< Jeremiæ 21 >

1 Verbum, quod factum est ad Ieremiam a Domino, quando misit ad eum rex Sedechias Phassur filium Melchiae, et Sophoniam filium Maasiae sacerdotem, dicens:
Magana ta zo wa Irmiya daga Ubangiji sa’ad da Sarki Zedekiya ya aiki Fashhur ɗan Malkiya da firist Zefaniya ɗan Ma’asehiya gare shi. Suka ce masa,
2 Interroga pro nobis Dominum, quia Nabuchodonosor rex Babylonis praeliatur adversum nos: si forte faciat Dominus nobiscum secundum omnia mirabilia sua, et recedat a nobis.
“Yanzu ka roƙi mana Ubangiji saboda Nebukadnezzar sarkin Babilon yana kawo mana yaƙi. Wataƙila Ubangiji zai yi mana waɗansu abubuwa banmamaki kamar a lokacin baya don yă janye daga gare mu.”
3 Et dixit Ieremias ad eos: Sic dicetis Sedechiae:
Amma Irmiya ya amsa musu ya ce, “Ku faɗa wa Zedekiya cewa,
4 Haec dicit Dominus Deus Israel: Ecce ego convertam vasa belli, quae in manibus vestris sunt, et quibus vos pugnatis adversum regem Babylonis, et Chaldaeos, qui obsident vos in circuitu murorum: et congregabo ea in medio civitatis huius.
‘Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yake cewa ina shirin juya kayan yaƙin da suke a hannuwanka a kanka, waɗanda kake amfani don ka yaƙi sarki Babilon da kuma Babiloniyawa waɗanda suka kewaye katangar birnin, zan kuwa tsiba kayan yaƙinka a tsakiyar birnin nan.
5 Et debellabo ego vos in manu extenta, et in brachio forti, et in furore, et in indignatione, et in ira grandi.
Ni da kaina zan yi yaƙi da kai da miƙaƙƙen hannu mai ƙarfi cikin fushi da hasala mai girma.
6 Et percutiam habitatores civitatis huius, homines et bestiae pestilentia magna morientur.
Zan kashe waɗanda suke zaune a wannan birni, mutane da dabbobi za su kuwa mutu da muguwar annoba.
7 Et post haec ait Dominus: dabo Sedechiam regem Iuda, et servos eius, et populum eius, et qui derelicti sunt in civitate hac a peste et gladio, et fame, in manu Nabuchodonosor regis Babylonis, et in manu inimicorum eorum, et in manu quaerentium animam eorum, et percutiet eos in ore gladii, et non flectetur, neque parcet, nec miserebitur.
Bayan wannan, in ji Ubangiji, zan ba da Zedekiya sarkin Yahuda, fadawansa da kuma mutanen wannan birni waɗanda suka tsira daga annoba, takobi da kuma yunwa, ga Nebukadnezzar sarkin Babilon da kuma ga abokan gābansu waɗanda suke neman ransu. Zai kashe su da takobi; ba zai ji tausayinsu ko ya yi musu jinƙai ko ya yi juyayinsu ba.’
8 Et ad populum hunc dices: Haec dicit Dominus: Ecce ego do coram vobis viam vitae, et viam mortis.
“Bugu da ƙari, ka faɗa wa mutanen cewa, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, ga shi na sa a gabanku hanyar rai da hanyar mutuwa.
9 Qui habitaverit in urbe hac, morietur gladio, et fame, et peste: qui autem egressus fuerit, et transfugerit ad Chaldaeos, qui obsident vos, vivet, et erit ei anima sua, quasi spolium.
Duk wanda ya zauna a wannan birni zai mutu ta takobi, yunwa ko annoba. Amma duk wanda ya fita ya miƙa kansa ga Babiloniyawa waɗanda suka kewaye ku zai rayu; zai kuɓutar da ransa.
10 Posui enim faciem meam super civitatem hanc in malum, et non in bonum, ait Dominus: in manu regis Babylonis dabitur, et exuret eam igni.
Na ƙudura in yi wa wannan birni lahani ba alheri ba, in ji Ubangiji. Za a ba da shi a hannuwan sarki Babilon, zai kuwa hallaka shi da wuta.’
11 Et domui regis Iuda: Audite verba Domini,
“Ban haka ma, ka faɗa wa gidan sarauta na Yahuda cewa, ‘Ku saurari maganar Ubangiji;
12 domus David, haec dicit Dominus: Iudicate mane iudicium, et eruite vi oppressum de manu calumniantis: ne forte egrediatur ut ignis indignatio mea, et succendatur, et non sit qui extinguat propter malitiam studiorum vestrorum.
Ya gidan Dawuda ga abin da Ubangiji yana cewa, “‘Ku yi gaskiya kowace safiya; ku kuɓuta daga hannun mai danniya wannan da aka yi wa fashi in ba haka ba hasalata za tă sauka ta kuma ci kamar wuta saboda muguntar da kuka aikata za tă ci babu wanda zai kashe ta.
13 Ecce ego ad te habitatricem vallis solidae atque campestris, ait Dominus: qui dicitis: Quis percutiet nos? et quis ingredietur domos nostras?
Ina gāba da ku, mazaunan Urushalima, ku da kuke zama a bisa wannan kwari kan dutsen da yake a fili, in ji Ubangiji ku da kuke cewa, “Wa zai iya yaƙe mu? Wa zai iya shiga mafakarmu?”
14 Et visitabo super vos iuxta fructum studiorum vestrorum, dicit Dominus: et succendam ignem in saltu eius: et devorabit omnia in circuitu eius.
Zan hukunta ku gwargwadon ayyukanku, in ji Ubangiji. Zan sa wuta a kurminku da za tă cinye kome da yake kewaye da ku.’”

< Jeremiæ 21 >