< Jonas Propheta 4 >
1 Et afflictus est Ionas afflictione magna, et iratus est:
Sai abin ya ɓata wa Yunana rai ƙwarai har ya yi fushi.
2 et oravit ad Dominum, et dixit: Obsecro Domine, numquid non hoc est verbum meum, cum adhuc essem in terra mea? propter hoc praeoccupavi ut fugerem in Tharsis. scio enim quia tu Deus clemens, et misericors es, patiens, et multae miserationis, et ignoscens super malitia.
Sai ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji, ba irin abin da na faɗa ke nan ba tun ina gida? Wannan ne ya sa na yi ƙoƙarin tserewa zuwa Tarshish. Ai, na sani kai Allah ne mai alheri da tausayi, mai jinkirin fushi da cikakkiyar ƙauna, kai Allah ne mai dakatar da nufinka na yin hukunci.
3 Et nunc Domine tolle quaeso animam meam a me: quia melior est mihi mors quam vita.
Yanzu, ya Ubangiji, ka ɗauki raina, domin ya fi sauƙi a gare ni in mutu da in rayu.”
4 Et dixit Dominus: Putasne bene irasceris tu?
Amma Ubangiji ya amsa, ya ce; “Daidai ne ka yi fushi?”
5 Et egressus est Ionas de civitate, et sedit contra Orientem civitatis: et fecit sibimet umbraculum ibi, et sedebat subter illud in umbra, donec videret quid accideret civitati.
Sai Yunana ya fita daga birnin ya yi wajen gabas, ya zauna. A nan ya yi wa kansa rumfa, ya zauna cikin inuwarta yana jira yă ga abin da zai sami birnin.
6 Et praeparavit Dominus Deus hederam, et ascendit super caput Ionae, ut esset umbra super caput eius, et protegeret eum: laboraverat enim: et laetatus est Ionas super hedera, laetitia magna.
Sai Ubangiji Allah ya sa wata’yar kuringa ta tsiro, ta yi girma a inda Yunana yake, don ta inuwantar da shi, yă ji daɗi. Yunana kuwa ya yi murna matuƙa da wannan kuringa.
7 Et paravit Deus vermen ascensu diluculi in crastinum: et percussit hederam, et exaruit.
Amma kashegari da safe sai Allah ya sa tsutsa ta cinye’yar kuringar har ta mutu.
8 Et cum ortus fuisset sol, praecepit Dominus vento calido, et urenti: et percussit sol super caput Ionae, et aestuabat: et petivit animae suae ut moreretur, et dixit: Melius est mihi mori, quam vivere.
Sa’ad da rana ta yi sama, sai Allah ya sa iskar gabas mai zafi ta huro, zafin ranar kuma ya buga kan Yunana, har ya ji sai ka ce zai suma. Ya so a ce ya mutu ma, sai ya ce, “Gara in mutu da a ce ina zaune da rai.”
9 Et dixit Dominus ad Ionam: Putasne bene irasceris tu super hedera? Et dixit: Bene irascor ego usque ad mortem.
Amma Allah ya ce wa Yunana, “Daidai ne ka yi fushi saboda wannan kuringa?” Sai Yunana ya ce, “I, daidai ne, ina fushi matuƙa, har ina so da na mutu ma.”
10 Et dixit Dominus: Tu doles super hederam, in qua non laborasti, neque fecisti ut cresceret. quae sub una nocte nata est, et sub una nocte periit.
Sai Ubangiji ya ce, “Ai, wannan kuringa ta tsira dare ɗaya ta kuma ɓace kafin dare na biyu, ba ka yi wata wahala dominta ba, ba kai ne ka sa ta yi girma ba, duk da haka ranka ya ɓace saboda ita.
11 Et ego non parcam Ninive civitati magnae, in qua sunt plus quam centum viginti millia hominum, qui nesciunt quid sit inter dexteram et sinistram suam, et iumenta multa?
Ashe, ba dole ne in ji tausayin babban birnin nan Ninebe mai mutum sama da dubu ɗari da ashirin marasa alhaki, da kuma dabbobi masu yawa ba?”