< Hiezechielis Prophetæ 45 >

1 Cumque coeperitis terram dividere sortito, separate primitias Domino, sanctificatum de terra, longitudine vigintiquinque millia, et latitudine decem millia: sanctificatum erit in omni termino eius per circuitum.
“‘Sa’ad da kuka rarraba ƙasar gādo, ku miƙa wa Ubangiji rabon ƙasar ya zama yanki mai tsarki, tsawonsa ya zama kamu 25,000 fāɗinsa kuma ya zama 20,000, dukan ƙasar za tă zama mai tsarki.
2 Et erit ex omni parte sanctificatum quingentos per quingentos, quadrifariam per circuitum: et quinquaginta cubitis in suburbana eius per gyrum.
Daga cikin wannan, sashe guda da yake murabba’i mai tsawo kamu 500 zai zama don wuri mai tsarki, kamu 50 kewaye da shi zai zama fili.
3 Et a mensura ista mensurabis longitudinem vigintiquinque millium, et latitudinem decem millium, et in ipso erit templum, sanctumque sanctorum.
A cikin yanki mai tsarki, ka auna tsawo kamu 25,000 da kuma fāɗi kamu 10,000. A cikinsa wuri mai tsarki zai kasance, Wuri Mafi Tsarki.
4 Sanctificatum de terra erit sacerdotibus ministris sanctuarii, qui accedunt ad ministerium Domini: et erit eis locus in domos, et in sanctuarium sanctitatis.
Zai zama tsattsarkan rabo na ƙasa domin firistoci, waɗanda za su yi hidima a cikin wuri mai tsarki da kuma waɗanda za su zo kusa don su yi hidima a gaban Ubangiji. Zai zama wuri don gidajensu ya kuma zama tsattsarkan wuri saboda wuri mai tsarki.
5 Vigintiquinque autem millia longitudinis, et decem millia latitudinis erunt Levitis, qui ministrant domui: ipsi possidebunt viginti gazophylacia.
Wani sashi kuma mai tsawo kamu 25,000 da fāɗi 10,000 zai zama na Lawiyawa, waɗanda suke hidima a cikin haikali, zai zama mallakarsu don su zauna a ciki.
6 Et possessionem civitatis dabitis quinque millia latitudinis, et longitudinis vigintiquinque millia secundum separationem sanctuarii, omni domui Israel.
“‘Za ka ba wa birnin fāɗin mallakarsa kamu 5,000, tsawonsa kuma 25,000, haɗe da tsattsarkan rabo; zai kasance na gidan Isra’ila duka.
7 Principi quoque hinc et inde in separationem sanctuarii, et in possessionem civitatis, contra faciem separationis sanctuarii, et contra faciem possessionis urbis: a latere Maris usque ad Mare, et a latere Orientis usque ad Orientem: Longitudinis autem iuxta unamquamque partem a termino Occidentali usque ad terminum Orientalem.
“‘Sarki zai kasance da fili da ya yi iyaka da kowane gefe na yankin wuri mai tsarki da kuma mallakar birnin. Zai miƙe ya yi wajen yamma daga gefen yamma ya kuma yi wajen gabas daga gefen gabas, yana miƙewa a tsawo daga wajen yamma zuwa wajen gabashin iyaka don yă yi hannun riga da rabon kabilan.
8 De terra erit ei possessio in Israel: et non depopulabuntur ultra principes populum meum: sed terram dabunt domui Israel secundum tribus eorum.
Wannan fili zai zama mallakarsa a Isra’ila. Kuma sarakunana ba za su ƙara zaluntar mutanena ba amma za su bar gidan Isra’ila ya mallaki ƙasar bisa ga kabilansu.
9 Haec dicit Dominus Deus: Sufficiat vobis principes Israel: iniquitatem et rapinas intermittite, et iudicium et iustitiam facite, separate confinia vestra a populo meo, ait Dominus Deus.
“‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko na ce ku sarakunan Isra’ila, danniya da zaluncin da kuke yi sun isa! Ku yi shari’a bisa ga gaskiya da adalci, ku bar korar mutanena, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
10 Statera iusta, et ephi iustum, et batus iustus erit vobis.
Ku yi amfani da garwan da yake daidai, efa da yake daidai da kuma garwa da yake daidai.
11 Ephi, et batus aequalia, et unius mensurae erunt: ut capiat decimam partem cori batus, et decimam partem cori ephi: iuxta mensuram cori erit aequa libratio eorum.
Efa da garwan su kasance girmansu ɗaya, garwan ya zama kashi ɗaya bisa goma na ganga efa kuma ya zama kashi ɗaya bisa goma na ganga; ganga fitaccen ma’auni na duka biyu.
12 Siclus autem viginti obolos habet. Porro viginti sicli, et vigintiquinque sicli, et quindecim sicli, mnam faciunt.
Shekel zai kasance da gera ashirin. Shekel ashirin a haɗa da shekel ashirin da biyar a haɗa da shekel goma sha biyar zai zama mina guda.
