< Esther 10 >
1 Rex vero Assuerus omnem terram, et cunctas maris insulas fecit tributarias:
Sarki Zerzes ya sa a biya haraji a ko’ina a cikin daular, har zuwa ƙasashe masu nesa na bakin teku.
2 cuius fortitudo et imperium, et dignitas atque sublimitas, qua exaltavit Mardochaeum, scripta sunt in libris Medorum, atque Persarum:
Dukan ayyukan Sarki Zerzes masu iko da masu girma tare da cikakken rahoton girmama Mordekai wanda sarki ya yi masa, ba a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Mediya da na Farisa ba?
3 et quomodo Mardochaeus Iudaici generis secundus a rege Assuero fuerit: et magnus apud Iudaeos et acceptabilis plebi fratrum suorum, quaerens bona populo suo, et loquens ea, quae ad pacem seminis sui pertinerent.
Mordekai mutumin Yahuda, shi ne na biyu a matsayi bayan Sarki Zerzes, mai farin ciki kuma a cikin Yahudawa, aka kuma ɗauke shi da martaba cikin’yan’uwansa Yahudawa. Gama ya yi aiki don kyautatawar mutanensa, ya kuma yi magana don a kyautata rayuwar dukan Yahudawa.