< Hiezechielis Prophetæ 21 >
1 Et factus est sermo Domini ad me, dicens:
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
2 Fili hominis pone faciem tuam ad Ierusalem, et stilla ad sanctuaria, et propheta contra humum Israel:
“Ɗan mutum, ka kafa fuskarka gāba da Urushalima ka kuma yi wa’azi a kan wuri mai tsarki. Ka yi annabci gāba da ƙasar Isra’ila
3 Et dices terrae Israel: Haec dicit Dominus Deus: Ecce ego ad te, et eiiciam gladium meum de vagina sua, et occidam in te iustum, et impium.
ka faɗa mata, ‘Ga abin da Ubangiji ya ce ina gāba da ke. Zan ja takobina daga kubensa in karkashe adalai da mugaye daga cikinki.
4 Pro eo autem quod occidi in te iustum, et impium, idcirco egredietur gladius meus de vagina sua ad omnem carnem ab Austro usque ad Aquilonem:
Domin zan karkashe adalai da kuma mugaye, ba zan rufe takobina a kan kowa daga kudu zuwa arewa ba.
5 Ut sciat omnis caro quia ego Dominus eduxi gladium meum de vagina sua irrevocabilem.
Sa’an nan duka mutane za su san cewa Ni Ubangiji na ja takobina daga kubensa; ba zai sāke koma kuma ba.’
6 Et tu fili hominis ingemisce in contritione lumborum, et in amaritudinibus ingemisce coram eis.
“Saboda ka yi nishi, ɗan mutum! Yi nishi a gabansu da ajiyar zuciya da ɓacin rai.
7 Cumque dixerint ad te: Quare tu gemis? dices: Pro auditu: quia venit, et tabescet omne cor, et dissolventur universae manus, et infirmabitur omnis spiritus, et per cuncta genua fluent aquae: ecce venit, et fiet, ait Dominus Deus.
Kuma sa’ad da suka tambaye ka, ‘Me ya sa kake nishi?’ Sai ka ce musu, ‘Domin labarun da suke fitowa. Kowace zuciya za tă narke kowane hannu kuma ya gurgunta; kowane ruhu zai sume kowane gwiwa kuma ta rasa ƙarfi kamar ruwa.’ Yana zuwa! Tabbatacce zai faru, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.”
8 Et factus est sermo Domini ad me, dicens:
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
9 Fili hominis propheta, et dices: Haec dicit Dominus Deus: Loquere: Gladius, gladius exacutus est, et limatus.
“Ɗan mutum, yi annabci ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji ya faɗa, “‘Takobi, takobi, wasasshe da kuma gogagge,
10 Ut caedat victimas, exacutus est: ut splendeat, limatus est: qui moves sceptrum filii mei, succidisti omne lignum.
wasasshe don kisa, gogagge har yana walwal kamar walƙiya! “‘Kada ku yi farin ciki, hukunci yana zuwa, domin kowa ya ƙi jin abin da na yi gargaɗi a kai.
11 Et dedi eum ad levigandum ut teneatur manu: iste exacutus est gladius, et iste limatus est ut sit in manu interficientis.
“‘An ba da wannan takobi don a goge, don a kama da hannu; an washe shi aka kuma goge, shiryayye don a yi kisa da shi.
12 Clama, et ulula fili hominis, quia hic factus est in populo meo, hic in cunctis ducibus Israel, qui fugerant: gladio traditi sunt cum populo meo, idcirco plaude super foemur,
Ka yi kuka ka yi makoki, ɗan mutum, gama yana gāba da dukan sarakunan Isra’ila. An jefa su ga takobi tare da jama’ata. Saboda haka ku buga ƙirjinku.
13 quia probatus est: et hoc, cum sceptrum subverterit, et non erit, dicit Dominus Deus.
“‘Gwaji tabbatacce zai zo. Kuma a ce sandan Yahuda, wanda takobi ya ƙi, ya ci gaba? In ji Ubangiji Mai Iko Duka.’
14 Tu ergo fili hominis propheta, et percute manu ad manum, et duplicetur gladius, ac triplicetur gladius interfectorum: hic est gladius occisionis magnae, qui obstupescere eos facit,
“Saboda haka fa, ɗan mutum ka yi annabci ka kuma tafa hannuwanka. Bari takobi ya yi sara sau biyu, har sau uku ma. Takobin kisa ne, takobi ne don kisa mai girma, zai kewaye su a kowane gefe.
15 et corde tabescere, et multiplicat ruinas. In omnibus portis eorum dedi conturbationem gladii acuti, et limati ad fulgendum, amicti ad caedem.
Domin zukata su narke da yawa kuma su fāɗi, na tsai da takobin kisa a dukan ƙofofinsu. Kash! A sa ya haska kamar walƙiya, ana riƙe da shi don kisa.
16 Exacuere, vade ad dexteram, sive ad sinistram, quocumque faciei tuae est appetitus.
Ya takobi, yi sara zuwa dama ka yi kuma zuwa hagu, duk inda aka juya ka.
17 Quin et ego plaudam manu ad manum, et implebo indignationem meam ego Dominus locutus sum.
Zan tafa hannuwana, fushina kuwa zai sauka. Ni Ubangiji na faɗa.”