13 Et hae sunt primitiae, quas tolletis: sextam partem ephi de coro frumenti, et sextam partem ephi de coro hordei.
“‘Wannan ita ce bayarwa ta musamman da za ku miƙa, kashi ɗaya bisa shida na efa daga kowace gangan alkama da kashi ɗaya bisa shida na efa daga kowace gangan sha’ir.
14 Mensura quoque olei, batus olei, decima pars cori est: et decem bati corum faciunt: quia decem bati implent corum.
Sashe na man da aka ƙayyade, da aka auna da garwa, kashi ɗaya bisa goma ne na garwa daga ganga (wanda yakan ci garwa goma, gama garwa goma suna daidai da ganga guda).
15 Et arietem unum de grege ducentorum de his, quae nutriunt Israel in sacrificium, et in holocaustum, et in pacifica, ad expiandum pro eis, ait Dominus Deus.
A kuma ba da tunkiya daga kowane garke mai tumaki ɗari biyu daga makiyaya da aka yi masa banruwa sosai na Isra’ila. Za a yi amfani da waɗannan don hadayun gari, hadayun ƙonawa da hadayun salama don yin kafara saboda mutane, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
16 Omnis populus terrae tenebitur primitiis his principi in Israel.
Dukan mutanen ƙasar za su yi wannan bayarwa ta musamman saboda amfanin sarki a Isra’ila.
17 Et super principem erunt holocausta, et sacrificium, et libamina in sollemnitatibus, et in Calendis, et in Sabbatis, et in universis sollemnitatibus domus Israel: ipse faciet pro peccato sacrificium, et holocaustum, et pacifica ad expiandum pro domo Israel.
Zai zama hakkin sarki ne ya tanada hadayu na ƙonawa, hadayu na gari da hadayu na sha a bukukkuwa, Sabuwar Wata da Asabbatai, a duk ƙayyadaddun bukukkuwa na gidan Isra’ila. Zai tanada hadayu don zunubi, hadayu na gari, hadayu na ƙonawa da hadayu na salama don yin kafara saboda gidan Isra’ila.
18 Haec dicit Dominus Deus: In primo mense, una mensis sumes vitulum de armento immaculatum, et expiabis sanctuarium.
“‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a farkon wata a rana ta fari za ku ba da ɗan bijimi marar lahani a kuma tsarkake wuri mai tsarki.
19 Et tollet sacerdos de sanguine quod erit pro peccato: et ponet in postibus domus, et in quattuor angulis crepidinis altaris, et in postibus portae atrii interioris.
Firist zai ɗibi jinin hadaya don zunubi ya shafa a madogaran ƙofar haikali, a kusurwoyi huɗu na gefen bisa na bagade da kuma a kan madogaran ƙofar shiga na fili na can ciki.
20 Et sic facies in septima mensis pro unoquoque, qui ignoravit, et errore deceptus est, et expiabis pro domo.
Za ku yi haka kuma a rana ta bakwai ga watan domin duk wanda ya yi zunubai ba da gangan ba ko ta wurin rashin sani; saboda haka sai ku yi kafara domin haikalin.
21 In primo mense, quartadecima die mensis erit vobis Paschae sollemnitas: septem diebus azyma comedentur.
“‘A wata na fari a rana ta goma sha huɗu za ku kiyaye Bikin Ƙetarewa, bikin da yakan ɗauki kwana bakwai, a lokacin ne za ku riƙa cin burodi marar yisti.
22 Et faciet princeps in die illa pro se, et pro universo populo terrae, vitulum pro peccato.
A wannan rana sarki zai tanada bijimi a matsayin hadaya don zunubi domin kansa da kuma domin dukan mutanen ƙasar.
23 Et in septem dierum sollemnitate faciet holocaustum Domino septem vitulos, et septem arietes immaculatos quotidie septem diebus: et pro peccato hircum caprarum quotidie.
Kowace rana a kwanaki bakwai na Bikin zai tanada bijimai guda bakwai da raguna bakwai marar lahani a matsayi hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji, da kuma bunsuru saboda hadaya don zunubi.
24 Et sacrificium ephi per vitulum, et ephi per arietem faciet: et olei hin per singula ephi.
Zai tanada efa na gari don kowane bijimi da kuma efa don kowane rago, tare da kwalabar mai don kowane efa guda.
25 Septimo mense, quintadecima die mensis in sollemnitate faciet sicut supra dicta sunt per septem dies: tam pro peccato, quam pro holocausto, et in sacrificio, et in oleo.
“‘A lokacin kwana bakwai na Bikin, waɗanda za su fara a wata na bakwai a rana ta goma sha biyar, zai ba da abubuwan nan saboda hadayu don zunubi, hadayu na ƙonawa, hadayu na gari da kuma mai.

< Hiezechielis Prophetæ 45 >