga gaban wuri mai tsarki.”
5 Confestimque pergentes, tulerunt eos sicut iacebant, vestitos lineis tunicis, et eiecerunt foras, ut sibi fuerat imperatum.
Sai suka zo suka ɗauke su, suna nan cikin taguwoyinsu, zuwa waje da sansani yadda Musa ya umarta.
6 Locutusque est Moyses ad Aaron, et ad Eleazar, et Ithamar filios eius: Capita vestra nolite nudare, et vestimenta nolite scindere, ne forte moriamini, et super omnem coetum oriatur indignatio. Fratres vestri, et omnis domus Israel plangant incendium quod Dominus suscitavit:
Sa’an nan Musa ya ce wa Haruna da Eleyazar da Itamar’ya’yansa maza, “Kada ku bar gashin kanku barkatai, kada kuma ku yage tufafinku, don kada ku mutu. Yin haka zai jawo fushin Ubangiji a kan dukan jama’a. Amma dangoginku, wato, dukan Isra’ilawa, suna iya kuka saboda waɗanda Ubangiji ya hallaka da wuta.
7 vos autem non egrediemini fores tabernaculi, alioquin peribitis: oleum quippe sanctae unctionis est super vos. Qui fecerunt omnia iuxta praeceptum Moysi.
Kada ku bar ƙofar Tentin Sujada ko kuwa ku mutu, domin man Shafan Ubangiji yana kanku.” Saboda haka suka yi kamar yadda Musa ya faɗa.
8 Dixitque Dominus ad Aaron:
Sa’an nan Ubangiji ya yi magana da Haruna ya ce,
9 Vinum, et omne quod inebriare potest, non bibetis tu et filii tui, quando intrabitis in tabernaculum testimonii, ne moriamini: quia praeceptum sempiternum est in generationes vestras.
“Kai da’ya’yanka maza, ba za ku sha ruwan inabi ko wani abu mai sa jiri ba a duk sa’ad da za ku shiga cikin Tentin Sujada, in ba haka ba za ku mutu. Wannan dawwammamiyar farilla ce wa tsararraki masu zuwa.
10 Et ut habeatis scientiam discernendi inter sanctum et profanum, inter pollutum et mundum:
Dole ku bambanta tsakanin mai tsarki da marar tsarki, tsakanin marar tsabta da mai tsabta,
11 doceatisque filios Israel omnia legitima mea quae locutus est Dominus ad eos per manum Moysi.
za ku kuma koyar da Isra’ilawa dukan farillan da Ubangiji ya ba su ta wurin Musa.”
12 Locutusque est Moyses ad Aaron, et ad Eleazar, et Ithamar filios eius, qui erant residui: Tollite sacrificium, quod remansit de oblatione Domini, et comedite illud absque fermento iuxta altare, quia Sanctum sanctorum est.
Musa ya ce wa Haruna da Eleyazar da Itamar’ya’yansa maza da suka ragu, “Ku ɗauki ragowar hadaya ta gari wadda aka yi hadaya ta ƙonawa da ita ga Ubangiji ku ci ba tare da yisti ba, a gefen bagaden, gama tsattsarka ne.
13 Comedetis autem in loco sancto: quod datum est tibi et filiis tuis de oblationibus Domini, sicut praeceptum est mihi.
Ku ci shi a tsattsarkan wuri, gama rabonka ne da na’ya’yanka daga cikin hadayun da akan ƙone da wuta ga Ubangiji; gama haka aka umarce ni.
14 Pectusculum quoque quod oblatum est, et armum qui separatus est, edetis in loco mundissimo tu et filii tui, et filiae tuae tecum. tibi enim ac liberis tuis reposita sunt de hostiis salutaribus filiorum Israel:
Amma kai da’ya’yanka maza da mata za su iya ci ƙirjin da aka kaɗa, da kuma cinyar da aka miƙa. Ku ci su a wuri mai tsabta; an ba da su gare ku da kuma’ya’yanku a matsayin rabo daga hadaya ta salama ta Isra’ilawa.
15 eo quod armum et pectus, et adipes qui cremantur in altari, elevaverunt coram Domino, et pertineant ad te, et ad filios tuos lege perpetua, sicut praecepit Dominus.
Cinyar da aka miƙa da kuma ƙirjin da aka kaɗa, dole a kawo su tare da ɓangarori kitsen hadayun da aka yi ta wuri wuta, don a kaɗa a gaban Ubangiji a matsayin hadaya ta kaɗawa. Wannan zai zama na kullayaumi gare ka da’ya’yanka, yadda Ubangiji ya umarta.”
16 Inter haec, hircum, qui oblatus fuerat pro peccato, cum quaereret Moyses, exustum reperit: iratusque contra Eleazar et Ithamar filios Aaron, qui remanserant, ait:
Sa’ad da Musa ya nemi sani game da akuyar hadaya don zunubi, ya kuwa gane cewa an ƙone shi, sai ya yi fushi da Eleyazar da kuma Itamar,’ya’yan Haruna maza da suka ragu, ya kuma yi tambaya,
17 Cur non comedistis hostiam pro peccato in loco sancto, quae Sancta sanctorum est, et data vobis ut portetis iniquitatem multitudinis, et rogetis pro ea in conspectu Domini,
“Me ya sa ba ku ci hadaya don zunubi a cikin wuri mai tsarki ba? Mafi tsaki ne; an ba ku ne don a ɗauke laifin jama’a ta wurin yin kafara saboda su a gaban Ubangiji.
18 praesertim cum de sanguine illius non sit illatum intra sancta, et comedere debueratis eam in Sanctuario, sicut praeceptum est mihi?
Da yake ba a kai jininsa cikin wuri mai tsarki ba, ya kamata ku ci akuyar a wuri mai tsarki, kamar yadda na umarta.”
19 Respondit Aaron: Oblata est hodie victima pro peccato, et holocaustum coram Domino: mihi autem accidit quod vides. quomodo potui comedere eam, aut placere Domino in ceremoniis mente lugubri?
Sai Haruna ya amsa wa Musa, “Yau sun miƙa hadayarsu don zunubi da kuma hadayarsu ta ƙonawa a gaban Ubangiji, ga kuma irin waɗannan abubuwa da suka same ni, da a ce na ci hadaya don zunubi yau, da zai yi kyau ke nan a gaban Ubangiji?”
20 Quod cum audisset Moyses, recepit satisfactionem.
Da Musa ya ji haka, sai ya gamsu.

< Leviticus 10 >