18 Et factus est sermo Domini ad me, dicens:
Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
19 Et tu fili hominis pone tibi duas vias, ut veniat gladius regis Babylonis: de terra una egredientur ambae: et manu capiet coniecturam, in capite viae civitatis coniiciet.
“Ɗan mutum, ka nuna hanyoyi biyu inda takobin sarkin Babilon zai bi, duka biyun su fara daga ƙasa guda. Ka kafa shaida inda hanyar za tă rabu zuwa cikin birni.
20 Viam pones ut veniat gladius ad Rabbath filiorum Ammon, et ad Iudam in Ierusalem munitissimam.
Ka nuna hanya guda wadda takobi zai fāɗo wa Rabba ta Ammonawa ɗayan kuma da zai fāɗo a kan Yahuda da kuma Urushalima mai katanga.
21 Stetit enim rex Babylonis in bivio, in capite duarum viarum, divinationem quaerens, commiscens sagittas: interrogavit idola, exta consuluit.
Gama sarkin Babilon zai tsaya a mararrabar hanya, a inda hanyar ta rabu biyu, don yă yi duba. Zai jefa ƙuri’a da kibiyoyinsa, zai nemi shawarar gumakansa, zai bincike hanta.
22 Ad dexteram eius facta est divinatio super Ierusalem ut ponat arietes, ut aperiat os in caede, ut elevet vocem in ululatu, ut ponat arietes contra portas, ut comportet aggerem, ut aedificet munitiones.
A hannunsa na dama ƙuri’a don Urushalima za tă fito, inda zai kafa dundurusai, ya ba da umarni kisa, a yi kururuwar yaƙi, a kafa dundurusai a kan ƙofofi, a gina mahaurai a kuma yi ƙawanya.
23 Eritque quasi consulens frustra oraculum in oculis eorum, et sabbatorum otium imitans: ipse autem recordabitur iniquitatis ad capiendum.
Zai zama kamar duban ƙarya ne ga waɗanda suka yi rantsuwar yin masa biyayya, amma zai tunashe su game da laifinsu ya kuma kama su.
24 Idcirco haec dicit Dominus Deus: Pro eo quod recordati estis iniquitatis vestrae, et revelastis praevaricationes vestras, et apparuerunt peccata vestra in omnibus cogitationibus vestris: pro eo, inquam, quod recordati estis, manu capiemini.
“Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, ‘Domin ku mutanen nan kun tuna da laifinku ta wurin tawaye, kun kuma bayyana zunubanku cikin dukan abin da kuke yi, domin kun yi haka, za a kama ku.
25 Tu autem profane, impie dux Israel, cuius venit dies in tempore iniquitatis praefinita:
“‘Ya kai ƙazantaccen mugu, yerima Isra’ila, wanda kwanansa ta zo, wanda lokacin hukuncinsa ya cika fal,
26 Haec dicit Dominus Deus: Aufer cidarim, tolle coronam: nonne haec est, quae humilem sublevavit, et sublimem humiliavit?
ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ka kunce rawanin, ka ɗauke rawanin nan. Ba zai zama kamar yadda yake ba. Za a ɗaukaka ƙasƙantacce, amma a ƙasƙantar da mai girma.
27 Iniquitatem, iniquitatem, iniquitatem ponam eam: et hoc non factum est donec veniret cuius est iudicium, et tradam ei.
Hallaka! Hallaka! Zan hallaka shi! Ba za a maido da shi ba sai ya ga ainihin mai shi; gare shi zan bayar da shi.’
28 Et tu fili hominis propheta, et dic: Haec dicit Dominus Deus ad filios Ammon, et ad opprobrium eorum, et dices: Mucro, mucro evagina te ad occidendum, lima te ut interficias, et fulgeas,
“Kai kuma, ɗan mutum, ka yi annabci ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa game da Ammonawa da kuma zarginsu. “‘Takobi, takobi, an ja don kisa, an goge don cinyewa yana haske kamar walƙiya!
29 cum tibi viderentur vana, et divinarentur mendacia: ut dareris super colla vulneratorum impiorum, quorum venit dies in tempore iniquitatis praefinita.
Duk da wahayin ƙarya game da kai, duban ƙarya game da kai, za a sa shi a wuyan mugaye waɗanda za a kashe, waɗanda kwanansu ta zo, waɗanda lokacin hukuncinsu ya cika fal.
30 Revertere ad vaginam tuam in loco, in quo creatus es, in terra nativitatis tuae iudicabo te,
“‘Ka mai da takobi a kubensa. A inda aka halicce ka, a ƙasar kakanninka, zan hukunta ka.
31 et effundam super te indignationem meam: in igne furoris mei sufflabo in te, daboque te in manus hominum insipientium, et fabricantium interitum.
Zan zub da hasalata a kanka in hura maka wutar fushina; Zan ba da kai a hannun mugayen mutanen da suka gwanince a hallakarwa.
32 Igni eris cibus, sanguis tuus erit in medio terrae, oblivioni traderis: quia ego Dominus locutus sum.
Za ka zama itacen wuta, za a zub da jininka a ƙasarka, ba za a ƙara tuna da kai ba; gama Ni Ubangiji na faɗa.’”